BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

     Tun fitowarsu take faman kaikawo a harabar gidan, dan ko sashen Fadwar sun gagara komawa tsabar mamaki da jinjina ƙwarewar iskancin Shareff ɗin a yau. Yaron da ko ido bai cika ɗagawa ya kalla mutane ba shine yay musu wannan baƙin iskancin. Ina bazata iya haƙuri har sai sunje gida ba, dole ne ta kira Mommy kam ai. Takai wayar kunenta tana faman kaɗa ƙafafu da jijjiga jiki na tsantsar bala’i. Cikin sa’a aka ɗaga mata gab da zata tsinke.
      “Sakina har kun isa gidanne?”.
Mommy ta faɗa tunkan aunty Sakinar tace wani abu. Aiko cikin matuƙar ɗacin murya ta tare numfashin Mommy din da faɗin, “A dole Mustapha kam yafi karfinki wlhy Yaya Nafi! Dan tabbas babu makawa an wanke an basa ya sha.”
     Ƙirjin Mommy ya buga da ƙarfi, sai dai kafin tace wani abu Aunty Sakina ta cigaba da bata labarin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Ta ƙare da faɗin, “Zama dai kam bai gammu ba dan wannan yarinyar tafi uwarta hatsabibanci. Nan gaba babu makawa zaima iya cewa kwanciyar aure zaiyi da ita a gabanki saboda ya tabbatarma duniya shi ɗin tantirine na gask……” Ƙitt!! Wayar ta yanke. Tai saurin cirota a kunenta tana kallo a tunaninta ko kuɗine suka ƙare. Ƙoƙarin siya tai ta banki ta ƙara kiran Mommy ɗin. Sai dai kuma number busy ake nuna mata alamar waya take ko kiran wani…..

       Ring ɗin wayarsa ne ya sake sashi buɗe idanunsa da har yanzu ke’a rufe. Ya kafe fuskar wayar da kallo tamkar mai tsoron ɗauka ganin sunan First Luv ruƙu-ruƙu na yawo. Rabon da suyi koda waya ne harya manta, ya kuma tabbatar gargaɗin da yayma su Aunty Sakina ya risketa ne matsayin saƙo. Bazai iya ƙin ɗaga kiranta ba koda yana jin tsoron dukkan wani furuci daga bakinta, kimarta da girmanta sun wuce a musalta a cikin idanunsa da zuciyarsa. Hannu ya kai ya ɗaga tana gab da tsinkewa, yakai kunen nasa cikin ƙarfafa kai….
     “First luv barka da safiya”.
“First ubanka ba first luv ba. Al-Mustapha wlhy ina gab da jamaka kalmar ALLAH ya i…..”
       “Please First luv, abeg kar kice haka dan girman ALLAH.”
“Idan ka sake kirana da sunannan ALLAH sai naci ubanka. Kuma kazo ina nemanka idan ba hakaba ka bari na tako ƙafata gidanka da kaina yarinyar nan na a ciki wlhy wlhy wlhy kadaiji na rantse ko! Sai na jamaka ALLAH ya isa da manyan baƙi no-no na daka sha dan bakai kaɗai na haifa ba balle ka ɗauramin hawan jini”.
       Harshensa har sarƙewa yake wajen faɗin, “Shi… Shike nan naji zanyi, zan zo, amma kimun alfarma Mommy dan ALLAH sai gob…….”
     “Alfarma ubanka, Al-Mustapha ni kake son tozartawa a idon maƙiyana dai ko? Kana nunama duniya mace ta fini daraja da kima a idonka?”. Ta faɗa tana fashe masa da kuka. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi, ya girgiza kai tamkar yana a gabanta. “Mommy wlhy babu wata mace da darajarta zata ko kama ƙafarki a wajena. Dan ALLAH ki fahimceni Mommy ina a tsaka mai wuya……”
      A fusace ta yunƙuro zatai magana Gwaggo ta fisge wayar. “Nafisa wai kin rasa hankalinki ne halan?! A tunaninki wannan butsutsun naki akan Mustapha shine mafita ta ƙarshe da zakibi wajen raba auren?!!……”
         Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da lumshe idanunsa ya saki wayar a jikinsa batare daya ƙarasa jin abinda Gwaggon ke faɗa ba. Dan kuwa tabbas a wannan gaɓar ta taimakesa taimako irin wanda bakinsa bazai iya maimaita faɗa ba, sosai al’amarin Mommy ke daɗa tayar masa da hankali, ya rasa ta inda zai kama domin shawo kanta akan wannan aure. Har yanzu yarasa gane minene takamaimai laifin su Abie a gareta da take musu irin wannan ƙiyayyar (Niko nace Shareff a haka ta tashi, tun tana ƙaramarta an riga an cusa mata ƙinsu. Haka ɗan adam yake, a duk lokacin daka koyar da shi wani abu ƙyaƙyƙyawa ko mummuna yakanzo ya fika iyawa. Iyaye tabbas muna kuskure, kuskuren da shike saka ƴan ubanci a zukatan ƴaƴanmu tsakaninsu da ƴan uwansu. A kullum baki da aiki saina aibanta kishiyarki gaban ƴaƴanki, baki da aiki sai na zaginta da nuna cutarki take zaluntarki take bata sonki, bata ƙaunarki, maƙiyarki ce kuma a gaban ƴaƴanki. Tayaya kike tunanin bazasu tsaneta su tsani ƴaƴanta fiye da yanda kike tsanarta ba, saboda ke ra’ayin ƙinta ya shigekine da girmanki da hankalinki, idan kin so zaki iya yaƙarsa, suko kin raini zukatansu ne akan wannan ƙiyayyar, dolene su dawwama da ƙinta da ƙin duk wani abinda ya shafeta koda bata aikata musu komai ba na ƙi ɗin. ALLAH ka gafarta mana ka gana damu gaskiya koda bazata mana daɗi ko zuwa dai-dai da son zukatanmu ba).
        Anan falon yabar lap-top ɗin da takardun ya fice, koda ya fito su Aunty Samira sun wuce dan baiga motarsu ba. Motar ya shiga shima ya fita a gidan, dan yana buƙatar yin nesa da su har zuciyarsa ta huce. Haka yake baya son yanke hukunci cikin fushi, ya gwammaci yin nesa da abu a duk lokacin da zuciyarsa ta harzuƙa. Asibiti ya nufa wajen Dr Jamal, sai da ya shigo cikin asibitin sannan ya kira wayarsa..
     Daga can Dr Jamal yace, “Ka shigo mana, ni kaɗaine ma a office”.
   Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yanke wayar, bai cika san buɗe cikinsa ga kowa ba. Amma dai mutane biyunnan sun wuce abokai kawai a garesa aminaine na gaskiya. Daga Dr Jamal har Fharhan abokansa ne tunna ƙuruciya, koda yabar ƙasar kuma basu yarda juna ba. Basu da abokin shawara sama da shi, duk da shi yakan jima basuji nasa cikin ba saboda yanada zurfin ciki matuƙa. Na ukunsu kuwa shine Khaleel, duk da kasancewarsa ƙani a garesa hankalin yaron da nutsuwarsa kansa ya kallesa tamkar aboki, sannan shima Khaleel ɗin bashi da wani amini sama da shi duk da yana amsa sunan yayansa ne.
      Sai da yay knocking aka bashi izinin shiga sannan ya shiga. Dr Jamal na zaune a kujerarsa ya amsa masa sallamar da yay fuskarsa da murmushi. Cikin danne kishin rashin Anaam yace, “Ango kasha ƙamshi”. Harararsa ya ɗanyi ya ɗauke kai, ya zube cikin kukerar dake gaban desk ɗin Dr Jamal ɗin yana furzar da iska mai nauyi. Dr Jamal dake binsa da kallo danya fahimci damuwa a fuskar abokin nasa ya miƙa masa hannu sukai musabaha.
     “Wai yana ganka haka kamar mara lafiya? Ko jikinne har yanzun?”.
Kai ya girgiza masa, sai dai baice komai ba. Dr Jamal ya tsura masa ido na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe ya ɗakko masa ruwa. Baiyi musu ba ya amsa, murfin ya ɓalle ya kai bakinsa. Tass ya shanyesa yana dire robar da lumshe idanu ya sake lafewa a kujerar yana sauke numfashi. Kusan mintuna uku suna zaune a haka shiru, kafin ya buɗe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya canja ya kalla Dr Jamal daya tsura masa ido…
      “Kai kurwana da ɗaci irin wannan kallo haka”.
Dariya Dr Jamal ya kwashe da shi. “Ɗan wulakanci, inda ni maye ne ALLAH kamun kaɗan a ci ɗan iska kawai”.
     Murmushi yay a karon farko da gyara zamansa. “To zama mayen mana kaga idan zan ciwu a wajenka mara mutunci”.
       Dr Jamal yay dariya kawai. Sai kuma ya miƙe daga kujerar zamansa ya dawo inda Shareff ɗin ke zauna shima ya zauna suna facing juna. “Mike faruwa? Damuwa ta kasa ɓoyuwa a kan fuskarka my Dude”. Nannauyan numfashi ya sauke da ɗan ɗage kafaɗa, “Bani da wata damuwa kawai dai nace bari in gaisheka”. Idanu Dr Jamal ya tsura masa fuskarsa na canjawa zuwa jin haushi……..✍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button