BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

★★Washe gari an tashi ne mafi yawan rayuwuka a ɓace, ga amaryar Maheer ta iso tun daren jiya, tana a sashen Mom kamar yanda Daddy ya sharɗanta. Aunty Halima dai tun daren jiya tabar gidan tare da Fadwa, acewarta dai su Daddy basa ƙaunarta babu ita babu su, Fadwa ma tabar gidan Shareff kenan sai dai ya biyota da takardarta. Komai babu wanda yace mata a cikinsu, sai Gwaggo dake faman matsar ƙwalla tana faɗar maganganu. A haka dai babu daɗin rai akai walima washe gari dan dama ango Maheer shi bai yarda da wani event ko ɗaya ba, butsutsunsa yasa Mommy haƙura duk da taso a sha shagali tamkar bikin Shareff da Fadwa.
Shareff ma dai tun a daren ya koma can gidansa tare da Khaleel da Maheer ɗin da suka kwana da shi a can saboda yanayin jikinsa daba gama daidaita yay ba. Itama dai Anam bata kwana da lafiya ba dan tunda sassafe ma sai da Abie ya kaita asibiti da kansa aka bata gado. Dan haka har yamma tana can tare da Aunty Mimi da Abie ɗin, sai su Mom da su Daddy da sukaje daga baya dubata. Wannan ya kawo ƙaracin armashin buɗar kai da akai na amaryar Maheer, bayan sallar la’asar danginta da wasu a dangin Mom sukai mata rakkiya gidan mijinta. Gida yayi ƙyau dan Maheer ma yayi ƙoƙari sai sambarka. Sannan iyayen amarya ma sunyi nasu ƙoƙarin dan kun san dai Mom dama duk inda take na masu manda ne. (Tana bala’in son huɗɗa da masu kuɗi a gidan sanyi????).
Tun a ranar mafi yawan baƙi suka kauce dan uwar bikin a birkice take. Tako’ina Mommy ɗin ta birkicema kowa. Gida yayi lafiya, baƙin da suka rage kalilanne, Hakan yasa koda aka sallamo su Anam daga asibiti sanda suka shigo gidan tsitt yake.
Washe garin data kasance lahadi sai ga mahaifin Fadwa har gida ya maido Fadwa, babu ragi yay mata tatas a gaban su Daddy ita da Mommy. Fafir kuma yaƙi sauraren zantukan Gwaggo duk da uwa take a garesa. Wannan dattako daya nuna ya matuƙar faranta ran kowa a gidan ciki harda Shareff da aka sashi zuwa gidan. Daga ƙarshe kuma ya bisu da nasihar zaman haƙuri dana riƙe junansu domin samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Bayan wucewarsa su Daddy suka sake zama da Shareff, sun basa umarnin ƙarasa abinda ya rage masa dan nan da sati ɗaya amarya zata tare ɗakinta. Yaso yace suɗan ƙara masa amma baiga wannan damar a fuskokinsu ba dan umarni suka bashi ba shawara ba. Daddy kuma ya turkesa a wajen yace ya biyasa kuɗin sadaki dan shine ya ranta aka biya a waccan ranar. Dole yayma Daddy transfer ɗin kuɗinsa take a wajen sannan ya barsa ya tafi.
Ƙin shiga wajen Mommy yayi dan wasan ɓuya yake da ita tun ranar, ya aika Aysha ta kira masa Fadwa tazo su wuce. Amma sai Mommy tace a faɗa masa Fadwan ta ƙarfi ce idan yanada ƙarfin yazo ya ƙwata. Murmushi kawai yayi sanda Aysha ta zo masa da amsa, batare da yace komaiba ya shiga motarsa ya fice a gidan dan gwara wannan wasan ɓera da magen da yake da Mommy ɗin akan tunkararta face to face a yanzun.
★ Kamar wasa ciwo ya kwantar da Anam sai da aka kwasheta aka koma da ita asibiti a daren yau. Dawowar su Amrah cikin gida yasa su Mom suka sani, dan daga Mamie har Abie da Aunty Mimi duk suna acan asibitin. Duk da dare ya farayi haka Abbah da Daddy suka fita, Khaleel ne ya jasu a motar bayan sun kira Abie sunji asibitin da suke.
Lokacin da suka iso har an bama Anam ɗin gado amma saka mata ruwa barci ya ɗauketa. Ta rame sosai dayin wani irin fayau da ita, suna cikin jajantama juna Shareff ya shigo, Khaleel ne ya tura masa sms ya sanar masa sanda zasu taho, dan haka ganin nasa ya bama kowa mamaki har Abie ya kasa haƙuri yay magana.
“Babana waya saka fitowa a wannan daren haka? Ga anguwarku da nisa?”.
Ƙaramin Murmushi yay idonsa na satar kalllo Anaam dake barci duk ta koɗe tayi fayau da ita abin tausayi……….✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
BABU SO????????AREWABOOKS
37
………Kiran sallar farko ya farka, dama ba wani barcin kirki yayi ba, dan bai baro asibiti ba a daren jiya sai kusan ƙarfe ɗaya, shima sai da Abie ya korashi dan suma duk lokacin suka wuce aka bar aunty Mimi kawai da Anam dake barci. Sai da ya watsa ruwa kozai samu ƙarfi sannan yay alwala ya fita massallaci, gari ya ɗanyi shaa ya shigo gidan, ya ɗan ja tsaki dan gaba ɗaya gidan yay masa wani irin girma, yayi niyyar sakama Fadwa ido yaga iya gudun ruwanta amma a yau yaji bazai iya hakan ba, dan ya kula sai ya fito mata ta inda bata zato sannan zasu samu dai-daito. Wayarsa ya ɗauka yana zama bakin gado dayin ƙaramar ƙwafa, aunty Mimi ya kira, bugu biyu kuwa ta ɗauka suka gaisa, ya tambayi yamai jiki tace da sauƙi amma bata tashiba har yanzun dai.
“Masha ALLAH, nima zan shirya yanzu zan shigo, ko kuna buƙatar wani abu ne shiyyasa na kira?”.
Aunty Mimi ta amsa da “To ALLAH ya kawoka lafiya. Bama buƙatar komai tunda bata tashiba balle aji ko ita tana son wani abu ɗin”.
“Okay to sai nazo”.
Ya faɗa yana yanke wayar. Bai wani jima ba ya kammala shiryawa ya fice, sai da ya shiga mota ya fara kiran number Fadwa, harta tsinke ba’a ɗagaba, ya sake tsuke fuska ransa na ƙara ƙuna dan ya tsani raini a rayuwarsa. Wayar ya jefa kujerar gefansa yay ma motar key ya fice.
Gama wayar aunty Mimi babu jimawa ta farka, da taimakonta taje toilet dake a cikin ɗakin, jikinta sam babu ƙarfi, hakan yasa Aunty Mimi taimaka mata ta ɗan watsa ruwa mai ɗumi sosai sannan tai alwala suka fito. Murya a karye irin ta mara lafiya tace, “Ummie bazan iya salla a tsaye ba ina ganin jiri”. Taimaka mata aunty Mimi tai ta zauna kan sallaya, dai-dai nan masu gyara ɗakin suka shigo tare da wata nurse. Su dukansu suka gaida Aunty Mimi da tambayar mai jiki, ta amsa musu da fara’a.
Gyaran gado mai sharar ta fara, yayinda Nurse ɗin ke tsaye tana jiran Anam ta idar. Sai da tai addu’a Nurse ɗin ta taimaka mata ta koma saman gado, kwancia ta ƙarayi dan gaba ɗaya batajin ƙarfin jikinta. Harta lumshe ido sallamarsa ta sakata buɗewa, kallo ɗaya tai masa ta maida ta rufe abunta fuskarta na sake tsukewa. Gaisheshi Nurse ɗin tai hakama mai sharar, ya amsa sama-sama yana ƙarasawa gaban aunty Mimi ya ajiye ledojin hanunsa. Aunty Mimi dake dubansa da murmushi tace, “Babana mun hanaka barci ko?”.
Murmushi ya ɗanyi da kaiwa zaune a ɗayan gadon dake ɗakin, ya rissina yana gaisheta kafin ya bata amsa da “Ko badan kuba dole na fito ai yau akwai office”.
“Tofa ango guda da zuwa office”.
Idanunsa ya sauke akan Anaam batare daya ce komai ba, cikin son basar da zancen yace, “Har yanzu bata tashi ba?”. Kallon Anaam aunty Mimi tayi, ganin tayi luff kamar bata jinsu tai ƴar dariya. “Yanzun nan tai salla ma, tana komawa saman gadon kana shigowa. Sallamar Doctor ta hanashi cewa komai, tare yake da nurse ɗin ɗazun, ya miƙa masa hannu suka gaisa yana tambayar yamai jiki. Da aunty Mimi ma suka gaisa sannan ya ƙarasa gaban gadon.
Cikin tsokana yace, “My patient barcine ko likimo?”. Duk da ta jisa bata motsa ba, sai dai taɗan buɗe idonta ta kallesa ta maida ta rufe. Murmushi yayi da sake faɗin, “Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya. Sister Rabi taimaka mata ta tashi”.
Da taimakon Nurse daya kira sister Rabi ta tashi, sai langaɓewa take kamar zata saki kuka, cikin lallashi doctor yake mata ƴan tambayoyi akan yanayin jikinta tana bashi amsa, ko sau ɗaya taƙi yarda ta kalli sashen da Shareff yake. Bayan doctor ya kammala ya bada umarnin a bata abinci ko kaɗan taci zai aiko a sake saka mata ruwa da allurai uku, dan suna buƙatar ta samu barci sosai da alamu suka nuna kwana biyu bata samu. Koda ya fice shi da Nurse ɗin bata yarda ta kalli inda yaken ba, saima ƙoƙarin kwanciya da taso yi aunty Mimi ta dakatar da ita. Idanunta ta ɗago cikin marairaicewa ta kalli aunty Mimi, har ƙwalla sun taru dan ma gilashin idonta ya ɗan ɓoyesu duk da fari ne tas, karaf suka haɗa ido, ta sake yin kicin-kicin da ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. Shiko ya kafeta da nasa idanun sai dai shima tashi fuskar tsamm take babu wasa.
“Ummie jiri”.
Ta faɗa a hankali.
“Na sani mamana ki daure kici abinci kamar yanda doctor yace sai ki kwanta ɗin. Bata iya musu ba, dan haka tai shiru. Aunty Mimi ta bubbuɗe ledojin da Shareff ya shigo dasu, kayan tea ne a leda ɗaya, ɗayar kuma abincine dai-dai cin mara lafiya kuma abinda Anam ɗin take matuƙar so. Amma da yake daru takeji sai tace ita bata son shi, aunty Mimi sai lallashinta take amma ta kafe ita bata sonsa a kira Mamie ta kawo mata wani.
Sarai yana jinsu amma bai tanka ba, sai danna wayarsa yake kai kace hankalinsa baya kansu sam. Ana cikin badaƙalar Khaleel ya iso. Cikin shirin office yake, ya gaida aunty Mimi da Shareff ɗin yana ajiye basket na abinci da Mom ta aikosa ya kawo. Kafin ya karasa gaban gadon yana kallon Anaam da ƴar sakin fuska dan shi murmushi ma kakan daɗe baka gani ba tare da shi. “A jiki yayi sauƙi granny tunda gaki zaune, jiya har mun fara ƴar ƙwalla da murnar cin gummba”.
Murmushi ta saki tana kallon Khaleel ɗin kamar ba ita ke bori ba. “Kai Yaya Khaleel, kai ashe soma kake na mutu?”.
Murmushi yayi shima a karon farko, “To Granny na sani ko lokaci yayi jikin tsufa”.
Ta ɗan hararesa tana ɗauke kanta, dariya yayi nan ma. A ɗan shagwaɓe tace, “Yaya mika kawo min?”.
“Breakfast ne Mom tace a kawo miki kafin su ƙaraso”.
“Na gode”.
Ta faɗa tana maida dubanta ga Aunty Mimi da ke kallon Shareff daya miƙe fuskarsa kicin-kicin kamar zaiyi aman wuta. “Ummie zanci”. Da ga shi har Aunty mimi kallonta sukai, yay mata wani mugun kallo ya ɗauke kansa. Itama harara ta balla masa ta ɗauke nata idon. Sarai yaga harar dan haka ransa ya ƙara ɓaci, batare da yayima kowa sallama ba ya fice abinsa.
Daga aunty Mimi har Khaleel da kallo suka bisa…..