BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

49

………Da sauri ya saketa yana yarfar da hanun, tako kwashe da dariya ga hawaye sharɓan a fuskar. “Kaɗan ma ka gani indai nice Yaya”. Ta faɗa cikin riƙe ƙugu da murguɗa baki.
    Idanunsa da har sun kaɗa alamar cizon ya shigesa matuƙa ya ɗago yana kallonta da kaiwa zaune cikin kujerar dake kusa da shi. Ƙoƙarin barin falon tai tana masa gwalo, zamewa ƙafarta tai a dalilin turza carpet tai baya zata faɗi. Da ƙyar ta samu nasarar dafe kujerar da yake zaune, samun rinjayen jikinta a nasa ya tilasta mata zubewa kansa inba hakaba dole sai ta faɗin. Jikinta har rawa yake wajen son yunkurawa ta tashi ya sake saka ƙafa ya taɗota ta koma. Ya saƙalo hanunsa ta saman ƙugunta ta yanda bata isa sake ko yunƙurin tashin ba, fuskokin su gab suna shaƙar numfashin juna. Idanunta dake cikin gilashi ta shiga ƙyafta masa zuciyarta na wani irin bugu da sauri-sauri saboda bata taɓa tsintar kanta a cikin irin wannan halin tare da namiji ba bayan shi, ta sake yunƙurin tashi gaba ɗaya dan kunya ta gama dabaibaye rayuwarta bakinta cike da tsiwa tana motsashi sai dai bayajin abinda take faɗa. Ƙafarsa yasa ya sake harɗeta da manneta da jikin nasa dai-dai lokacin da Fadwa ke ƙoƙarin shigowa falon ɗauke da ƙaramin basket a hannu, cak numfashinta ya tsaya, sallamar datai niyyar rangaɗawa ta maƙale a maƙoshi.
      Idon Anaam yaga Fadwa sarai, dan haka ta dakata daga yunƙurin tashi da takeyi duk da tsumar da jikinta ke mata, shiko da bai lura da Fadwan ba saboda baya ya bata kaɗan sai ya kamo haɓar Anaam ɗin tare da sake matso da fuskar tasa gab da tata. Ya ɗan ɗage girarsa ɗaya a sama yana kallonta cikin tsakkiyar ido.
     “K bakin ki bazai taɓa mutuwa ba ko?”.
      A salon da yay maganar ba ƙaramin tsargawar zuciya ya saka Anaam ba, sai dai tai matuƙar daurewa wajen tura masa bakin nata sabida tunawa da Fadwa a wajen. Lips ɗin ya ɗalla da ɗan yatsa, babu shiri taja kanta baya da ƙoƙarin dafe bakin ya hana hakan ta hanyar buge hanun ya ɗaura nasa lips ɗin akan nata. A matuƙar bazata abin ya zomata. Cikin tsumar jiki ta ƙanƙamesa zuciyarta na luguden daka a ƙirjinta tamkar zata wantsalo dan wannan shine second kiss nata a tsayin rayuwarta duk da kuwa ta kasance girman cikin jajayen fata. Ko saurayi irin na school ɗin nan Anaam bata yarda tayi koda ance ana sonta, sai takai ma tsiwarta da rashin ragowa yasa matasan samarin makarantar tasu na shakkar tararta da abinda ya shafi soyayya, kaɗan daga aikinta ta maka tatas a gaban kowa ita ba ruwanta, hatta da ƙawa ɗaya gareta itama dan hali yazo ɗayane shiyyasa suke shiri, dan itama fitinanniya ce ta bugawa a bangon class. Hakama data shiga jami’a bata shiga sabgar kowanne namiji duk nacinsa kuwa inba akan abinda ya shafi karatu bane ba.
       Ta kowanne ƙofar jininta saƙonsa shiga yakeyi jikinta, ya kashe dukkan wani sauran kuzarinta da yunƙurinta, sai da ya barta dan kansa ta samu damar kife kanta a ƙirjinsa tsigar jikinta na tashi, shekara ashirin da uku ba shekara sha uku bace, itama mutum ce tamkar kowa kuma lafiyayya dake samun ingantaccen abinci mai gina jiki, ga kwanciyar hankali, giɓin rashin mahaɗinne kawai tattare da ita dama. Samuwarsa gareta a halin yanzu kuwa tamkar motso mata dukkan abinda ke ɓoye a cikin jininta ne ko tana so ko bata so.. Hannayensa duka biyu ya ɗaura a saman bayanta, tare da kai bakinsa saitin kunenta murmushin dake ta ƙoƙarin son bayyana kansa a fuskarsa na ƙoƙarin kufce masa.
       “Daga yau da wannan zan dinga punishment ɗin bakin rashin kunyar tunda shi idan aka faɗa sai ya maida”.
     Janye kanta ta rinkayi dan yanda yake maganar a cikin kunenta da busa mata numfashi sai yake neman sake hargitsa mata lissafinta. Nasarar janye jikinta ta samu ta silale ƙasan kafafunta, shiko ko’a jikinsa, sai ma umarni daya bata cikin kame murya.
          “Malama tashi ki bani abinci, muje kuma ki gyara bedroom ɗin can yau komin dare”.
     A yanda take kai a kife cikin cinyoyinta ta gallaro masa harara da murguɗa baki, sai da taja wasu sakanni sannan ta miƙe bisa shawarar zuciyarta, dakewar kuwa tai itama, tai kicin-kicin da fuska ta kuma ƙi yarda tako kalla sashin da yake. Bataga Fadwa ba yanzu, da alama tuni taba kafarta abinci. Haka kawai taji murmushi ya suɓuce mata ta ɗan harari ƙofar tamkar har yanzu tana a wajen ne. 
      Fuskarta a gefe tace, “Nifa banda abinci anan”.
   Ɗan dagowa yay daga latsa wayar da yake ya dubeta, sai kuma ya dubi ledar daya shigo da shi ɗin wadda yasan sarai itama ta gani ɗin. Sake maida kansa yay ga wayar batare da yace komai ba. Jitai kamar ta makesa dan duk tana kallonsa ta gefen ido, batare da ta sake magana ba ta ɗauka ledar ta nufi kitchen tana kwaikwayon yanda yay magana cikin bada umarni shi a dole mai kame girma bayan ya gama tsotse mata baki.
       Bayan wasu mintuna ta dawo da abinda ke cikin ledar cikin plate data juyo sai ruwa da lemo da cup duk ta haɗo a saman tray. Ta ajiye a saman centre table batare data yarda ko sau ɗaya ta kalla sashen da yake ba. ALLAH ya sota ma waya yakeyi, takoyi wuff tabar wajen. Da kallo ya bita harta shige, ya ɗauke kansa da ɗan furzar da numfashi yana cigaba da sauraren Fharhan….

        ★Gaba ɗaya brain ɗinta kusan daina neman yin aiki tayi, kukan da take sonyi dan taji daɗi ma yaƙi fitowa ko ɗigo ɗaya. Tasa ƙafa ta hankaɗe basket ɗin abincin data tafi da niyyar kaiwa Anaam ɗin saboda ganin Shareff ya shiga can, dan koda ya dawo sashenta ya fara shiga ya kai mata ledarta, da tace masa ga abinci cewa yay ya ƙoshi tunda bai daɗe da cin na rana ba. Taji haushi amma ta dake harya barota fuskarta da murmushi, yana fita ta zabgama ƙofar harara da faɗin, “Munafuki” (Ƴan uwana mata a kiyayi zagin miji koda a zuciya????). Harta zauna zata buɗe ledar daya kawo matan sai kuma ta mike, abincin data shirya domin shi ɗin ta tattara cikin ƙaramin basket ta ɗauka da nufin zuwa ta kaima Anaam a gabansa, Cikin ranta har tana saƙa abinda zai faru dan tayi shirin kunna Anaam ɗin ta yanda yau ko kwana a ɗaki ɗayan ma sai ya gagaresu duk da tasan iya shi ɗinne zai faru a tsakaninsu saboda ta yarda da su aunty Malika ɗari bisa ɗari. Amma maimakon hakan sai tai gamo da abinda ya nema saka zuciyarta faɗowa ta baki, wai yau mijinta, abin sonta Al-Mustapha ne rungume da yarinyar data tsana fiye da komai a rayuwarta yana kissing. Ta rumtse ido da sauri komai na dawo mata tamkar a film, ƙara ta saki dayin cilli da throw pillows ɗin dake a kujerar da take ƙasa, hawayen da take ta faman son zubo mata na rige-rigen sakkowa a bala’in guje…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button