BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin ƙanƙanin lokaci rashin lafiyar Shareff ɗin ta shiga kunnen kowa. Waɗan da basu riga sun wuce wajen kamu ba sai suka zarto asibitin dubasa. Babu wanda aka bari ya shiga wajensa dan ba’ason masa hayaniya. Sai Mommy data matsa ita da Gwaggo suka leƙasa. Har dare anata shigowa asibitin duba san, dan wandama sukaje gidan kamu daga can nan suka dinga zartowa. Hakan sai ya tabbatarma da jama’a mara lafiyan ɗan dangi ne. Har sha biyu bai farka ba, anata ma ƙara masa ruwa har lokacin, dole kowa ya tattara ya tafi aka bar Khaleel da Maheer a wajensa duk da Fadwa harda kukanta itace zata zauna da shi. A can gida ma Anam tana kwance rijif da zazzaɓi duk da doctor yazo ya dubata bayan na ido. Haka dai aka kwana zukatan mutane da yawa babu daɗi.
Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure duk da rashin daɗin da ake ciki akan ciwon Shareff dan na Anam ba kowa ya sani ba. Da sassafe Fadwa ta wuce asibiti ita da Mommy data zillema mutane da ƙyar. Sun samu ya farka har Maheer ya taimaka masa zuwa bayi yayo alwala. Yana cikin yin sallar daya makara ne suka shigo. Sun ɗanji sanyi a ransu. Suna zaune harya idar, suka shiga jera masa sannu yana amsa musu da kai dan sam baya son yin magana. A dai-dai lokacin suma su Abba suka shigo harda Daddy, kamashi su Khaleel sukai ya koma saman gado, cikin magana ƙasa-ƙasa da bata fita da ƙyau ya gaida su. Cikin kulawa duk suke amsa masa da tambayar ƙarfin jikinsa. Ya amsa musu “Da sauƙi” akan laɓɓansa. Abba ya fara masa faɗa akan ya akai ya zauna da ciwo haka babu wanda ya sani? Sai kace wanda baida kowa?.
Ɗan murmushin ƙarfin hali yayi na yaƙe, murya ƙasa-ƙasa yace, “Abba zazzaɓine kawai shiyyasa. Kuma naji sauƙi Alhamdulillahi”.
Abie ya girgiza kansa yana mai dubansa da tausayawa. “Wannan yafi ƙarfin zazzaɓi kawai my son. Kaga kuwa yanda ka rame? Sannan a kwanakin nan gaba ɗaya babu mai ganinka, mu duk mun zata aikine ya maka yawa shiyyasa”.
Ɗan murmushin yake ya kumayi sai dai baice komaiba anan ma. Idanunsa da sukai wani irin kaɗawa jazur ya lumshe da jingina a jikin filon da Khaleel ya saka masa. Ya buɗesu a hankali ya saci kallon Mommy da Fadwa dake zaune kowa ya zuba tagumi. A hankali ya furta “Mommy inajin yunwa”.
Kai Mommy ta jinjina masa, tare da taɓa Fadwa datai zurfi a duniyar tunani. Numfashi ta kawo mai haɗe da ajiyar zuciya ta kalli Mommyn. “Kira su Bintu muji wai ba’a kammala abincin bane gashi yace yunwa yake ji”. Da to ta amsa. Tana shirin kiran waya sai ga sallamar Mom da Mamie. Su Abba ne kawai suka amsa da Khaleel. Suka shigo Maheer biye da su ɗauke da basket, sai Mubarak da carton na ruwa. Daga Mom har Mamie fuskokinsu sun kasa ɓoye damuwarsu akan yanayin Shareff ɗin, suka shiga masa sannu da jera masa addu’a su Daddy na amsawa da amin. Mommy da Fadwa dai sunyi kamarma basu san da zuwansu ba. Abba ne ya bada umarnin Maheer ya zuba masa abincin dasu Mom ɗin suka kawo tunda yace yunwa yakeji daman…
Shigowar Doctor ta sakasu duk suka fito, Daddy ya dubi agogo, ganin lokaci yaja gashi yau juma’a ga ɗaurin aure yace su ai gara su wuce gida ma Khaleel da Fadwa sai su zauna a waje sa, dan dama acan gida sune suka hana kowa zuwa har Gwaggo. Cema mutane akai kawai an ma sallamesa dan haka kowa ya dakata da yunƙurin zuwa aka maida hankali ga shagalin biki. Fadwa da Khaleel aka bar masa, su kuma gaba ɗayansu suka wuce gida, sai dai Maheer bai so hakaba, soyay shima a barsa anan basai yaje ɗaurin auren ba. Amma babu yanda zaiyi su Abba suka korashi, ga Mommy sai zabga masa harara takeyi…..
★★
Gidajen biyu duk sun gama cika da jama’a, bakajin komai sai hayaniya da al’ada irin ta biki. Maza duk sun wuce massallaci domin halartar sallar juma’a da ɗaurin aure. Yayinda amarya Anam ke ƙudundune har yanzu taci kuka harta godema ALLAH, zazzaɓi ne mai tsananin zafi tattare da ita. Haushin kowa takeji a gidan, har shi Muzzaffar ɗin da rabonta da shi a zahiri tun randa Shareff ya dawo, saita waya jefi-jefi yake kiranta daga gaisuwa kuma sai yace mata yana da uzuri. badan bata son sa ba take jin haushinsa, kauce-kaucen da yake mata ne yafi komai mata zafi, musamman a kwanakin matsowar bikin. Su Abie sun isa da itane shiyyasa take danne komai saboda farin cikinsu, ko sai bayan sun ɗaura mata aure suka gaya mata bazata taɓa jayayya da su ba saboda matuƙar girma da darajar da suke da shi a gareta. Amma shi mizaisa ya dinga mata kauce-kauce kamar dole akai masa ya aureta bashi yazo yace yana sonta ba?, ya kuma ɗauke ƙafa da zuwa inda take ma sai kace zasuyi auren ƙiyayya?. Hawaye ne suka cigaba da silalo mata a hankali dan bata da ƙarfin yin kuka, a wannan yanayin barci ya saceta saboda allurar barci da doctor ya mata.
★Tun bayan barin su Daddy asibitin yaƙi ya sake magana da kowa, Fadwa da Khaleel ma cayay su bashi waje yana buƙatar kaɗaici. Ran Fadwa ya ɓaci sosai har ta kasa shanyewa ta dubesa zatai magana Dr Jamal ya ɗan girgiza mata kai da mata alamar roƙo kar tace komai. Harara ta watsama Shareff tai fitowarta. Shiko Khaleel biyota yay fuskarsa ɗauke da murmushi, yayi tunanin ma asibitin zata bari gaba ɗaya, amma sai ya sameta a waje zaune tana danna waya alamar kira take ƙoƙarin yi. Baice mata komai ba ya kai zaune a kujerar dake kallonta, waya ya ɗauka shima, yana jinta tana faman jan tsaki da alama wanda take kiran bai ɗauka ba. Suna a wajen zaune Dr Jamal ya fito, Fadwa ya kalla dake cika tana batsewa. Yay murmushi da girgiza kansa. “Madam kiyi haƙuri kar kiji zafinsa da yawa, shi mai ciwo haƙuri ake da shi dan bakomai ake masa yaga an masa daidai ba. Zaki iya komaa yanzun ya samu barci, amma ba’a buƙatar motsi mai ƙarfi dan barcin nasa bazaiyi nauyi sosai ba”.
“Amma Doctor dan mutum na ciwo sai ya dinga dizga mutane kuma. Shi baya ganin ƙoƙarin mu ne?”. “Bawai baya gani bane, yanayin da yake ciki ɗinne sai anyi haƙuri da shi Please. Ki ƙara haƙuri ki koma ciki mu zamuje massallaci ne”. Bata sake cewa komai ba ta tashi ta shiga, su kuma suka fice shi da Khaleel da yaƙi saka baki a maganar tasu dan ƴan miskilancin na kusa……….✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
BABU SO????????AREWABOOKS
36
………Burin Mommy kawai ya kalleta amma yaƙiyin hakan. Tsahon minti guda baice komai ba yana satar kallon fuskokinsu ta gefen idanu. Tabbas ya hango tashin hankali kala-kala musamman a fuskar Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima da Fadwa, ya haɗiye busashen yawu da ƙyar tare da tattaro dukan ƙwarin gwiwarsa da jarumtarsa. Cikin dakewa ya ce, “Baba bani da ja akan hukuncinku”.
“Kan ubanka Al-Mustapha!!”.
Mommy ta faɗa cikin suɓutar baki, Murmushi Abba da Abie suka saki kusan a tare, hakama aunty Mimi da Mom da aunty Amarya sai da sukai kananun murmushi. Ɗayan yayanta da suke cema Yaya Kamil ya harareta, a kausashe yace, “Nafisa! Dama kina buƙatar ya bijirema iyayensa ne? A matsayinsu na mahaifa a garesa su zartar da hukunci ki nunama duniya k baki bama ɗanki tarbiyya ba saboda wani banzan tunaninki da hujjojinki? Karna sake jin bakinki a wajen nan, in ba hakaba ranki zaifi haka ɓaci billahillazi!!”.
Dole tai shiru saboda a maganar Yaya Kamil ɗin babu wasa sam. Baba Ibrahim ya sake maida hankalinsa ga Shareff. “Ka bamu amsa ne a dunƙule Shareff, kana nufin ka amsa auren kenan?”.
Sai da ya ɗan saci kallon Mommy ta gefen ido, tako zuba masa ido cikin matsanancin ɓacin rai, janye idanunsa yayi ya maida kan Daddy shima ya tsume kamar fuskar tasa zatai aman wuta.
“Shareff kai muke saurare, in har a ranka kanajin auren nan cutuwane a gareku ka saki yarinyar nan tun yanzu anan karka saka ku a wani halin da zai wargaza zuminci”.
A hankali ya girgiza kansa dake rissine a ƙasa. “Baba ku gafarceni bazan iya sakinta ba tunda an ɗaura….”
Kukan da Anaam ta fashe da shi ya hana Gwaggo data ɗauki sallami tana tafa hannaye ƙarasawa, hakama Mommy da Gwaggo Halima da suka zaburo. Fadwa ma kuka ta saki mai ƙarfi yayin da Aunty Mimi da Mom da Abba suka saki wata nannauyar ajiyar zuciya, Abie ko murmushi ya saki, shi ko Daddy ya ɗan lumshe idanu. Mamie dai kanta a ƙasa yake babu mai iya gane yanayinta. Albarka su Baba Ibrahim suka shiga sanya masa da suma murmushin ya ziyarci fuskokin su, hakan ya ƙara tunzura kukan Anam da Fadwa….
“Nidai bana Son sa baba, akwai wanda naima alƙawari zan aura nima, kuma shi nake so!!”. Furucin Anam cikin matsanancin kuka ya daki kunnuwan kowa dake a falon. Cikin sauri da zaburowa Mommy tace, “Shima ai ba son naki yake ba, shegiyar yarinya mai kama da ifiratan aljanu. Yaya ai kaga abinda nake gudun masa tun farko, mizaiyi da wannan mara tarbiyyar yarinyar har tana wani iƙirarin ba son sa take ba fitsararriya…..”
Hayaniyace ta nema sake kaurewa a falon, yayinda Anam ke rusa uban kuka ita akwai wanda take so. Tsawar da Abie ya daka mata ce ta saka gaba ɗaya hayaniyar kukan Fadwa da Hargowar Mommy data Gwaggo yin tsitt. Anam ta maƙure jikin Aunty Mimi tana sake fashewa da kuka. Baba Ibrahim ne ya kalla Abie cikin murmushi, kansa ya girgiza masa cikin dattako. “Ayi haƙuri Usmanu abita a hankali sai a samu masalaha sahihiya. Tsanani baya kai kowa ga hanyar nasara. Juwairiyya zonan kinji”.
Da taimakon aunty Mimi ta mike taje gabansa, kusa da ƙafafunsa ya nuna mata, ta zauna tana shashshekar kuka da sharɓar hawaye da gyalen data rufe har fuskarta. Cikin lallashi yace, “Kukan ya isa haka to, maza share hawayrnki”. Da ƙyar ta iya danne kukan, sai dai hawayen basu bar zirara ba.
Cikin lallashi yace, “Faɗa min wa kike so?”.
Kai tsaye tace, “Muzaffar!”.
“Miyasa shi Shareffuddeen baƙya son shi?”.
Shiru tai ta kasa magana, ya ƙara maimaita mata tambayar.
“Kawai Baba”.
“Ai shi mutum ba’a ƙinsa kawai Juwairiyya. Amma zan baki wata dama da kuma alfarma kin yarda?”.
Cikin share hawaye ta jinjina masa kanta. Yay murmushi irin nasu na manya masu basira.
“Ina so kimin alfarmar yarda a kaiki gidan Shareffuddeen. Daga nan zuwa wata uku in har baki samu wani farin cikin zama da shi ba, kizo ki sanar min, ni kuma na miki alƙawarin da kaina zan saka shi ya sallama miki”.
Karon farko ta ɗago ta kallesa. Cike da tabbatarwa ya jinjina mata kansa yana murmushi. Ta kai dubanta ga Shareff, cikin sa’a kuwa suka haɗa ido. Wani shegen kallo da taima fassara dana tsana ta hango cikin idanun nasa, sai taji ƙwarin gwiwar cin nasarar shawarar baba ibrahim, dan kuwa ta tabbatar babu wani farin ciki da zata samu daga Shareff ɗin musamman idan ta auna irin tsanar da yay mata a rayuwa. Idan haka ne gara ta amince kodan goge laifinta da su Abie zasu iya gani, cikar wata uku kuma dai-dai da kammala Serves ɗinta kenan……
“Baki ce komai ba”.
Baba ibrahim ya katse mata tunani.
“Baba na amince”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa, hakama abie da Abbah da Daddy duk sai da suka saki ajiyar zuciya. Yayinda Mommy tai ƙwafa sai dai babu damar cewa wani abu.. Baba Ibrahim ya sake ƙara musu nasiha baki ɗaya musamman Gwaggo dake a matsayin uwa garesu su duka a wajen. Hakama Mommy data hau dokin zuciya da yasan bazata taɓa tanƙwasuwa ta sauƙi ba. Itama dai Fadwa da Gwaggo Halima sun sami nasu rabon musamman ma Fadwa da yaketa lallashi dan yasan an mata laifi. Suma dai su Daddyn ya musu nasihar ya kuma ƙara bama kowa haƙuri da fatan komai ya wuce sannan yay addu’a taron ya tashi dan dare ya farayi…..