BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

★★★
Kamar su, itama dai makarar tata bai hanata tashi yin salla akan lokaci ba, koda ta idar kuma kasa komawa tai ta kwanta kamar yanda tai niyyar yi, sai ta ɓige da kiran wayar aunty Malika dan a yanzu sune ke bata dukkan ƙwarin gwiwar da bata samunta a gun kowa hatta mahaifiyarta data san suma suna a cikin tasu damuwarne game da wannan auren ƙaddara ko biyayyar daya sami mijinta da rana tsaka. Cikin muryar barci suka gaisa da aunty Malika…
“Fadwa badai kin saka shashanci a zuciyarki kin gagara barci ba? Yanzu saboda abunda baida amfani kika zaɓi hana idanunki barci bayan mun gama miki da matsalar?”.
“Aunty naso mantawa da komai tamkar yanda kuka faɗa sai dai na kasa. Wlhy na tsaneta shima a yau naji na tsanesa. Tare fa suka kwana a sashensa da ita”. Ta ƙare maganar da rushewa da kuka. Aunty Malika taja tsaki tana tashi zaune. “Lallai Fadwa ke shashasha ce gaskiya, yo duk da nasan cewar baki girmi yarinyar nan ba sai dai kuyi sa’anni kuma ita ɗin girman turaice ai banyi tunanin samunki haka muguwar lusara ba. Har mi akai wai akai wannan tsefatar yarinyar da kaɗan tafi wada tsaho. Fadwa kefa girman Nigeria ce, Nigeria ɗin ma Arewa, arewar ma kano kuma matsayin ƙabilar hausawa. Tunda kika taso a gidanku bayan mahaifiyarki kin sameta tare da wata matarne kafin ta fita tabar gidan, kinga kenan kinsan minene kishiya, kin san ilimin zama da ita tunkan ki buɗe ido kiga wata da sunan kishiyarki. Idan har kika cigaba da zubar da mutuncinki wajen zaman yin kuka ko bari Mijinki yaga lagonki to lallai k baki cika jinin zuri’armu ba…..”
Cikin tarar numfashin aunty Malikan tace, “Aunty wlhy nayi dukkanin ƙoƙarina, ban aikata wani abu saɓanin wanda kukace nayi ba”.
Ajiyar zuciya aunty Malika ta sauke. “Haka nake sonki ƴa tagari, ki zama jaruma kuma jajirtacciya a gidanta bawai lusara ba. Kamar yanda na faɗa miki yanzu ba’a bin boka ba’a bin malam akan kishi, kissa da kisisina da magungunan mata sune takubban ƴaƙar kishiya musamman irin taki da babu abinda ta sani sai kauɗi da buɗewar ido a cikin masu jajayen kunne. Kafin duniya ta goge mata idanu ta hango abinda kikema sakaci ki jajirce ki ƙwaci mijinki da wannan damar inba hakaba dare zaiyi miki, dare mai duhun tsiya da tafin hanunki ma sai kin gagara gani balle hanyar ceton ranki. Dan haka yanzu ki tashi ki haɗa breakfast mai rai da lafiya irin wanda baki taɓa masaba, kije ki shirya musu a sashen nasa kamar yanda ya buƙata”.
Hawayenta ta share, duk da sam wannan shawarar batai mata daɗi ba amma zata jure, dan ita shaidace taga alfanun danne zuciya a jiya, badan ta shanye komai ta maidashi ba komai ba Shareff bazai ko dubeta ba akan abunda ta dinga masa tun daga fara rikicin auren nan. Amma gaskiyar su aunty Malika namiji tamkar yaro yake, duk kunnasan da kai da zarar ka lulluɓesa da kwalba sai kaifinsa ya zama mara tasiri ya koma haska maka zuciya da hasken wutar daka kunna masan. Da layin barci da dauriya ta shirya breakfast mai sauƙi kuma mai daɗi tamkar ba Fadwa mai babbake abinciba. Maimakon ɗauka takai sai ta fara shiga wanka, tsaf ta shirya cikin doguwar rigar lass ta caɓa ado tamkar ita ɗince amaryar, ta baje jikinta da kalolin turarren da tasan yafi so da ƙauna sannan ta fice ɗauke da basket ɗin data haɗa komai cikin yauƙinta da iya taku…
Fitowarsa da ga bedroom yayi dai-dai da shigowarta. Sanye yake shima cikin ƙananun kaya masu taushi da rashin nauyi yanata bulbula ƙamshi. Ta sakar masa murmushi da faɗin, “Good morning Soulmate”.
Idanunsa ya lumshe da jinjina mata kansa, laɓɓansa shima da ɗan murmushin. “Morning dear! how are you?”.
“Alhmdullh” ta faɗa tana kauda kumburarrun idanunta da yakema kallon tuhuma, tasan shi mutum ne mai saurin fahimta, amma zatai duk yanda zatai domin hanasa hakan a wannan karon. Hanunsa ɗaya dake cikin aljihun wandonsa ya zare dai-dai yana ƙarasowa gareta, ya amsa basket ɗin. Batai musun bashi ba. Cikin zolaya da cigaba da kafeta da idanunsa dake tsumata ya kashe mata ido ɗaya.
“Ai da nasan haka zan dinga samun gatan nan a wajenki dana jima da ƙara aure gaskiya”.
Har cikin ƙwaƙwalwar kai maganar nan ta soketa. Harta kasa ɓoyewa fuskarta ta canja, amma sai tai ƙoƙarin saita kanta ta hanyar maida abun wasa ta hararesa da juya baya kamar tayi fushin wasa. Basket ɗin ya ajiye ya rungumota ta baya yana ɗaura habarsa akan kafaɗarta da murmushi bisa fuskarsa. “Juyawa Shareff ɗinki baya yana nufin lalacewarsa matata. Amma da gaske wannan aure yamun ranar zama ɗan gatan Fadwa”.
Ita shaidace bai iya ƙaryaba, ko tace baya ɓoye-ɓoye. Duk abinda ya fito a bakinsa koda mai ɗaci ne shine iya gaskiyar dake zuciyarsa. Ta sani tayi kuskure a baya na gazawar bashi kulawa, duk da taci matuƙar burin hakan a garesa kafin aure……
Jan hanunta da yay ya katse mata tunani, ya zaunar da ita a kujera yana faɗin, “Kinga jirani anan ina zuwa”. Kafin ta samu damar tuhumarsa harya fice. Ta bisa da kallo zuciyarta na ƙuna har hawaye na ciko idanun nata. Duk da gargaɗinta da zuciya keyi haka ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsa wai ko zata samu sauƙin ranta idan bataga alamar abinda take tsoro ba…..
★Da sallama ya shigo akan laɓɓansa idanunsa nabin ko’ina na falon da kallo, yayinda ƙamshin dake tashi ke masa maraba da amsa sallamar tasa. Samun falon shiru bai hanashi cigaba da kutsa kai ciki ba har zuwa bedroom ɗinta. Anan ɗin ma dai tsaf, sai dai babu alamar tana a ciki. Ya ɗanyi jimm na tunani sannan ya fito, falon ya dawo ya nufi hanyar kitchen…
Tsaye take ta juyama ƙofa baya tanata kici-kicin saita sabon oven da take son ɗumama meat pie da take son yin breakfast da shi. Bluetooth ne a kunenta tana sauraren sabuwar waƙar mawaƙin nata da wata ƙawarta ta tura mata daga can malaysia, hargitsin bikin nan ya hanata zaman ji sai yau ta tuna da ita. Atamfa ce jikinta, wadda akaima ɗinkin fitted gown da yabi jikinta ya kwanta luff da fidda surarta matuƙa tamkar an zanata da pen, daga cinya zuwa ƙasa rigar ta buɗe matuƙa har tana zan ƙasa daga can baya. Bata cika son irin kayan nan ba, amma gargaɗin Mamie da nasiharta ana gobe za’a kawota ya sata daurewa ta tsara zata dinga sakawar insha ALLAH koda ba kullum ba. Bata iya ɗaura ɗan kwali ba, dan haka a maimakonsa saita kawo hula ta saka irin ta zamanin nan mai kama da ɗan kwalin. A jikinta taji tamkar ana kallonta, gabanta ya faɗi ta juyo da sauri dan dama dauriya kawai take na kasancewa ita kaɗai……….✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107