BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Kallonshi tayi cikin tsoro tare da fad’in Yarima plz ka barshi Kawu nane yake kira, so yake Inba ma Abba, wayan Abba ne ya sami matsala in an kira yana ji amma ba’a jinshi, inna d’auka nace bana gida zai iya zuwa har gidan ya sami Abba da Umma yayi musu fad’a akan Mai yasa zasu dinga bari Ina fita da yamma, kuma yanzu inna shiga Gida Umma bazata Bari in fita ba, dan yanzu tana tunanin ina d’akin makwabciyan mune…..

Yarima Aliyu ajiyan zuciya ya sauke, lallai Zainab gidansu gidan tarbiya ne, sabanin yanzu da iyaye suke sakin y’ay’ansu suna abunda suka ga dama, har ma wasu zaku ga kaman su suke juya nasu iyayen sai abunda sukace iyayen nasu keyi….. Amma a fili sai yace Mata my princess na fad’a miki tun Farko ai ki bani dama inga Abba kinki, yanzu Idan yazo ya gammu ya kike so inyi???

Cikin sanyin murya tace bazanji dad’i ba, domin na tabbata Abba zaiyi fushi Sosai, amma Yarima tunda harna yarda yau kazo gidanmu hakan ya kamata ya nuna cewa Ina son Kaga Abba din…..

Wani irin murmushi Yarima ya saki cikin jin dad’i tare da furta Kalman Alhamdullilah cikin ranshi, domin wannan maganan da Zainab tayi mishi yasa shi cikin farin ciki Sosai….. Kallonta yayi cikin ido tare da fad’in my princess kin tabbata kina son inga Abba.???

Ganin bazata iya juran kallon cikin idonshi ba yasa ta kawar dakai gefe tare da fad’in eh Ina so ka ganshi, domin hakan ya kamata Ayi tun Farko

Murmushi yayi tare da fad’in zan iya ganinshi yau?

Tace eh amma sai dai ka tura wani yaje ya maka sallama dashi duk da ban tunanin ya dawo amma kuma hala ya dawo din dan lokacin dawowarsa yayi …..

Dariya Yarima yayi tare da fad’in am joking bazan iya zuwa ni d’aya ba, but zuwa jibi Zanzo da Usman da wasu friends dina sai mu ganshi mu nemi izinin zuwa zance Kafin manya su shiga

Murmushi tayi tare da fad’in Allah ya taimaka

Ya amsa da Ameen, tare da fad’in where is my promise?

Kallonshi tayi taga shima ita yake kallo da sauri ta kawar da kanta gefe tare da sakin murmushi sannan tace wani promise??

Yace abunda ya faru wajan Walima.

Dariya tayi wanda ya kara mata kyau sannan tace Yarima ban samu daman d’aukan komai ba saboda jama’a Wlh kunya duk ta hanani gashi mune masu saukan….. Amma munyi hoto a gida da kawaye na Wanda mukai saukan tare

Yace OK Nasan duk kinfi yin kyau

Tace a’a tare da danna wayarta tace na tura maka ta whatsapp

Murmushi yayi ya d’auko wayanshi ya fara dannawa, yace my princess duka sun sa nikaf Kema Aida kinsa ko so kike ayi ta kallemin ke

Dariya tayi tace a cikin gida nefa babu Mai kallo na sai Kai ta karasa maganan tare da rufe fuska

Murmushi yayi tare da fad’in my princess yunwa nake ji banci komai ba tunda safe…..

Da sauri ta kalleshi tare da fad’in mai zakaci in kawo ma? Yarima taya zaka zauna har yanzu bakaci komai ba ulcer zai kamaka plz mai zaka ci??

Murmushi yayi cikin jin dad’i domin ganin yanda ta nuna kulawanta akanshi, ya tabbatar mishi da cewa tana sonshi Sosai……

Katse mishi tunani tayi da fad’in Yarima ko in kawo maka tea kasha Kafin in dafa maka wani abu??

Yace a’ah ki barshi zanje Inci abinci yanzu

Shuru tayi tana d’an nazari can tace ko in kira habib yaje ya kawo ma wani abu kaci?

Hannunta ya koma tare da ri’ke mata su duka biyun yace my princess karki damu zanje wani waje Inci, ko zaki raka ni?

Da sauri tace eh muje Kafin Abba yasa Umma ta kirani a d’akin da take tunanin ina ciki inya dawo Kar yasa a kirani yaga bana nan koda yake Nasan ma ya dawo ganin habib Nasan bazai damu daya ganni ba.

Murmushi yayi yace Nop Bari inje alone banso Ayi miki fad’a my princess

Tace Yarima plz muje kaci abinci habib na nan bari in kirashi sai muje tare zance ma Abba zani maraban jos In kwana bazai hana ba sai muje kaci

Yarima yace ok my princess

Fita tayi ta shiga cikin gidan Jim kad’an sai gata ita da habib da abbanta na Bariki Sun fito daka gani ya fito raka habib dinne a yanda Yarima ya fahimta kenan???? har bakin titi ya rakasu sannan ya dawo ya shiga gidan yarima yana kallonshi cikin ranshi yace wannan daka gani Dattijo ne yana yin kamalan shi ya nuna ma Yarima hakan???????????? kai ana abu a duniya sai yasa akace sometimes abunda ka gani bashi bane gaskiya……

Yarima tada motar yayi shima ya nufa titi bai gansu ba kiran Zainab dinne yasa ya dauki waya tare da fad’in my princess where are you?

Tace muna gaba wajan NDA Abba saida muka shiga mota ya koma shine muka sauka a nda

Yarima yace ok ga ninan zuwa, Yarima juyawa yayi ya nufi nda din ya d’aukesu ta shiga gaba habib kuma baya, Yarima ya kalleta yace Ina zaki kaini Inci abinci??

Ido ta d’an zaro tare da fad’in ni Ina na sani tunda ba zuwa nake ba

Habib dake Bayan motar yana jinsu cikin ranshi yace bariki ko y’ar iska ke inane baki Sani ba cikin garin kaduna yanda kuka san map din garin ne a kanta amma yanzu tana wani nuna ita ta Allah ce….. ????

Yarima wani babban restaurant ya faka motarshi wajan yayi mugun had’uwa gashi babu irin tarkacen mutane a wajan, daka ganin alama wajan ba kowa ke zuwa ba sai y’an gayu na gaske, private waje suka zauna, shidai habib cewa yayi cikin mutane zai zauna danya dinga ganin masu shiga da fita

Bariki tace muje tare mana

Yace ke barni in zauna nan ko zanyi kasuwa

Bariki dai dariya tayi sannan ta nufi ciki inda Yarima yake domin yace baya son su zauna inda akwai mutum ko d’aya dan baya son ana kallon mishi ita…….

Yarima ya fad’a abunda za’a bashi bariki kam tace ta koshi Yarima yace dole taci wani abu, babu yanda ta iya tasa a kawo mata snack dan a koshe take shima takeaway tace tana so, yarima yace abar snack din in Sun tashi fita zata zaba abunda take so.

Wajan 15 mnt aka kawo ma Yarima abinci lokacin ana ta kiran sallah magrib tashi yayi ya Kalli bariki tare da fad’in bari inyi sallah.

Tace OK tare da kallon Wanda ya kawo abincin tace maida kayan inya dawo sai kayi warming din abincin ka kawo.

Mutumin yace ok ma, Yarima bai tafi ba saida yaga mutumin ya fita dan ya Lura dashi yanda yake kallon zainab kaman yana son yi mata magana…..

Yarima Aliyu na fita kam saiga mutumin ya dawo da sauri yana fad’in ma plz I need to talk to you.

Bariki tace lafiya maiya faru?

Yace ma ance in amso phone number d’inki ne

Tace what? Are you mad da aurena inzo da mijina kazo kace min in baka phone number dina get lost frm hare Kafin mijina ya dawo ya ganka

Mutumin yace sorry ma Nima na fad’a mishi kina da aure saboda irin shigarki amma yace babu damuwa koda kina da aure in amso mishi number d’inki

Bariki tace Waye zan iya ganinshi??

Yace let me go and ask him in yace in kawo ki sai kizo

Bariki tace ok yana tafiya saiga Yarima ya dawo Allah yasa bai ganshi ba

Bariki tashi tayi tare da fad’in har an idar kiran mutumin tayi da baiyi nisa ba yazo tace Kawo Mai abincin

Yace OK ma

Bai dad’e ba saiga abincin ya kawo, Yarima coffee ya fara sha sannan ya kalli bariki yace my princess feed me plz

Dariya tayi tare da fad’in feed ur self u r not a baby

Yarima kallonta yayi tare da fad’in oh really? Ni baby dinki ne

Ido ta rufe alaman jin kunya

Hannunshi yasa yana kokarin cire mata hannunta da tasa ta rufe fuskanta ….. Muryan Wanda ya kawo abincin ne yazo yana fad’in ma he said that you can come he is waiting for you……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button