BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

game da ɗaure-ɗauren fuskar tasu. A hanun
kujerar da take kwance ya zauna,
“Tashi kisha. Kimmaci abinci kuwa?”.
Sai da ta ɗan saci kallon gefen Fadwa sannan
ta ɗan tura baki da narke fuska. “Ni banajin
ci”.
“Uhhm baƙya son ci, yarinyar nan ki ragetaɓaran nan naki, yanzu abincin ma sai kin
nuna masa hali? Yanzu dai kinga ba’a shan
magani sai da abinci, faɗamin mi zaki ci?”.
Kallonsa ta ɗanyi da juya ƙwayoyin
idanunta, sai kuma ta narke fuska da girgiza
kai. “Da gaske bana son ci, barci nakeji kawai”.
“Uhm-uhm fa, bana son zama da yunwa
sam! Ki dai sha ko fruits ɗin can ne idan Aysha
ta kawo. Zakisha ko?”. Ya ƙare maganar da
ranƙwafowa kanta yana sinsinar wuyanta. Ta
gefen ido ta saci kallon Fadwa, sai taga su
take kallo fuskarta ciɗin-ciɗin kamar zata
fashe har wani jajaja takeyi na alamar ɓacin
rai abunka da fari. Murmushi tai mai sanyi
dakai hannu ta shafi fuskar tasa a ranta tana
faɗin (Ashe kin san akwai ciwo ni kike yi masa
kiss a gabana, zan koya miki iya zaman
duniya). Hanunta da take neman janyewa ya
cafke da sauri yana maidashi akan tattausan
gashin kumatun nasa. “Kin yarda zaki sha?”.
“Ni dai ɗan kaɗan”.
Ta faɗa a shagwaɓe.
Da ƙyar ya iya jan numfashi, dan shagwaɓar
tata ba ƙaramin susutashi take ba. “Good
girl”.
Murmushi tayi da janye hanun. Riƙeta yay, ta
marairaice masa. “Nifa fitsari zanyi”.
“Okayy to ana buƙatar abokin rakkiya?”.Ta faɗa da zille masa tana ƴar dariya.
Bedroom ɗinsa ta nufa batare da ko sashen
Fadwa ta kallaba. Tana shiga ta zube a
gadonsa dan babu wani fitsari dama. Kawai
dai taba Fadwa space ne. Domin rama abinda
tai mata bashike nufin bazata mata adalci ba.
Kuma koba komai yanzu kawai ta nuna mata
cewar alwashinta tabbatacce ne akan mantar
da Yaya MM ita in har tana a tare da shi.
Shiko daga can da kallo ya bita har saida ta
shige, a hankali ya haɗiye murmushi kan
fuskarsa. Miƙewa yay kamar zai bar falon.
Tasan idan tai wasa da wannan damar zatafi
haka shan wahala. Kamar yanda Mama
(Gwaggo halima) ta faɗa mata ba haka ake
buƙata ba, taje ta shirya dashi kodan
kasancewar gobe ne zata amshi girki, suna
buƙatar tai aiki da wasu fitinannun maganin
mata da aka kawo dominta tun daga ƙasar
sudan.
“Dan ALLAH kayi haƙuri” ta faɗa da sauri
tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da tun ɗazun
take son su zubo ko zata samu sassauci.
Ratseta yay zai wuce tai azamar riƙosa. Bai
juyoba amma ya dakata. Ta share hawayenta
hanunta riƙe da nasa. “Dan ALLAH kayi
haƙuri, nasan nayi kuskure. Amma wlhysharrin shaiɗanne”.
Ransa a ɓace ya dubeta da wani mugun kallo
daya matuƙar neman gigitata. Saurin sakinsa
tai da girgiza masa kai. “Nasan nayi kuskure
amma dan ALLAH kayi haƙuri haka bazata
sake faruwa ba”.
“Tashi kibar min falo”.
“Please Soulmate dan ALLAH”.
Sallamar Aysha ce ta sakashi haɗiye maganar
bakinsa, ya koma ya zauna da amsa mata.
Itama hawayenta ta shiga sharewa idonta na
satar kallon ƙofar bedroom ɗinsa, dan
zuciyarta raya mata take Anaam na wajen
laɓe tana saurarensu. Sosai takejin raɗaɗi da
ɗacin hakan, amma taci alwashi komi zai faru
a yanzu ɗin bashi ne Anaam ɗin zataci itama
zata rama.
Aysha ta dire tray ɗin hanunta a gabansa,
fuskarta da murmushi ta gaida Fadwa da taƙi
kallonta saboda kar Aysha ta fahimci tayi
kuka. Kanta kawai ta jinjina mata. Ayshan
bata damu ba, dan tasan halin Fadwa wani
lokacin itama akwai yarfi. Hankalinta ta
maida akan Share!, “Yaya a zuba?”. Kai ya
girgiza mata alamar a’a, sai kawai tai musu
sallama ta fice a ranta tana ayyana akwai
matsala gaskiya, sai dai rashin ganin Anaam
yasa taji wani iri.
Kusa da shi ta taso ta dawo, “Soulmate……Hannu ya ɗaga mata a fusace. “Fadwa! leave
me alone. Tashi ki fita”.
Idanu ta tsura masa zuciyarta na mata
raɗaɗi, tasan a cikin fushi yake, kuma shi baya
son yanke ma mutum hukunci cikin fushi. Jiki
a saɓule ta tashi ta fice wasu hawaye masu
zafi da jin matuƙar tsanar Anaam na ƙaruwa a
ranta. Dan a ganin duk an mata hakane
saboda Anaam, ta kuma tabbatar ba haka
iyayen Anaam suka bar Share! ɗin ba kamar
yanda Mama ta sanar mata yanzun.
Ya jima zaune a wajen zuciyarsa na masa
raɗaɗi da ƙuna, baya son ɓacin rai da
damuwa, yama rasa ina zai kama da halin
matan nasa. Ya samu ita Anaam ɗin ta sakko
ya fara samun kwanciyar hankali ita kuma
Fadwar na neman rikita masa lissafi. dole ne
ya musu sabon shiri na zama da kowacce da
halinta. Yasan duk abinda Anaam zatai tana
yinsane a karan kanta sannan bata da ɓoye-
ɓoye. Fadwa kam ya fahimci akwai zugar
mutane baibaye da ita, dan tun zuwan Anaam
gidan ya fahimci ta ajiye wasu halayenta na
zahiri ta aro waɗansu daban, idan bai tashi
tsaye a kanta ba zasu iya laɓewa a bayanta su
tarwatsa masa farin cikin gidansa, shi kuma
harga ALLAH yana sonta itama. Ya furzar da
numfashi mai ɗaci, tunawa da Anaam dakecikin bedroom ya sashi miƙewa ya nufi
bedroom ɗin. Da mamaki yake kallonta
kwance a gado har tayi barci, ya tsugunna
saitin fuskarta yana sakin murmushi da kai
hannu ya shafa kanta. “Dama fitsarin ƙarya ne
kenan?”.
Idanu ta buɗe a hankali dan dama barcin
baiyi nisa ba, sai kuma ta maida zata lumshe
da ture masa hannu. Hannun nata ya riƙo
cikin nashi, fuskarsa gab da tata, “Tunda kin
tashi muje kisha fruit ɗin”.
“Ni na ƙoshi barci nakeji Yaya”.
“Ni kuma ban yarda ba idan kika sha sai kiyi
barcin”.
“Uhhum-uhhum”. Ta faɗa tana noƙe
kafaɗarta. Miƙewa yay yana murmushi, ya
ɗagata gaba ɗayanta. Watsal-watsal ta farayi
da ƙafafunta. “Wayyo Yaya! Wayyo Yaya ni ka
saukeni na ƙoshi”.
“Wayyo Aunty! Wayyo aunty ni bazan
saukeki ba sai kinsha”. Ya faɗa dai-dai suna
kaiwa falon………
✍
End of book
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO
Chapter: 67
………Da ƙyar ya iya lallaɓata tasha fruit salad ɗin, dan da gaske barcine a idonta sosai. Ganin tanata faman lumshe idanu dole ya barta. Itama sai ta miƙe tana ɗaga masa hannu. “Yaya good night”.
Kafin ya samu damar cemata komai tabar falon da hanzarinta dan bata buƙatar yace zai dakatar da ita. Shima baiyi yunƙurin dakatar da itan ba. ya dai bita da kallo.
Kamar yanda ya saba bayan gama duk wata al’adar rayuwarsa yay shirin barci. Yaso yin kwanciyarsa anan amma zuciyarsa taƙi aminta da hakan. Ya fito a nutse yana kulle ƙofar. Sashen Fadwa ya fara nufa dan bazaiƙi sauke nauyin da ALLAH ya ɗaura masa ba komi sukai masa na laifi. Yayi mamakin samunta a falo bata kwanta ba. Sai dai hankalinta gaba ɗaya yana akan waya ne. Ta mugun shagala a yin editing video da zatai posting, wanda ɗauka ce mara daɗi, dan kuwa faɗa suke da wata mai suna Teema. Faɗan kuma ya samo asaline akan ita Teema ɗin ta ɗaura hoton Shareff a shafinta tana bin waƙar soyayya. Sai wasu a cikin followers ɗinta suka ɗakko videon suka dinga tagging Fadwa da gaba ɗaya a yau bata buɗe data ba sai da yammar nan, dan tashin hankalin Anaam ya saka a kwana biyun nan ta rage yin posting akai akai kamar da da arana takan ɗora videos sama da uku. Sima itace ta fara kiran Fadwa ta sanar mata lokacin fitowarta a sashen Shareff kenan. To shine fa tun ɗazu ɗin ake tafka rigima tsakanin Fadwa da mabiya bayanta su Sima. Itama Teema da nata magoya bayan sunama Fadwa izgilin Teema zata shigo itama ata uku kafin shekara ta ƙare. (????gsky naso ace kuje tiktok kuga rigimar nan guys????????).
Tsaiwarta a kusa da ita ta sakata wani mugun zabura, daka ganta kasan ta firgita. Ta kife wayar akan kujera a daburce take masa sannu. Idanu ya tsira mata cike da mamaki matuƙa, dan baiga abin zabura ɗin ba anan. Ya maida dubansa ga wayar da take faman ja tana turawa ƙasan throw pillow, zuciyarsa ta ɗarsu a karo na biyu game da ganinta da ɗaukar hankalinta da waya keyi, sai dai na yau yafi ƙarfi dan ƙarara alamun rashin gaskiya sun bayyana akan fuskarta. Komai baice mata ba ya juya ya fice.