BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Wajan karfe 9 Yarima ya shigo d’akin amarya ba tare da Aboki ko d’aya ba, dan yace kallon da suka mata wajan dinner ya isa haka, bariki na zaune akan gado Yarima ya shigo tunda ya shigo gabanta ke faman fad’i, inda take ya nufa tare da cire mata gyalen dake kanta yace Alhmdlh tsarki ya tabbata da Allah daya nuna min wannan ranan, janyota yayi jikinshi yayi mata wani irin runguma, har tana jiyo ajiyan zuciyarshi, lokaci d’aya ya saketa tare da d’agota ya sauketa k’asa yace my princess muje muyi alwala muyi ma Allah godiya….. Gabanta taji yana fad’i yaka mata Yarima yasan gaskiya Kafin wani abu ya shiga tsakaninsu, wayarshi dake ajiyu yayi kara d’auka yayi yaga number kaman Karya d’aga, sai kuma ya d’auka, ban son mai aka fad’a mishi ba naga ya kashe da sauri tare da fara danna wayar duk wannan abunda ake suna tsaye shida bariki suna kallon juna amma shi idonshi nakan wayar…. Lokaci d’aya hawaye ya fara zuba a idonshi tare da fad’in today is our wedding night, the day dat I have waiting for since d day dat I have meet u, but you destroy my life, you have cheated me….. Cikin tashin hankali tace Yarima maiya far…. Yace keep quiet tare da ri’ke kirjinshi alaman yana mishi ciwo yana kokarin yin magana ya fara tari Sosai lokaci d’aya yayi k’asa……

TOH MASU MIN KORAFI IN K’ARA YAWAN RUBUTU YAU DAI NA K’ARA, AMMA KUDA KUGA WANI POSTING DIN SAI NAN DA KWANA UKU, BUT IN NAGA COMMENTS DINKU YAU YAYI YAWA MAY BE GOBE IN MUKU

not edited

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

WANNAN PAGE DIN NAKU NE
JANAF, SA’ADATU ALKALI TSAFE, MAIMUNA MATAR ABDULLAHI, MRS ADAM Y’AR MUTAN KAGARA, PRETTY MARDY, HAFNAN, XINNE SMART, AMENAT KABIR KIRU, ummyONtop, DEEJAT THANI, FARIDA BASHIR UMMU SAFWAN, HAUWA S ZARIA, BINTA UMAR ABBALE, AYSHA ALTO, FAUZY MB, UMMU AFFAN, SIS FAUZY Y’AR AMANAN KAINUWA WRITERS, WANNAN PAGE DIN DUKA NAKU NE

BOOK 2

                 *PAGE 17*

Tari yake Sosai, bariki kuka ta Fara Tana fad’in Yarima Mai yake damunka?? Tare da tabashi tana son d’ago Shi ,hannunshi da yasa a baki yana tari ya cire ya fara kokarin tureta alaman tabar tabashi, amma jikinshi babu kwari ya kasa tureta din…… Wani irin tari yayi tare da yunkurin yin amai saiga jini nan….. Wani irin ihu ta saki mai ban tsoro tare da kiran nashiga uku Yarima maiya sameka??

Ganin jinin a bakinshi yana fita yasa ta fita da gudu, tana fita taga fadawa tace dan Allah kuzo Yarima zai mutu, tana maganan tana kuka da ihu, kuzo mu kaishi asibiti….. Da sauri suka shiga wasu kuma suka je fad’ama iyayenshi, koda fadawa suka shiga ganin Yarima sukayi a kwance yana wani irin nishi ga jini na zubar mai a baki, da sauri suka D’aukeshi suka fita dashi, suna cikin sashi a mota mum dinshi tazo, ganin halin da d’an nata yake ciki yasa ta Fara fad’in Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, Yarima maiya sameka, lokaci d’aya kuma tasa kuka, shiga motar tayi da sauri suka nufi asibiti…… Bariki Kafin ta karaso har Sun wuce dan haka ta Fara cewa sauran fadawan muje ku kaini dan Allah inda suka je….. Ganin kanta ko dankwali babu yasa wasu kuyangi dake tsaye wajan suka karaso suna fad’in Allah ya taimaki gimbiya, ki koma ki saka mayafi sai a kaiki,.

Sai a sannan bariki tasan a halinda take da gudu tayi ciki, inda ta d’auko mayafinta tana kokarin fita wayar Yarima dake d’akin ya fara K’ara dole yasa ta koma ta d’auki wayar babu suna number ne ke kiranshi harya tsinke bata d’auka ba….. Fita tazo yi lokaci d’aya kuma ta tsaya cak domin tunawa da abunda ya faru da Yarima, wanda tunda aka kirashi ta rasa gane kanshi,har wannan abun ya sameshi, danna wayan tayi da nufin ta shiga taga Mai aka turo mishi, gani tayi akwai password, shuru tayi tana nazari Mai Yarima ya gani?? Kodai wani ya fad’a mishi koni wacece?? Gabanta taji ya fara fad’i tunawa da kalaman daya Fara Mata Kafin ya fad’i…… Wani irin kuka ta saki mai ban tausayi, tare da fad’in shikenan2 sunyi nasara Sun fad’ama Yarima koni wacece kuka take Sosai, lokaci d’aya kuma ta fita da gudu inda taga mota na jiranta shiga tayi domin aka kaita asibiti da yake fadawa sun San asibitin da suke zuwa nan aka nufa da ita dan suna da tabbacin can aka Kai Yarima, tana mota tana kuka……

Kafin kace Mai har labari ya bazu cikin masarauta, Yarima Aliyu bashi da lafiya rai a hannun Allah, har wasu na cewa jini ke fita a bakinshi hala amaryanshi ba budurwa bace, wasu kuma suce kodai wani abu tayi mishi?? Haka dai ake ta jita jita, koda kuyangin gimbiya zinatu suka fad’a mata cikin tashin hankali itama tayi asibitin…..

Yarima Aliyu ko Kafin akai asibiti, ya daina koda motsi, ana zuwa akai emergency dashi, likitoci sukai kanshi aka fara dubashi, tare da bashi taimakon gaggawa….

mum ta kasa zama sai kuka takeyi ga fadawa a wajan da yawa, kowa ya shiga cikin damuwa.

basu dad’e ba saiga bariki ta karaso Tana kuka, tare da fad’in mum Ina Yarima?? Ina Yarima?? Mum din ri’keta tayi tare da rungumeta, ta kasa ko magana sai shafa ma bariki baya takeyi alaman tayi shuru……

Suna cikin haka saiga Zinatu tazo cikin Tashin hankali ganin Bariki wajan mum ko ba’a fad’a mata ba tasan itace amaryan da Yarima ya auro, da sauri ta nufi bariki ta fincikota tare da watsa mata Mari Tana fad’in mai kika ma Yarima?? Mai kika mishi?? Kuka ta saki Zinatu tare daci gaba da fad’in Wlh Idan wani abu ya sameshi saina kasheki W…….

Mum sai yanzu ta iya magana, tace Zinatu kina da hankali kuwa?? A gabana kike wannan abun?? Shi Yarima dinne yace miki ita ta mishi wani abu??

Cikin kuka tace mum, daka ita sai shi, Nasan wani abu tayi mishi……

Mum tace ya isa haka, plz ki barni inji da abunda yake damuna ban son rigima….

Bariki kam tunda zinatu ta mareta take ri’ke da wajan Tana kuka, ko bata tambaya ba tasan itace Uwar gidan Yarima Aliyu…… Bariki tasan lallai ko ba’a fad’a ba dole kowa yayi zarginta, abunda Zinatu ta fad’a gaskiya ne….. Kuka tayi k’asa tanayi tare da fargaban Kar wani abu ya sami Yarima dan bazata iya jura ba…..

Kowa na cikin Tashin hankali, ga doctors har yanzu basu fito ba…… Suna nan zaune saiga Mai martaba shida Hafsat Sun zo cikin Tashin hankali.

Mum ganin Mai martaba yasa ta tashi ta nufeshi tana kuka, tare da fad’in ina jin tsoro Kar Yarima ya mutu Aman jini yakeyi Ina tsor…..

Toshe mata baki Mai martaba yayi, tare da fad’in ki daina fad’in haka, Hafsat itama kuka ta Fara cikin Tashin hankali…..

Duka kowa shuru yayi babu Mai rarrashin wani, suna nan tsaye d’aya daka cikin doctors din ya fito, suna ganinshi suka nufeshi tare da fad’in Dr ya ake ciki, ganin Mai martaba yasa yace ranka ya dad’e wacece Zainab a cikin nan??

Da sauri mum tace ga tanan tare da nuna bariki, yace ok tare da kallon Bariki yace taso muje……

Da sauri ta tashi tabi Dr, kowa da abunda yake sakawa, Zinatu ta Fara fad’in mum kin gani ko kin gani wlh itace tayi mishi wani abu…..

Kowa shuru yayi ya kasa cewa koda uffam…. Suna jira suga ikon Allah……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button