BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Koda Bariki suka shiga oxygen din da akasa ma Yarima yana k’asa alaman yana son d’aukewa, kuma yana saka zero shikenan mutum ya mutu, da sauri Dr yace plz ki mishi magana sunanki yake ta kira pls say something karku rasa shi…….

Da sauri ta ri’ke Mai hannu tana kuka tare da fad’in Yarima karka bari wani abu ya sameka….. You know that I can’t live without you, plz Yarima ka tashi kasan ina Sonka kaine rayuwa na, wlh bazan iya juran inga wani abu ya faru dakai ba……

Lokaci d’aya oxygen din ya fara k’aruwa alaman numfashin shi yana son dai daituwa…. Likitocin ganin haka yasa suka fara kallon juna alaman jin dad’i an fara nasara….. Bariki kuka take Sosai tana fad’in karya mutu ya barta….

Idonshi dake rufe ya fara zubar da hawaye…… Lokaci d’aya numfashin shi ya dai daita……

D’aya daka cikin doctors din yace ma Bariki yauwa komai yayi dai dai mu jira muga kuma yanda Abun zai kasance amma muna bukatar ki zauna har muga farkawanshi, muna nufin Kar kibar asibitin nan har sai munga ya farka ….

Cikin kuka tace babu inda zani Ina nan tare dashi

Dr din fita sukayi, inda suna fita Mai martaba yace ya akayi?? Mai yake faruwa dashi??

D’aya daka cikin Dr din yace ya samu bugawan zuciya ne, ina tunanin yaga abunda ya bashi tsoro ko mamaki, kuma daka duka alamu abunda ya gani ko yaji yana d’aya daka cikin abu masu muhimmanci a rayuwanshi, hakan yana faruwa wasu ma rasa ransu suke, a gskya masu rasa ransu ma sunfi yawa amma shi yayi Sa’a ko ince mun samu mun ceco rayuwanshi tare da taimakon Allah da kuma wannan baiwar Allah dake ciki, magananta da yaji shine yasa zuciyarshi ta Fara harbawa, inda badan ita ba toh gaskiya dasai dai kuji mummunan labari , dan haka dole ta zauna dashi muga yanda Allah zaiyi…..

Mai martaba godiya yayi ma Dr din tare da fad’in zamu iya ganinshi?? Sannan kana ganin zai tashi babu wani matsala??

Dr yace zaku iya ganinshi amma plz Kar kuyi magana, sannan zai tashi insha Allah Indai yarinyar na kusa dashi kuma yana jin magananta a kusa dashi…..

Mai martaba yayi ma Dr godiya, sannan suka shiga d’akin, ganin Bariki sukayi a zaune kusa dashi hannunta na ri’ke da nashi tana kuka…..

Kowa tsayawa yayi yana mamakin irin wannan Abun musamman mum damai martaba, ita dama zinatu bata shigo ba domin maganan Dr yasa taji wani iri tare da takaici….. Mum ce ta k’arasa kusa da inda Yarima din yake tare da kamo d’ayan hannunshi, fuskanshi tayi fayau ga hawaye a idonshi na zuba….. Mum itama hawayen ne yake zuba daka idonta, kowa dake wajan ya tausaya mishi…… Mai martaba ganin mum nason kuka mai sauti yasa ya kamota sukai waje, Hafsat da Bariki suka zauna a d’akin

Zinatu ce ta shigo d’akin ganin zinatu yasa bariki tashi tabar d’akin domin irin kallon da taga zinatu din nayi mata, kuma ko babu komai ya kamata ta dan bata waje ta gana da mijinta duk da bai farka ba…..

Fita Bariki tayi tana fita, Mai martaba yace Zainab ya kika fito?? Ko wani abu kike bukata??

Tace a’a Abba cikin jin kunya, na d’an basu waje ne…..

Mai martaba ya gane ta fito ne saboda Zinatu…….

Mum tace Zainab bai kamata ki fito ba ai, maza ki koma Kinji…..

Tace toh mum jiki a sanyaye Bariki ta shiga, abubuwa sun mata yawa, na farko Tana zullumin Mai aka fad’ama Yarima a waya, sannan maiya gani, duk wannan Abun suke ta faman Mata yawo a Kai….. Koda Bariki ta shiga zintau fita tayi

Bariki zama tayi kusa da Yarima tare da kurama fuskanshi ido, har yanzu yana hawaye, gaba d’aya zuciyarta ta tsinke, shidai har yanzu bai farka ba, toh wannan hawayen fah????….. Kiran Hafsat akayi a waya ta tashi tabar d’akin Tana fita kaman ance Yarima ya bud’e ido , a hankali ya bud’e idonshi ya sauka akan na Zainab wacce itama shi take kallo tana murna tare dason yin magana murna ya hanata……

Murmushi ya sakar mata, tare da kamo hannunta ya ri’ke tare da matse su…..

A hankali tace Yarima Ina Sonka I can’t live without you, tana maganan tana kuka, tace I was scare with your condition I……

Hannunshi yasa ya rufe Mata baki yana kokarin yin magana ya tsaya alaman ya tuna da wani abu……. Lokaci d’aya ya sake mata hannu tare da fad’in leave from hare I hate to see your face……..

Cikin kuka tace Yarima zainab din’ka ce Yarima nice maina……

Ya daka mata tsawa tare da ri’ke kirjinshi yace I said leave from here ……. Su mum dake waje Suka shigo harda su zinatu, ganin Bariki na kuka Yarima shima hawaye ne ke zuba a idonshi gashi ya ri’ke kirjinshi…… Kallon iyayenshi yayi tare da fad’in mum tell her to leave from here……. Kowa kallonshi yake cikin mamaki da sauri Hafsat ta fita kiran doctor…… Mai martaba yace Aliyu matarka ce kake koranta?? Maita maka??…… Yace Abba plz tell her to leave I don’t want to see her face…. Why am I still alive…. Dai dai lokacin doctor yazo yace kowa yabar d’akin…….. Bariki da sauri ta fita Tana kuka lallai ta tabbatar an fad’ama Yarima ko ita wacece kuka take Sosai tare da barin asibitin ba tare da sanin kowa ba……

Hmmmm Ashe masoya novel’s din bariki suna da yawa?? Ban taba sani ba sai jiya???????????? lallai kuna son posting naga ruwan comments harda Wanda ban San suna karantawa ba, jiya Sun zuba comments, tunda hakane nima daka yanzu zan daina posting kullum Indai bakwa zuba comments kunga 50 50 kenan kuyi rowan comments inyi rowan posting???????????? Ina sonku masoya novel’s dina

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO……

          *HASSAN ATK, MMN TWINS MAI DADDAWA  A BANI NA GOMA????????, NAFISA ISA SHEHU,  HAUWA LADAN KAURA NGD DA K'AUNA, 80K, MARYAM KANO MMN SAHLA, HAFSAT ALHASSAN????, KINA RAINA MY SWT FRIEND HABIBA BUSY MY KAWAR AMANA*

BOOK 2

                 *PAGE 18*

Bariki kuka take Sosai tana tafiya a kafa, tafiya take bata san inda take wurga kafarta ba, ba komai bane a ranta sai yanda Yarima yake nuna tsanan ganinta, ta tabbata abunda take boyewa take burin in sunyi aure ta fad’ama Mai, wanda take burin Sanar Mai an samu wani ya fad’a Mai….. Zama tayi a k’asa gefen titi Tana kuka cikin Tashin hankali, bata taba tunanin abubuwa zasu cabe Mata haka ba, tunda take shirya wannan abun bata taba tunanin Idan ta fad’ama Yarima gaskiya dole iyayenshi Suma su san gaskiya tunda tayi amfani da iyayen bariki, gaba d’aya dana sani takeyi Wanda hausawa ke cewa k’eya ce, da yake dare ne Sosai babu mutane sai motoci dake Faman wucewa, suma motocin jifa jifa suke wucewa ba Sosai ba……

Bayan iyayen Yarima sun fito dasu zinatu, kowa da abunda yake sa’kawa cikin ranshi game da wannan al’amarin…..

Zinatu kam dad’i ya cikata Sosai, tare da aiyana ma ranta lallai Yarima ba virgin ya sami matarshi ba, tunda har Ya nuna baya son ganinta, yake nuna mata tsana k’arara, ji take kaman tai ihu dan murna, tare da fad’in da Gimbiya Amina batai bacci ba dana kirata na bata wannan kyakyawan labarin, amma Allah ya kaimu gobe……

Sunyi wajan 20mnt a wajan, sannan mai martaba yace Ina Zainab??

Nan mum ta kalli Hafsat tace ina tayi??

Hafsat tace nima ban sani ba mum,

Nan mum ta tambayi fadawan dake wajan ko sunga inda tayi??

D’aya daka cikin fadawan yace ta fita, daka ganin alama kuma waje tayi dan yanda ta fita da sauri tana kuka……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button