BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Habib ne da Hjy babba tsaye a kofar gida suna tattaunawa, Hjy babba ya hango bariki tana fitowa daka mota da sauri ya nufeta tare da fad’in ah ikon Allah, yana ganki a golf Ina jeep din? Tace hjyta dan Allah ki barni a gajiye nake, Hjy babba tabe baki yayi tare da fad’in ai dole ki gaji tunda kin tafi daka ke sai shi cin safe daban na rana daban na maraici ma daban, habib shima karasowa yayi yana fad’in ah oyoyo oyoyo tauraruwan gidan ta dawo, yana maganan ne yana bangare kirji, bariki shuru tayi bata ce musu komai ba, habib yace yau naga sabon iskanci ke bariki ana magana kinyi shuru, sai kace wani ne ya danneki, Hjy babba tace gane min hanya y’ar uwa, bariki tace Hmmm in kuna son jin matsalan muje amma ba’a nan ba, binta suka farayi suna rangwada har d’akinta zama tayi katifarta su kuma suka zauna akan carpet, Hjy babba yace wai bariki da wani sabon iskanci kika dawo ana magana kina wani tamke fuska kaman ba’kin hadari, filo ta jefa ma Hjy babba tare da fad’in ai duk kai kaja min ka had’ani da dan iskan mutum, Hjy babba ya fara salati tare da fad’in na shiga uku an fasa aurena, wa kike nufi? Tace Mai ayabar yara mana, habib yace oh ni habiba karku lalatani, bariki ta wurga Mai harara, Hjy babba tace maiya miki haka? Tace ni ya Mara Wlh saina nuna mishi ni y’ar iskance ta gaske, Hjy babba yace Mari? Oh ni Wai Mai yasa mazan nan basu da tausayi ne su kama mata suyi ta duka, habib yace ai maza basu da mutunci Sun Mai damu kaman bayinsu, in sun tashi biyan bukatarsu sai Kaga y’an banzan sun zo, Hjy babba yace Aini sai yasa Wlh nida maza sai nesa nesa tunda basa tausaya mana kuma sun San mu Mata rauni garemu, wayar bariki ne yayi kara dan dama bata canza sim ba, bud’e jakarta tayi taga alh madu, kin d’auka tayi tare da sakin tsaki, har wayan ya tsinke ya kara kira, ganin zai dameta yasa ta saka wayan a silent, Hjy babba tace uhm Kaga Abu Kala Kala tabe baki yayi tare da fad’in ki d’auki wayan mana, tace bazan d’auka ba dan Wlh sai n….. Shigowan Haulat yasa bata karasa abunda tayi niya ba, Haulat rungume bariki tayi tana fad’in bariki Ina kika jene? Bariki tace nayi tafiya ne, bariki ta kalli Haulat tace gobe sati koh akwai rawan gwatso Haulat ta tashi ta Fara kad’a duwawu, habib yace dad’in Abun Muma muna dashi, Haulat ta saki dariya tare da tura duwawunta dai dai wajan fuskan habib ta girgiza sannan tace amma ba irin wannan ba jin karan ihu kaman ana fad’a yasa suka fita su duka da gudu, dan suga maike faruwa, wata karuwa ce ita da saurayinta suke fad’a sai jibganta yake yana fadin dan ubanki Mai kika nema kika rasa? Yar iska kawai harta d’akin da kike zama ni nake biya abincin da kike ci ni nake baki amma sai kije kina kula wasu maza zabga Mata Mari ya kuma yi yana fad’in karuwar banza karuwar hofi ni nafi karfin wulakanci, bariki ce ta nufeshi tare da ture shi ta d’aga yarinyar wacce ya mata jina jina amma duk da haka bakinta bai mutu ba sai fad’i take aurena kayi dan iska aiba sadaki na ka biya ba, balle ka hanani hulda da wasu mazan shege karamin dan iska sai naci Uwar babanka, zabura yayi zai kuma cafko ta bariki ta tareshi tare da fad’in haba mlm ai wannan ba girmanka bane kaita dukan mace, Hjy babba tazo tana fad’in na shiga uku an fasa aurena Wai y’an mazan nan Mai yasa kuke mana hakane ku kamamu kuyi ta jibga kalli yanda ka fasa mata baki ni Wlh Ina takaicin halin maza, jamil da habib suma suka karaso suna fad’in oh sai kace ana ya’kin duniya, habib yace gaskiya Malam baka kyauta ba ka kama y’ar uwarmu mace kaita jibga sai kace ka sami gardin namiji irinka gaskiya mazan nan bakwa mana adalci, jamil ya tabe baki tare da fad’in ai wannan wulakanci ne wlh maza kuna cin zarafin mu haba dan Allah mutumin ganin Sun mishi ca yasa ya fita tare da kallon yarinyar yace zan kamaki yar iska mayaudariya, tace kaine dan iska shege dan zina, Hjy babba tace la na bani daman dan zina ne oh Kaga Abu in baka mutu ba, shewa suka saki tare da fad’in sawa suka had’a duwawu suka buga, bariki ta kalli yarinyar tace haba khairat mai yasa zaki biye mishi harki Bari ya duke ki? Khairat tace haba bariki Dan kawai yaga wani yana cina sai ya fara duka na sai kace mijina Aiba aurena yayi ba ina da ikon duk Wanda naga daman ya cini in yarda, bariki tace hakane khairat amma da baki biye mishi ba jiba yanda ya ji miki ciwo, khairat tace ai Wlh shi zai biya kud’in magani, habib yace oh kunji bariki ya jibgeki sannan kice ya biya kud’in magani? Wucewa khairat tayi tana fad’in ai dole ya biya dan uwarshi, Haulat data gama waya tazo tace kuban labari maiya had’asu? Hjy babba yace sai kije gidan radio a baki labari, Haulat tace Kai dai ka sani, yace dakata Waye Kai? Haulat tace wanda ya tsargu, Hjy babba yace caf durun uwa Wlh zan miki rashin mutunci, Haulat tace kaima kanka dai Hjy babba yace Wlh Haulat kinfi kowa sanin halina nafi y’ar iska iya iskanci ganin Hjy babba tayi zafi yasa Haulat tace haba kawata wasa fa nake miki Hjy babba tace banso gskya banso taya zaki dinga kaini jinsin daba nawa ba, Haulat tace bazan kara ba Hjy babba gaba yayi yana fad’in iskancin banza Mai za’a nuna min, Haulat jan hannun bariki tayi sukai gaba tace muje inada magana dake.

Washe gari Yarima Aliyu ne cikin shiri mota ya shiga dan dawowa garin kaduna, fita sukai daka cikin masarautar suna fita saiga Gimbiya zinatu ta kirashi d’auka yayi yace hello, tace Yarima Ina hangoku kuka fita dan Allah ka tsaya muyi sallama, yace kiyi hakuri in muka karasa za muyi waya, inna fito bana komawa, babu yanda ta iya dole hakura tayi, Yarima Aliyu sun Kai garin kaduna wajan karfe 11 da wani abu na safe, direct maraban jos suka nufa inda suka shiga cikin anguwar basu karasa gidan ba Yarima yaga habib yana tafiya yana rangwada, yarima yace ma driver dinshi tsaya da motar, bayan driver din Yarima ya tsaya yasa sauran motocin suka tsaya tunda suka shigo anguwar idon mutane ke kansu, yarima ya nuna ma driver dinshi habib yace ka kira min shi, driver din ya fita tare da fad’in angama ranka ya dad’e…… Muje zuwa

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

                 *PAGE 10*

Driver din direct wajan habib ya nufa yace bawan Allah Yarima na son ganinka.

Habib waige ya farayi yaga dawa mutumin yake magana dan yaji yace Kai ba ke ba, habib yace dawa kake?

Mutumin yace dakai mana, yarima ke magana,

Habib yace dakata Aiba namiji ka gani a gabanka ba, mace ce a gabanka kalleni dakyau ko Kaga na maka kama da namiji?

Driver din Yarima yace ikon Allah, kai yanzu kana gansamemen kato ka dinga kiran kanka da mace?

Habib yace dalla Mlm dakata Wlh sai in rufe idona in sharta maka rashin mutunci.

Ganin haka driver din yace a’ah Allah ya baki hakuri Hjy, yarima na son ganinki,

Shuru habib yayi yace wani yarima?

Nuna Mai motar driver din yayi tare da fad’in yana cikin mota.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button