BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai jikinta ke ɓari, tana saki wani irin nishin kuka mai ban tausayi irin na wanda yay matuƙar galabaita da jigatuwa. Muryarta tayi ɗashewar da ba’a iya jin wani furuci daga bakinta. A hankali ya mirgino gareta, a jikinsa ya maidata ya rungume. Lallashinta yake son yayi, hawayenta yake son tsaidawa amma ya kasa. Ƙara tsuma jikinsa yakeyi da wani irin karsashi da zuciya ce kaɗai mai ajiye da wannan kundun sirrin bawai gangar jiki ko kalaman kan harshe ba. Bashi da wani zaɓi face sake matseta a cikin jikin nashi yana mai jujjuya mata kansa duk da a cikin ɗan hasken da suke na lamp bazai wadatar da idaniyar da yake da yaƙinin a rufe take iya ganinsa ba.
“ALLAH yayi miki albarka”.
Ya iya furtawa da ƙyar kuma a fisge yana sake matseta tamkar ya tsaga fatar jikinsa kawai ya turata ya huta. Tsahon lokaci ya kasa yanke shawarar abinyi na gaba, itako tana faman cigaba da juya kanta dake a ƙirjinsa laɓɓanta na motsawa a hankali alamar akwai abinda take faɗa da ba’aji, hawayenta masu ɗumi da zafi na cigaba da sauka a ƙirjinsa kai kace zata iya ƙarar da su ne a wannan dare baki ɗaya.
Jin kamar jikinta ya saki ya saka zuciyarsa harbawa da ƙarfi, babu shiri ya miƙa hannu ya kunna fitilar ɗakin. Sosai firgici ya bayyana akan fuskarsa, yatsunsa biyu ya ɗaura a kan hancinta. Da gaske bata numfashi. Zuciyarsa tai wani uban tsalle tamkar zata fito waje. Kansa ya dafe da cije lips ɗinsa da ƙarfi yana ambaton sunan ALLAH. Sai kuma ya shimfiɗeta saman filo ya fara laluben abinda zai suturta jikinsa. Rigarsa ya samo da ƙyar acan ƙasa, baiko saka botiran dai-dai ba ya sauka zuwa gefen gadon. Ruwan daya shigo da shi ya ɓallema murfi, ya zuba a tafin hanunsa ya shafa mata a fuskarta dake jage-jage da hawaye. Babu alamar zata kawo numfashi. Ruwan ya gumtsa ya fesa mata a fuska. Gaba ɗayanta ta zaburo tare da jan numfashi mai ƙarfi. Da zafin nama ya tallaffota ta koma cikin tafin hanunsa, “Juwairiyya!”.
Ya faɗa cikin sarƙewar harshe…
Jin bata amsa ba kamar ma ta ƙara koma masa lakaf ya sake girgiza mata kai ta hanyar rike haɓarta da sake kiran sunanta cikin nutsuwa.
“K! Juwairiyya K!?”.
Siririn kuka ta sakar masa, murya a ɗashe tace, “Zafi, wayyo Mamie na”.
Ta furta da ƙyar da buɗe idanunta kaɗan sai kuma ta maida ta rufe kanta na juyawa kaɗan-kaɗan.
“Ya ALLAH! ALLAH!!”.
Ya faɗa da sake girgizatan, sai kuma ya mannata da ƙirjinsa ya ƙanƙame ya kama hanunta ya fara murza tafin cikin kulawa. Wani bahagon numfashi ta fusga azabar zafi na ƙara ratsata. Sai dai bata da ƙarfin koda ƙanƙamesa balle gane a halin rayuwa take ko mutuwa. Yasan Anaam nada raki, sannan akwai ƙarancin ƙwarin zuciya na ɗaukar wahala a tattare da ita saboda yanayin rayuwar data tashi. Ita ɗin ƴar gata ce, rainon madara da biscuits da chocolates????, bata taɓa fuskantar makamanciyar wahala irin wannan ba a rayuwarta. Abinda ta sani kawai taci ta sha ta tafi makaranta, koda ya kama tayi wani aiki bamai yawa bane da zai tabbatar mata da ana wahala a duniya. Gashi kuma yasan baizo mata da sauƙi ba sakamakon tunaninsa shekarunta zasu iya ɗauka, bai san abun ba’a shekarun yake ba dan ƙarfin zuciya da juriyar ɗaukar wahala babu ruwanta da shekaru…
Sabon ragwanci da raki ya ƙara ɓarkewa a toilet yayin yake taimaka mata wajen samun nutsuwa dan ya fahimci wannan itace masalaha ta farko daya kamata ya bata agaji da ita. Kuka take masa sosai irin wanda yafi na farko dan a ɗazun wahala ta hanata yin kukan. Yanzu kam saita samu damar ɓarje guminta wajen yinsa fiye da abinda takeji. Rashin ƙarfin jiki ya tilastata sallama masa dole yana jujjuyata a yanda yake so cikin ruwan zafin. Koba komai ta ɗanji sassauci, sai dai hawayeta sun gagara tsayawa dan su kaɗai ne abinda take iyayi wajen nuna irin raɗaɗin da takeji da galabaitar da rayuwarta da yayi. A cikin ruwan ya barota ya fito, ya kintsa gadon ta hanyar canja bedsheet sannan ya koma fito da ita. Har cikin rai tausayi take bashi, duk da ya fahimci rakinta ne gaba-gaba wajen sake girmama narkewar tata. Koma dai minene ai shi ya takaloma kansa tunda yasan hali. Tun yana hasashen zatai haƙuri tai shiru sai saɓanin haka ya biyo baya, dan kuwa ƙiri-ƙiri ta hanasu barci sai gabanin asuba da ɓarawon yaci galaba a kanta. Kansa ya girgiza kawai, dan bai taɓa sanin darun yarinyar nan da rikicinta yakai faɗin haka ba sai a yau. Rashin barcin da wuri ya jawo musu makara. Bai fara tashinta ba sai da ya idar da tasa sallar, abinda yake gudunne kuwa ya faru, dan rikice masan ta farayi da kuku wuwu. Haka kawai yake jin nauyi da kunyarta shi kansa, domin yasan dai magana ta ƙare tunda a daren jiya ta gama ganin ƙarshen girmansa duk da matsayin ƙanwa da take da shi a garesa. Da farko ya lallaɓata har tai salla, ganin fa bata san zuru ba ya rumtse ido cike da borin kunya ya balbaleta da masifar da bata kai ciki ba, dan da ƙarfin hali yake yinta kawai….
“Kin isheni fa da kuka. Idan baki rufamin bakinki da kukan banzar nan ba ALLAH yagalgalaki zanyi da safen nan, dan na fahimci kukan naki harda na rashin ƙoshin dalilin yinsa…”
Kukan ta sake fashe masa da shi tana duƙunƙune kanta cikin bargo, dan hatta muryarsa razani take saka mata a zuciya. Tsoronsa takeji mai girma da tsananin shakkarsa. Ta cigaba da hawayenta batare da barin sautin kukan na fita ba sai dai yana jin yanda take jaa da shaƙar ajiyar zuciya tamkar zata shiɗe. Tashi yay ya fita, mintuna kaɗan sai gashi da kofin shayi. Yasan halin butsutsunta, dan haka ya ɗaure fuska cikin bada umarni yace ta tashi. Duk yanda taso zama da ƙyau domin shakkarsa ta gagara hakan, dole sai jinginata yay da jikinsa zuciyarsa na raya masa akwai matsala kenan. Da kansa ya bata tea ɗin tana sha da ƙyar, ko rabi bataiba tace ta ƙoshi. Bai barta ba har sai da ta ƙara sha, ya bata paracetamol dan jikinta akwai zazzaɓi. Kwanciya yay da sakata jikinsa yana shafa bayanta, sai kuma ya sumbaci kanta dake a ƙirjinsa da ƙara rungumeta da ƙyau, cikin lallashi ya fara magana a kunnenta…
“Kukan ya isa haka to mai tsadar tsada uhhmyim. Ko kina so a dinga kiranki raguwa ne? Jarumar mace bata irin wannan rakin da kike yi ai. Bakinki taf da tsiwa amma sai ragwantaka”.
Kukan ta sake fashe masa dashi da son turesa a jikinta amma bata da ƙarfi, yay murmushi da sake sumbatar kanta. “Oh ashe kinada sauran ƙarfi ma na wani zauna kallonki, bara na sake komawa kawai ko zan ƙara farauto baby na uku, dan insha ALLAHU jiya dai na samar da biyu da zakiyi tukuyci da su………✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Chapter 59
59