BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Labarin abunda ya faru mum taba Hafsat.

Hafsat cikin tashin hankali tace Abba da kanshi yasa Yarima yaje kurku?? Bari inje in ganshi mum tana maganan tare da fita

Direct kurkun ta nufa inda taga Yarima a ciki a rufe, kuka ta saki tare da bada umarnin a bud’e ta shiga.

D’aya daka cikin fadawan yace afuwa gimbiya Mai martaba ya bada umarnin Kar a bud’e kofar nan sai yayi sati biyu……

Yarima Aliyu murmushi yayi cikin takaici tare da ganin ba’a mishi adalci ba danya karya dokar daba addini bace, sannan abunda yafi d’aga mishi hankali yanda mahaifin nashi yayi amfani da mummunan kalma wajan cewa inya K’ara Karya al’ada bai yafe mishi ba, hakan bai isa ba saida Ya fad’a Mai ya dakile maganan auranshi da zainab…… Ido Yarima ya lumshe lallai mahaifinshi yana son rasa shi, domin a yanda yake ji, bazai iya rayuwa ba tare da Zainab ba, bazai ma iya ganin wani ya aureta ba inba shiba, inko hakan ta faru baya ganin zai iya jura ko kad’an……

Muryan Hafsat ne ya Katse Mai tunani da take fad’in bros Tana tsaye a waje tana kallonshi tace haka zaka kwana a nan? Tana maganan ne cikin tausayawa tare da kuka

Yace lil kin San ban son kuka koh?

Tace Bros taya bazanyi kuka ba, mai yasa Abba zaisa a rufeka danka saki matarka aiya kamata aji maita maka….. I dnt knw why Abba yake d’aukan al’ada kaman addini yake daraja wannan al’adan ya kamata duk a barshi is not fai……..

Yarima Aliyu sa hannunshi yayi a bakinta tare da toshe mata yace enough lil sis, karki kara fad’in haka Kinji??…. Abba yana da ilimin addini Sosai baki ga duk cikin al’adan da yafi bashi muhimmanci shine na saki ba, karki manta Idan akayi saki sai al’arshan uban giji ya girgiza….. Abunda Abba yayi shine dai dai bai kamata inyi saki ba duk da raina ya baci….. But thank god saki d’aya ne and kuma na maidata but I will teach her a big lesson for insulting my parent….. Zan iya tolerating komai but banda zagin iyaye koci musu mutunci….. Yanzu Ina son kije ki zauna da ita Kafin in fito

Hafsat kallon Yarima tayi tace bros gskiya ban tunanin zan iya zama da ita, matarka she use to show her attitude to anyone ,and ni kuma I won’t tolerate it, in Naje haushinta zanji coz saboda ita kake nan

Yarima Aliyu yace lil wani attitude??

Tace dazu fah mum tace in rakata d’akinta muna shiga ta wuce ta barni, ko magana babu ai wannan haline mara kyau….

Yarima duk da ranshi a jagule yake saida yayi murmushi, kaf sisters dinshi yafi son Hafsat tana sashi nishad’i, yace lil ki daina sawa a ranki haka ne, kina jin haushinta kawai dan tasa an rufe miki bros d’inki…..

Hafsat tace uhm uhm Dan tasan ya ganota… Tace Bros sauro zai dameka bari insa a kawo maka magani

Yarima Aliyu yace Nop leave it ko kin Kawo zasu shigo tunda kofar abude take….

Hafsat shuru tayi tana kallon d’akin da babu haske saina fitila domin ba’a Kai hasken huta ba dan dai kawai a horar damai laifi da duhu….. Gashi babu katifa balle filo, Hafsat ajiyan zuciya ta sauke tare da fad’in ina zuwa…….

Yarima Aliyu yana nan zaune shi d’aya…… Hafsat bata dad’e da tafiya ba saiga wani daka cikin fadawa yazo yana fad’in Allah ya taimaki Yarima Mai martaba ya bada umarnin a amshi wayoyin hannunka domin cikin nan ba’a shiga da waya……

Yarima shuru yayi tare da d’auka wayan yayi dialing number din Zainab ( bariki ) harya tsinke bata d’auka ba, kara kira yayi shuru, dan tsaki yaja kad’an Kafin ya kashe wayan ya mi’ka musu……

Hafsat direct gefen Mai martaba ta nufa, inda tayi sallama…. Amsawa yayi cikin sakin fuska tare da fad’in Hafsat baki bacci ba??

Tace eh Abba

Yace lafiya??

Tace Abba nazo neman alfarma ne

Yace Hafsat alfarman me?

Tace Abba dan Allah Nasan baka taba ce mana a’a ba akan duk abunda muke so, Abba kayi hakuri kasa Yarima ya fito dan Allah Abba, ta karasa maganan cikin kuka….

Mai martaba yace Hafsat tashi kije ki kwanta sannan daka yau karki kara zuwa inda Yarima yake daka yanzu na hana kowa yaje inda yake.

Tace Abba d……

Yace tashi ki tafi

Tashi tayi jiki a sanyaye domin dama tasan dakyar ya yarda dan tasan mahaifin nasu bai iya fushi ba…. Tasan mutum d’aya ce zata ma magana Indai tayi ma Mai martaba magana zai yarda a fito da Yarima itace gimbiya zinatu….. Toh amma bata son zuwa wajanta dan bata son raini, dan haka ta nufi gefen mum dinsu a falo taga mum din na zaune tana karanta al’qur’ani……

Mum din ajiye al’qur’ani din tayi ta kalli Hafsat tare da fad’in baki je kin kwanta ba??

Tace mum taya zan iya bacci Yarima na kulle, mum wajan fah ko katifa babu babu abun rufa ga sauro…. Dan Allah mum kije Kema kiyi ma Abba magana….

Mum tace Hafsat tunda Mai martaba yace a rufeshi ko Nayi magana bazai sa a bud’eshi ba, so Kinga gwara kije ki kwanta zaifi miki….

Hafsat cikin kuka tace haba mum, wajan fah akwai sauro Wlh ciwo zai Kama shi Dan Allah m…..

Mum ta dakatar da ita da fad’in go and slp plz.

Hafsat fita tayi direct ta nufi gefen gimbiya zinatu koda ta shiga haurawa tayi har bedroom dinta taje tana mata nocking…… Ta dad’e tana nocking saiga Gimbiya zinatu ta fito tana fad’in lafiya cikin wannan daren? Maiya faru?

Hafsat tace kin San mai martaba yasa a rufe Yarima kuwa??

Gimbiya zinatu tace ban sani ba, amma Nasan zai iya zama gaskiya tunda ya karya al’ada…..

Hafsat tace kiba Mai martaba hakuri yasa a bud’e shi

Gimbiya zinatu tace hakuri akan a saki Yarima? Dariya tayi tare da fad’in Aiko bazai fito ba, gwara yaji a jikinshi koda na kwana biyu ne Kafin a fito dashi…… Karki manta yau ko wata d’aya Banyi ba amma yayanki yamin saki d’aya…. Ke kina ganin yamin adalci? And akan wani dalili zanje ince ma sarki a sakeshi tunda gani mara kunya ni Uwar son miji ko??

Hafsat kallonta take cikin mamaki, tace amma Banyi zaton haka ba, kina maganan kunya AI baki dashi tunda har kika iya zagin iyayen mijinki…..

Gimbiya tace kin fad’i gskya, gashi na zagi iyayen nashi kuma har yanzu ina matsayin matarshi, sudai iyayen nashi su suka dawo dani….

Hafsat tace banyi mamakin jin haka daka gareki ba, and bazan biye miki ba domin irin tawa tarbiyan daban take, da taki…… Tas takai ma Hafsat Mari tare da fad’in karki manta koni wacece yayanki nake aure nafi karfin raini a Wajanki har abada………

zadai kuga typing error yau sosai domin typing din gaggawa Nayi yau

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 13*

wat a funny…. Wlh readers kuna bani dariya, ana baku novels a free daka writer tace novel d’inta ya koma na kud’i sai ku Fara zaginta…. Hmmm which bata ce dole saika biya ba, in kana da ra’ayi ka biya ka karanta in baka da hali saika bari bawai ka dinga zagin taba, tana da right ta mayar da Littafinta na kud’i tunda basirarta take zama ta rubuta muku, wasu ko comment basa iyawa, amma writer dan tace ta maidashi na kud’i saiku Fara zaginta, miye Abun zagi a ciki??…. Haba ku dinga yima writers adalci mana, in kina ra’ayi biya ki karanta in bakya ra’ayi babu dole????‍♀ writer zata bata lokaci ta muku typing amma comment ya gagara akwai alot of mutane da suke karanta novels din mutum amma basu taba comment ba sai anjika shuru za’a fara biyoka PC ana tambaya which hakan bai dace ba, idan writer tayi muku posting bata bukatar komai sai comments d’inku in taga bata samun comment ba dole ta maida na kud’i ba, in kud’i kuka biya inta tura ko kuyi comment ko Kar kuyi bai damu writer ba tunda kudinku kuke karanta wa, so ku gyara ko kuma writers suyi ta maida muku novels dinsu na kudi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button