BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

   “Kinga nutsu ki saurareni Fadwa. A yanzu haka gani tare da Aunty (Gwaggo halima) kuma duk tana jinki, dama nazone zan amsa sako da zamuje wani waje saboda ke”.

   Sunan maman ta fara kira cikin kuka, Gwaggo Halima da tun fara bayanin Fadwa wutar kanta ya ɗauke saboda shi babba duk inda yake babba sunansa, tuni zuciyarta ta hasko mata wani abu ya shiga tsakanin Shareff da Anaam kenan, dukan kokarinsu na hana faruwar hakan bai yuwuba kenan, taja numfashi. “Fadwa kinga nutsu kuka ba naki baneba. Karki damu damun bayanin komai na riga na sani domin ni na aiko su Safarah wajenki dama nace ne karsu faɗa miki. Yanzu ki jira zamu kiraki ina zuwa…”

  Kafin tace wani abu aka yanke wayar, ta zube a bakin gado da sake fashewa da kuka mai cin rai….


   Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin, yanzu dai taso nuna jarumtar hanashi taɓata amma ina hakan bai yuwu ba. Dan taku biyu kacal ta nema zubewa tamkar ta fasa ihu dan zafi. Dole dai ya ƙaraso ya ɗauketa.

   “Ni dai Yaya ka saukeni zan iya”.

Ta faɗa tana sharce hawayen dake ambaliya akan fuskarta saboda hango Dr Jamal dake nufosu alamar yasan da zuwan nasu. 

  Murmushi yay da kashe mata ido ɗaya “Da wannan tafiyar tonamin asirin ne zaki iya?”. 

   Idanunta ta rumtse kunyar duniya a kanta, dan gani take kowa zai iya sanin miya faru da ita ne. Da taimakon Dr Jamal suka sami ganin Dr Bilkisu a sahun farko. Ganin Anaam taƙi amsa tambaya ko guda ɗaya a gaban Shareff daya tsatstsareta da ido yasa Dr Bilkisu kallonsa da ɗan murmushi. “Alhaji Al-Mustapha ko zaka ɗan bamu wajene dan naga patient ɗin tawa kasancewarka tare damu ya hanata cewa komai”.

    Ido suka sake haɗawa da Anaam. Tai azamar janye nata da tura masa baki. Mikewa yay yana murmushi batare da yace komai ba ya fita. Ko’a bayan fitar tasa ma sai da Dr Bilkisu ta sha fama sannan Anaam ta amsa mata wasu daga cikin tambayoyin nata tana faman sinne kai, a yanda ta fahimci ta kasa zama da ƙyau tai hasashen abinda Anaam ɗin ke faman ɓoyewa. Batace komai ba ta taimaka mata zuwa gadon da suke duba marasa lafiya, ganin tana neman ɗage mata doguwar riga ta riƙe da sauri tana girgiza kanta………..✍
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

57

………A hankali ya tura ƙofar ɗakin laɓɓansa na motsawa alamar sallama, kamar mai irga steps ɗinsa ya cigaba da shigowa cikin ɗakin idonsa akanta duk da ƙudundune take cikin bargo, zaune ya kai gefenta tare da kai hannu ya yaye bargon. A yanda ta miƙe zumbur da alama bata san da shigowar tasa ba. Idanunsa sukai ƙyaƙyƙyawan ganin daya sakashi jan numfashi a fisge, dan shaiɗaniyar rigar jikinta bata bar komai a sirrance ba, a waccan ranar ya ganta, sai dai a yau rigar tafi bayyana masa komai har idonsa na neman tsolewa. Ita kuma data manta a yanda take komawa tai zata kwanta cikin taɓe fuskarta dan wani haushinsa da takaicinsa ne suka sake kamata. Riƙota yay, ta shiga fisgewa da fashe masa da kukan ƙarya.
      “Ni ka sake min hannu, kuma bana son ganinka ka koma can wajenta ita matar son naka, ƙarewar kiss kace ta cinyeka mana…”
   Sassanyar ajiyar zuciya ya saki, komai baice ba, bai kuma saki hanun nata ba sai dai murmushi ya suɓuce masa akan fuska kaɗan, ta cigaba da turesa da ƙoƙarin kai masa ƴan ƙananun duka a damtsen hanunsa. Bai hanata ba yana dai ta ƙoƙarin danne dariyarsa. Ganin abun nata bana ƙare bane ya rungumeta gaba ɗaya ya tura a jikinsa. Duk yanda taso cigaba da fisge-fisgen ya hana hakan, ya fara kai ma fuskarta da wuyanta kiss har yanzu murmushi bai bar fuskarsa ba. Ƙarfin kukanta ta ƙara da ture masa fuska amma yaƙi ya daina, sai da yay mai isarsa sannan ya barta da ƙara matseta a jikin nasa.
      “Shikenan sai bori ya ƙare an biyaki kiss ɗinki, ai ban san kina so bane amarya mai aji, nazo da ƙoƙon bara yau a barni na samu tubarrakin wannan tsadar tsada sarauniyar mata kona samo tukuycin nan da kikai alƙawarin badawa”
    Zabura tayi da nufin turesa tana waro ido sosai waje jin wai ashe duk yaji mita faɗa ɗazun, amma yanda ya naɗeta a jikin nasa yasa baiko motsa ba. A karan farko ya sakar mata siririyar dariya cikin kunnenta da cizonsa da haƙori. Ƙara ta saki kaɗan duk da bawani zafi na azo a gani taji a cizon ba.
“Ni dai wlhy ka tashi ka fita yaya, kaje ka ƙarata da matarka ni duk abinda na faɗa iya laɓɓana ne kaima kuma ka san…”
Ruff ya rufe bakin nata da nashi tare da ƙara matseta gamm ya fara mata wani salo daya nema zuƙe numfashinta gaba ɗaya taja ajiyar zuciya tankar mai shirin shiɗewa. Salo ne da bai taɓa kwatantashi ga wata bama, tun tana da zarrar yin yunƙuri harya ci galaba a kanta ta koma masa laƙwas sai dai ta kasa maida murtani sai ma jikinta dake tsuma.
“Yaya Please ALLAH wasa nake mata”. Ta faɗa a wahale tana janye bakinta daya sassauta riƙewa a nasa. Ganin yana neman sake cafkowa ta tura kanta cikin ƙirjinsa ta kanannaɗesa.
Murmushi ya saki da mata zobe da hannayensa, furzar da ƙaramar iska yay da ɗaura bakinsa kan kunenta. Cikin wata irin kasalalliyar murya mai ɗaukar amon sauti daga bututun gudun jini zuwa ƙahon zuciya ya fara fidda aman sauti “Haba autar mata kiji tausayin yayanki mana ki basa dama ya tabbatar miki ke wacece a aikace. Ko kina buƙatar sai naje ƙasa ne bayan kin gama min ɗaurin da wata ƴa mace bata taɓa yima namiji ba.”
Kasancewar da yaren malay yake maganar babu shiri ta ɗago ruɗaɗɗun idanunta a dalilin jin furucinsa. Cikin tsakkiyar ido suke kallon juna na kusan mintuna biyu, daga ita har shi tsuma jikinsu yake kowa da abinda ke masa kaikawo a zuciya, lips ɗinta suka shiga motsawa kamar zatai magana amma sai ya hana hakan ta hanyar haɗe goshinsu waje guda. Baya buƙatar bata wani space a wannan gaɓar, dan ya tabbatar hakan zai iya zame masa kuskure wajen tsaiwar amsa ɗunbin tambayoyin daya hanga cikin idonta da bakinta.
     Duk da a zaune suke gangar jikinsu ta kasa ɗaukarsu, dole yakai kwance da ita jikinsa na matuƙar rawa da tsuma irin na an daɗe ba’a haɗuba, daɗin daɗawa kuma ango yake, a yau zai sake zuwa irin duniyar da bazai taɓa mantawa da ita ba duk da a waccan gaɓar shima ɗin ya jigatu, ya kuma wahala kasancewar na farko a garesa, a yanzu kam sai dai ya zama malamin wasu inda ana koyarwa a aji.
       Ya matuƙar rikita hankalin Anaam da wani sabon salo. Ta shiga ruɗani irin wanda baka iya banbance fari da baƙi sam. Ita yanzu ba Anaam ɗin Abie da Mamie bace, wata sabuwar Anaam ce a wata duniya da hasashe bai taɓa kaitaba koda a lissafin hange. Ita ba Anaam ɗin data ɗauka alwashin jiran cikar watanni uku bane na barin gidan Yayanta. Ita ba Anaam bace dake tuna da Yaya MM take tare. Ita ba Anaam ɗin dake tuna bayan ita akwai wata mata tare da shi ba ce, ita ba Anaam ɗin dake buƙatar ɗunbin amsoshin tambayoyinta daga garesa bace, ita ba… Ita ba… Da yawa da bazata iya tunawa ba a karan kanta balle wani tsarinta ko burinta..
     Tuni ya jima da rabata da rigar kamar yanda ya raba kansa da tasa suturar shima, ya naɗesu a cikin bargo tare da mirginawa da su tsakkiyar gadon. A daidai gaɓar da Anaam ta dawo hayyacinta kenan dan a yanzu an ɗauki wani layine daya sata zaburowa a razane ta ƙwalla ƙara da ƙanƙamesa jikinta na rawa ta fara son turesa cikin magiya da roƙo…. Da gaske baya jinta, sai dai rufewar idon tasa bata hanashi fara ambaton addu’ar da MANZON ALLAH ya horar damu karantawaba yayin ziyartar juna……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button