BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

 *_Yau litinin_* da tai dai-dai da saura kwanaki goma sha ɗaya biki. A yau ake saka ran saukar su Mamie Nigeria sai dai Anam bata san da hakan ba. Hasalima ta tashi ne da ɗan zazzaɓi. Wajen ƙarfe sha biyu Muzzaffar yay kiranta a waya. Yanda yaji muryartane ya sashi ruɗewa yace zai zo ya kaita asibiti. Amma sai taki acewarta tasha magani. yata lallaɓata amma taƙi yarda dole ya barta dan yasan mutuniyar tasa ƴar tutsu ce. Koda sukai sallama ma sai ta kashe wayar gaba ɗaya ta gyara kwanciya. Wani barcin ne ya sake awon gaba da ita saboda maganin da Aysha ta bata tasha. Bata farka ba sai kusan uku. Alhmdllhi zazzaɓin ya sauka dan hakata samu tai wanka ta ɗanci abinci. Bayan sallar la'asar tana waje zaune ita da Aysha sai ga kiran Muzzaffar, kai tsaye ya sanar mata gashi a ƙofar gida. Murmushi kawai tai ta yanke wayar, dan zuwa yanzu kam Muzzaffar ya samu wani gurbi na musamman a zuciyarta duk da sun jima nesa da juna dan baifi kwana uku da dawowa ƙasar ba. Yau ne ya fara zuwa gidan suyi hira, dan haka sai da Aysha ta fita tayo masa iso, anan inda suke zaune da Aysha saman kujerun roba ya zauna. Aysha ta shige ciki ta kawo musa ruwa ta koma domin basu dama...
   “Da alama zazzaɓin nan yaci amanar ango da yawa harfa kin rame dama gaki ba auki ba”.
Veil ɗinta taja ta ƙara rufe fuskarta tana murmushi. Shima ya murmusa cikin ƙara sanyaya murya yace, “ALLAH da gaske nake madam. Kodai aje asibiti?”.
“A'a ni naji sauƙi fa”.

“Kin tabbata?”.
Kanta ta jinjina masa. Murmushi ya sakeyi mai faɗi da shafa sajen fuskarsa. “Alhmdllhi ALLAH ya ƙara lafiya to”
“Amin ya rabbi.”
Shiru sukai na wani ɗan lokaci kafin ta saci kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta maida idanunta ƙasa ranta fal mamakinsa, dan babu rawar kan nan tasa, kuma bai kirata Beauty ba ko sau ɗaya. Murmushi yayi da gyara zamansa. “Madam nifa da magana nazo a bakina yau”.
Fuskarta ta ɗan buɗe sai dai bata kallesa ba. Ya cigaba da faɗin, “Juwairiyya gaskiya nima aure nake so”. A karan farko ta ɗago kai ta zuba masa dukan idanunta dake cikin gilashi. A hankali ya lumshe nasa ya sake buɗewa. “Wannan kallo ai sai kisa na gagara faɗar abinda ke raina”.
A yanda yay maganar ya sata sakin siririyar dariya. Hakan yayi dai-dai da buɗe gate da maigadi yayi motar Khaleel ta shigo. Su duka basu maida hankali ba, sai ma dariyar da yake tayata shima yana ɗan duban fuskarta da take kaudawa gefe, yanda yaketa ƙara ƙoƙarin son ganin fuskar tata sai yake ƙara bata dariya harta kasa dainawa….

     “Alhamdulillahi lallai yau jama'ar gidan nan zasusha surprise na ganinka Yaya fiye da yanda ƴan can gidan suka sha”. Khaleel ya faɗa yana kashe motar. Bai saurari amsaba ya buɗe gefensa ya fito, zagayawa yay ya buɗe masa fuskarsa ɗauke da murmushi.
  Badan glass dake rufe da idanunsa ba babu abinda zai hana aga tsantsar ɓacin ran dake cikinsu. Tuni sun kaɗa sunyi jajur, duk wani annurin dake saman fuskarsa na farin cikin dawowarsa cikin zuri'arsa ya ɓace ɓat. Cike da izzar da fushi ya haddasa ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito, hakan yayi dai-dai da juyowar Anam dake shirin ɗagama Khaleel hannu.. Hannun nata da numfashinta a tare suka maƙale, ƙirjinta yay wata irin bugawa da batasan dalili ba. A hankali laɓɓanta suka motsa ta ambaci sunansa...
  “Yaya Shareff”.

Duk da akan laɓɓa tai maganar hakan bai hana Muzzaffar gane sunan wa ta kira ba, juyawa yay shima a hankali. Cikin dariya Khaleel ya ɗago musu hannu da faɗin, “Surprise”.
Murmushin yaƙe ta saki, mamakinta na sake bayyana akan fuskarta, ta miƙe a hankali kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta nufesu, hakan yasa shina Muzzaffar miƙewa fuskarsa da murmushi yabi bayanta……….✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

27

……….A hankali ta ajiye wuƙar tana murmushi, ta miƙe cike da isa da izza tana magana da shan gaban Anam, “To ƴar wasa da biri, ya akai ke kika zama birin kuma a hannun ƴan wasa?”.
       Idanunta dake cikin gilashi ta ɗago tana kallonta, ta saki ɗan murmushi da kauda idanun kamar bazatace komai ba. Sai kuma ta hurar da numfashi da sake maida kallonta gareta. “Mi kikeci na baka na zuba Madam. Da Juwairiyya kike tare fa, Juwairiyya Anam Usman MD Shareff bana gaggawa akan al’amarina, sai dai ina bama maƙiyi damar da zai sharemin hanyar fagen isar da saƙona. Su kin faɗa musu ni na zubar miki da ciki right? Tom ki jira shi kuma mai cikin yazo ya ɗaura bincikensa akan yanda akai na zubar ɗin, daga haka game ɗin zai fara ok!”. Ta ƙare maganar da kashe ido ɗaya ta rabata ta wuce tana dariyar rainin hankankali.
      Wani irin bugawa ƙirjin Fadwa ya shigayi da sauri-sauri, tabita da kallo harta shige. Juyawa tai ta kalli mai aikinta, ganin aikinta take hankalinta baya kansu tai saurin barin wajen ta nufi bedroom ɗinta. Kai kawo ta shigayi cikin tashin hankali, dan da gaske kalaman Anam sun mugun dukanta, kanta ya kulle harma ta rasa kalar tunanin da zatayi. Tayi waya da Shareff a daren jiya amma bai nuna mata komai ba akan maganar rigimar zubda cikin balle tace ko Anam ɗin ta sanar masa ne. (To mi yariyarnan take nufi?) ta tambayi zuciyarta batare da tasan ta inda amsa zata fito ba. Ganin ta rasa ina zata kama ta yanke shawarar kiran Sima, dan tana da basira sosai, tasha warware mata ƙulluka da ita ta gaza kuncesu musamman da abokan hamayyarta irin su Anam ɗin……

       Sima tazo, sai dai Fadwa ta jata sun fita can garden ɗin gidan dake bayan sashen maigidan saboda kar a ƙara maimaita irin na ranar. Acan suka tattauna. Har Sima ta wuce Aysha da Anam basu ma san da zuwanta ba dan suna can suna kwasar barci. sai yamma sosai suka tashi saboda saurayin Aysha daya kira ta zai zo…..


          Tun daga waccan ranar Fadwa bata sake shiga sabgar Anam ba. Itama Anam ɗin bata shiga tata ba aikinta ma ya ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta. Babban burinta tayi ta kammala tabar Nigeria ta huta. Bata sake waya da Shareff ba tun waccan ranar shima. Sai dai taga sunayi da matarsa wadda in ta gama Aysha kawai take cewa Shareff ɗin na gaidawa. Takanyi murmushi a duk sanda hakan ta faru, duk da kuwa a ranta tanajin zafi da haushinsa. Sai dai takan ce inma baice yana gaida tan ba sai me.

      ★A ranar wata alhamis da tai dai-dai da zubewar cikin Fadwa Daddy yay kiran Aysha da Anam akan su samesa a gida. Daga wajen aiki Anam ta wuce, inda ta samu Aysha tuni tana can. Basu sami zama dasu Daddy ɗin ba sai bayan sallar isha'i. Cikin kulawa su Abban ke tambayar su babu wata matsala dai ko?. Murmushi Anam tayi, dan kai tsaye tambayar tafi ƙarfi a kanta ne. Tace, “Babu wani damuwa sai na zafi”. Dariya Daddy da Abbah sukai mata. 
     Bayan sun sarara Daddy ya dubesu a tsanake, “Yauwa kun san miyasa muka kiraku nan?”. A tare sukace a'a. Daddy ya jinjina kansa da cigaba da faɗin “Magana ce mai muhimmanci akan aure, yanzu dai kunga kun kammala karatunku, babu abinda ya kamaceku sai aure inba so kuke mu zuba muku ido ku tsufa a gabanmu ba, dan haka muna mai baku umarni ba shawara ba, kowaccenku ta bama wanda yake zuwa wajenta dama yazo mu gana da shi”.
    A ɗan tsorace Anam ta ɗago tana kallon daddy, ganin shima kallonta yake ya sata maida kanta ƙasa. Aysha kam murmushi ne ya suɓuce mata, dan kuwa dama Junaid nata damunta akan hakan, itace taƙi bashi dama saboda ganin yanxu ta Yaya Maheer akeyi ba suba.
   “Mamana yaya dai?”.

Abba ya katsema Anam dogon tunanin data tafi. Kanta ta girgiza idonta na cikowa da ƙwalla. “Abba babu komai, kawai dai….” sai kuma tai shiru.
“Kawai dai mi? Faɗi kanki tsaye kinji Mamana. Maganar aure ba maganace ta wasa ba, shiyyasa muka zaɓi baku damarku duk da hakkinmu ne zaɓa muku mazan aure matsayinku na ƴammata”.
“Tabbas babu wanda zuciyarta ta aminta zata iya tsaidawa, sai dai kuma bata iya jayayyaba, koda wasa bazata iya ƙin bin umarninsu ba dan batun yanzu ba Abie yasha sanar mata su ɗin kamar shi suke a gareta, idan har taja da su akan koma minene na rayuwa dabai zama saɓama UBANGIJI ba tamkar tayi jayayya da shine. Sannan wani ɓangaren ta sani babu abinda iyayenta ke buri a yanzu tamkar ganin tayi aure, kuma itama a karan kanta tana son taga wannan rana kamar kowace ɗiya mace duk da zatai matuƙar kewar iyayenta a kusa da ita. Abu na gaba kuma burin Abie ɗinta ta fidda miji a ƙasarsu ta haihuwa Nigeria, ta tabbata kuma hakan zaisa su dawo kusa da ita suma duk da can yafi musu kwanciya hankali fiye da nan… A hankali taja numfashi, batare data yarda ta kallesu ba ta gyaɗa kanta alamar amsa umarninsu. Daga Abba har Daddy sunji daɗin hakan, dan haka suka sallamesu akan suna jiransu.

     Gaba ɗaya Anam rasa sukuninta tayi a kwanakin da suka gabata, musamman akan wanda ya kamata ta tsayar matsayin miji a tsakanin samarin dake faman mata kaikawo su biyu. Wato Muzzaffar da Dr Jamal. Daga ƙarshe da ta fahimci zata saka kanta cikin wani hali sai kawai ta kira Mamie domin neman shawararta. Mamie uwace, sai dai ta raini tilon ƴarta da matsayi kala daban-daban bana uwa kawai ba. Shiyyasa Anam bata da wata ƙawa ko aminiya a duniya sama da Mamie, dan ko shawara zatai da Aysha ko Amrah sai ta gama da Mamie, koda abun mai nauyine a gareta tanajin kunya zata rubuta ta bama Mamien a rubuce. Yanzun ma hakan tayi, dan haka koda Mamie ta gama karantawa sai tai murmushi, Abie dake zaune a kusa da ita ta nunawa, shima dai murmushin yayi harda ƴar dariya. Ya amsa wayar yana faɗin, “Nine zan bata amsar daya dace da ita”. 
  Mamie tai dariya da fadin, “Uhhm nidai naga yanda zaku ƙare a wannan rana”. Dariya kawai Abie yayi, ya tafa saƙon ya turama Anam da dama zaman jira take. Shiru tai tana kallon saƙon, zuciyarta cike da wasiwasi. Sai dai kuma a ganinta tunda Mamie tace mata yayi to itama koda son sa bai kai mata har can cikin zuciya ba zata aminta da shi kuwa watarana zata so sa da izinin ALLAH. Sai dai kuma kamar yanda Mamie tace kartai masa magana da kanta bazatayi ba, tunda dama ya jima bai zo wajenta ba bai kuma kira wayarta ba sai lokaci-lokaci sukan ɗan gaisa a chart, shima kullum cikin cemata uzirine ya riƙesa yake.

   ★Kwana takwas dayin wannan magana abin al'ajabi ya sauka a MD Shareff family, ba komai bane kuwa sai baiko da saka ranar Anam da Muzzaffar, Aysha da saurayinta Junaid, za'a haɗe biki tare dana Maheer.
   Su Mommy kasa magana sukai dan mamaki, duk da wani sashe na zukatansu sunji tamkar an musu rahama ne, amma kuma sunajin ɗaci da zafin ganin Anam ɗin zata auri wanda shima ba baya ba, dan mahaifinsa akwai kuɗi, shima kuma Muzzaffar ɗin a karan kansa akwai kuɗin dan wani babban gwaska ne a kamfanib MTN. Duk yanda suka so kuma danne abin a rayukansu kuma kasawa sukai har saida suka haɗu suka tattauna, sai dai a ɓangaren Fadwa ranar har ruwa ta zuba ƙasa tasha. Jitai kaso talatin cikin ɗari na tsanar Anam ya sauka a zuciyarta harta kasa ɓoye hakan. Ita Anam ma data lura da ita sai abun yay matuƙar bata dariya........✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

30

……….Ganin tanata bubbuɗe abincin tana nuna masa ta kurma yay mata nuni da fruit salad kawai. Ta nuna masa abinci, yay mata alamar 1spoon kawai. Yanda ya buƙata haka tai masa, sai dai tasa masa haɗin salad a gefen shinkafar da ɗan yawa saboda tasan yafi buƙatar hakan. Da idanu yay mata alamar ‘thanks’ ta sakar masa murmushi.
         Sun fara cin abincin yay sallama da wanda suke wayar ya ajiye. Harya maida hankali ga abincinsa ya ɗago ya kalla Aysha. “Ina Anam?”. Ya faɗa a taƙaice. “Yaya tana ɗaki bata da lafiya, nayi-nayi ta taso taci abinci amma taƙi kuma ko magani bata sha ba”. Idanu kawai ya zubama Ayshar, sai abincin dake bakinsa da yake taunawa a hankali. Sai kuma ya janye kamar baiso yace, “Kiramin ita”. Mikewa Aysha tai da faɗin to.
      Da ƙyar ta taso Anam, amma da tace bazataje ba ita abarta. Sai da Ayshan tace, “Kin san dai zai iya zuwa har ɗakin nan ya ɓata miki rai ko”. Kamar bazata tashin ba sai kuma ta tashi tana ɓata fuska ga idanunta jazur. Ya ɗan juya musu baya, dan haka har suka ƙaraso wajen bai ɗago kansa ba. Sai da Fadwa tai magana idonta akan Anam datai gefe da fuska sannan ya ɗago. Kallonta yay da ƙyau ya janye idanunsa. Hakan yasa Fadwa sake yin magana cike da kissa. “Baki da lafiya kuma sai kije ki kwanta da ciwo a ɗaki Anam?”.
    “Uhhm”.
Kawai Anam ɗin tace a taƙaice, amma ko kallonsu taƙi yi daga ita har mijin nata. Murmushi Fadwa ta sake saki a zahiri, sai dai a ranta daɗin damar data samu takeyi, cikin sake sakin fuskarta tace, “Kije ɗakina saman mirror cikin First aid box akwai maganin zazzaɓi sai ki duba wanda zaki iya sha”.
        Yanzu kam sosai ta juyo ta zuba mata idanu, mamakin kissa da sabon salon Fadwan fes a kan fuskarta, sai dai kafin tace wani abu Shareff da yay kamar bayajinsu ya katseta. “Ki wuce ki ɗakko kizo kici abinci kisha”. Baki ta buɗe zatai magana sai kuma ta fasa, ta jefama Fadwa dake murmushi har yanzu wani kallon banza ta wuce zuwa bedroom ɗin nata da yau ne karon farko da zata shigesa. Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo tana taɓe baki sannan ta nufi mirror zuciyarta na ƙoƙarin danne abinda ke taso mata saboda kayansu data gani a watse a ƙasa da saman gado alamar ansha bidiri dai. Magunguna ta samu zube akan mirror ɗin wanda har ta ɗauke kanta ta kasa sai da ta sake kallonsu.
     Wani irin mummunar bugawa ƙirjinta yayi lokacin da idonta ya sauka akan sticker ɗin ɗaya daga cikin magungunan. Batama san sanda tai wurgi da maganinba ta fasa ƙara dayin tsalle gefe jikinta na maƙyarkyata. Aysha da Fadwa har rige-rigen isowa ɗakin suke. Yayinda uban gayyar ya shigo a ƙarshe fuskarsa a haɗe. Aysha dai dama kanta tayi, Fadwa kam dariya ta fara sai dai shigowarsa ya sata gimtsewa da sauri itama ta nufi Anam ɗin. Da robar maganin data cillar yaci karo, ya ɗauke kansa da maida dubansa gareta saboda abinda take faɗa tafukan hanunta rufe da fuskarta taƙi yarda Aysha ta buɗe.
      “ALLAH ya isa! ALLAH ya isa ƴar iska wayyo Mamie na ban yafe ba ban yafe ba…..”
    “Ikon ALLAH badai mu bane ƴan iskan ko Anam?!”. Fadwa ta faɗa cikin tafa hannaye da nuna damuwa na makirci saboda ganin ya shigo. Shi kuma ɗakin yabi da kallo har idonsa ya dawo kan robar data cillar ɗin, baima san sanda yakai hannu ya ɗauka ba yawun bakinsa na ƙoƙarin kamewa. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ya buɗe akan Fadwa ransa a ɓace. Sai da gabanta ya faɗi ganin yanda idonsa ya kaɗa yay jazur cikin lokaci ƙanƙani.
      “Kamata ku fita!”.
Ya faɗa cikin bada umarni ga Aysha. Hanun Anam daketa faman jera ALLAH ya isa har yanzu ta kama suka fice. Sai da suka fice ya tako ya zauna a bakin gadon ya dafe kansa bayan ya ajiye maganin gefensa. Ƙoƙarin danne tsoron dake faɗi a ranta tai ta nufesa, cike da kissa takai hannu kan kafaɗarsa. “Soulmate wlhy na man….”
      “You’re vary stupid da zaki faɗamin kin manta. Kinsan suna shigo miki ɗaki zaki ajiye waɗan nan abubuwan a inda idonsu zai gani. Koke da kika saka kanki ajiyewar dole ne sai kin bar stickers nasu a jikinsu saboda baki da hankali!!”.
         Yanda yake masifa ba ƙaramin bugu zuciyarta ke mata ba. Ta shiga girgiza masa kai dan yana yine kamar zai mareta. Ta matso da nufin rungumesa ta basa haƙuri ya tureta ya fice. A falo ya sami su Anam har yanzu tana faman kwarara ALLAH ya isa, Aysha na tambayarta wai miya faru ta kasa bata amsa.
     “Shut up!! stupid!”.
Ya faɗa a tsawacen daya tilasta Anam gimtse bakinta da janye hanunta dake akan fuskarta har yanzun. Da sauri ta sake maidawa ta rufe ganinsa tsaye a gabansu. “Idan kika ƙara wani magana anan saina mareki, dalla kuwuce kuci abinci”. Kusan a tare duk suka miƙe zuwa dining ɗin, yabi bayansu yana jan tsaki mai ƙarfi. Aysha ta zuba mata abincin, jin yanda yaketa faman jan tsaki a jajjere ya sata cin abincin badan taso hakan ba. Laumarta baifi uku ba tai yunƙurin mikewa ya watsa mata harara. Da sauri ta koma ta zauna kamar zatai kuka.
        A daidai nan Fadwa ta fito jiki a saɓule, sai dai daka kalleta zaka san tayi kuka. paracetamol ta ajiye gaban Anam tana satar kallonsa, fruit ɗinsa yake sha sai dai fuskar tamkar zatai aman wuta. Kujera taja ta zauna. shiru wajen ya ɗauka babu mai ko tari sai ƙarar cokula. Anam ce ta fara turo nata dan da gaske zazzaɓin nata neman dawowa sabo yake. Aysha ta ɓalla mata magani ta bata. Amsa tai tasha babu musu, tana kammalawa tabar wajen da ɗan gudu-gudu dan karma yace zai dakatar da ita. Itama Aysha sauri-sauri tai ta gama ta gudu ta barsu a wajen……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button