BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Mai martaba yace zinatu ana son bawa koda yace ya tuba, yayi tuba na tsakani da Allah yanda bazai K’ara aikata wannan mummunan aikin ba

Allah gafurul rahim ne, Allah mai yafiya ne ga bayinsa, Allah yana son bayinsa masu tuba.

Zinatu ta kalli Yarima tace dan Allah Yarima kamin rai karka ce zaka rabu dani, wlh Ina Sonka, dan Allah ka yafemin Wlh na tuba, Yarima Ina Sonka dan Allah kayi hakuri.

Yarima Aliyu shuru yayi yana nazari, can yace zinatu Allah ya sani bazan iya zama ina kallonki da wannan abun ba, domin duk macen da zatai sha’awar mace y’ar uwarta, Toh kallon hoto take ma mijinta

Da sauri mum tace Aliyu kayi hakuri ka d’auki komai yazo maka a matsayin kaddara, lallai Kaga jarabawa, Allah yasa daka wannan sai jin dad’i,.

Yarima Aliyu wani hawaye ne mai zafi ya fito mishi tare da fad’in ya zanyi mum? Babu yanda zanyi tawa kaddaran kenan sai hakuri, Allah ya bani ikon cinyewa, zan zauna da Mata na zan basu dama na biyu, Indai zan yafe ma d’aya dole In yafe ma d’aya, amma daka ranan da suka k’ara aikata wani aiki irin wanda sukayi, bazan iya d’auka ba, amma d…..

Shuru yayi yana kallon Bariki yace mum dole In k’ara aure,

Da sauri Bariki ta taso ta nufeshi tare da fad’in Wlh ban yarda ba, tama manta suwaye a falon saida taji dariyan su sannan taji kunya tare da barin falon da sauri, ganin harda gudu takeyi yasa Yarima yabi bayanta da sauri Karta illata mishi unborn child dinshi, dan yaga kaman ta manta tana da ciki, kuma ance tana bukatan bed rest, shine take wannan gudun.

Bata tsaya ba sai cikin gefenta, a bedroom ya sameta ta kwanta akan gado tana sauke nishi, d’agota yayi tare da fara fad’a kin manta bake d’aya bace Zainab har kike wannan gudun.

Kuka ta sakar mishi da karfi tare da ihu Tana fad’in na shiga uku…..

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 28*

LAST PAGE????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Ido ya ‘kura mata yana kallonta, ganin yana kallonta ya’ki cewa komai yasa ta k’ara sakin wani ihun tana kuka, zama yayi akan kujeran bedroom din dake d’akin, yana kallonta yana murmushi.

Ganin haka yasa ta Fara fad’in bazaka bani hakuri ba? Bazaka ce inyi shuru ba? Sai kuma ta k’ara sakin kuka, ganin har yanzu bai taso ba yasa taci gaba da kukan tana fad’in Dad d’ina zanbi in tafi tunda an gaji dani…..

Yarima ri’ke kirjinshi yayi tare da d’an sakin k’ara, da sauri ta k’arasa wajanshi cikin tashin hankali, tana fad’in Yarima maiya sameka? Har yanzu yana maka ciwo ne,? Gaba d’aya ta rud’e Sosai, tace bari in kawo maka ruwa, tana k’okarin tashi ya kamo hannunta, tare da janyota jikinshi ya kashe mata ido tare da fad’in how far?..

Dukan wasa takai Mai, a hankali yace ah banda lafiya fah.

D’aure fuska tayi tare da fad’in Yarima Mai yasa kake min haka? Kaga yanda hankalina ya tashi kuwa? Nasha dagaske kana jin zafi plz karka k’aramin irin wannan Wasan plz Yarima.

Murmushi yayi tare da fad’in ina son sanin wani abu ne, and kuma na sani yanzu

A hankali tace mai kake son sani?..

Murmushi yayi tare da fad’in kina tsoran kiganni cikin damuwa ko ciwo, taya zaki iya barina? Ai nasan bazaki iyaba

Murmushi tayi tare da fad’in Yarima koda na minti d’aya bazan iya barinka ba, sai dai Inba mutuwa bace ta rabamu ta k’arasa maganan tare da zubar da hawaye.

Yarima Aliyu goge mata fuska yayi tare da fad’in, koda mutuwa zata zo, nafi son ta Fara d’auka na

Zainab tace Yarima kana tunanin inka tafi niya Zan kasance, nafi son mu mutu tare, rungumeta yayi tare da fad’in I love you

Lokaci d’aya tace Yarima

Yace ina ji my princess

Tace maganan k’arin aurenka Wlh zuciya na zai buga

Dariya yayi tare da fad’in inya buga zan baki magani

Tace Yarima dagaske nake fah

Yace keda Nasan ba wani sona kike ba, gwara in auro y’ar budurwa yar shekara Goma sha d’aya……

Kuka ta saki tare da fad’in dama Nasan abunda ke ranka, kana son samun budurwa, Yarima kaddara ce ta fad’amin, na rasa budurcina ba tare da sani naba dama Nasan dole kayi sha’aw….. Hannunshi yasa ya toshe mata baki, idonshi na cikin nata yace kina magana ko tsayawa ki huta bakya yi, za tayi magana ya k’ara rufe Mata baki tare da fad’in dnt say anything my princess, ku biyu kun isheni rayuwa, ina dake wace mace Zan kalla balle inyi tunanin aurota, wasa nake miki Yarima naku ne ku biyu.

Wani irin murmushi ta saki mai d’auke da farin ciki, Hancinta yaja tare da fad’in oya muje in miki wanka sai ki kwanta kin San yanzu an baki bed rest, so komai bazaki dinga yiba sai dai ayi miki, Kafin jikin ki yayi kwari, matsawa yayi kusa da kunnanta yace nima Ina bukatar matata but baby d’ina ya hana, dole in hakura har sai kinyi sati biyu, amma gskya zan cutu da yawa.

Zainab uhm kawai tace tare da nufa toilet da sauri yabi bayanta yana fad’in bazan bari kiyi wanka da kanki ba, kar a tabamin lafiyan baby.


Ranan da habib ya tafi duk inda yake tunanin Bariki zata je, yaje amma bai ganta ba, dan haka dole yasa ya koma domin yace May be bata shigo kaduna bane, amma yasan dole ta dawo tunda bata da kowa a zaria, tunda anyi mata saki uku, da sauri ya d’auki waya ya kira wanda ya bashi labari inda ya k’ara shaida ma habib Zainab tabar gidan.

Koda Hjy Umaima ta kira ya fad’a mata bariki bata dawo kaduna ba, tace tana ganin zata shigo kaduna din da kanta sai su nemo ta, ikon Allah kunji jaraba.

Hjy habiba tayi mugun shiga damuwa domin harta rame Sosai, d’anta gaba d’aya ya tsaneta, wanda a halin yanzu ta gwammaci daya auro haulat wacce ta gama sanin sirrinta ta kuma ta cita, ace yau d’anta ya aurota wannan babban abun kunya da Tashin hankali da kwamacala Ina zata kaishi, dan haka ta yanke mijinta yana dawowa zata Sanar mishi.

Kaman yanda hjy habiba ta yanke ranan da mijinta ya dawo daka tafiya, saida ta Bari lokacin kwanciya ta shiga d’akin mijin Nata da rigan bacci inda ta sameshi yana danna system, zama tayi a kusa dashi.

Yace lafiya kuwa, yau naga gaba d’aya kaman baki da lafiya, wai Mai ke faruwa ne??

Hjy habiba hawaye ne ke zuban Mata a fuska tare da shesshe’kar kuka, ta Fara fad’in dan Allah ka yafemin Wlh Ina tsoran Sanar dakai abunda na aikata, na cuci kaina da kaina

Jin haka gaba d’aya hankalinshi ya dawo kanta, yana kallonta tare da fad’in habiba maiya faru?

Tace ina son kamin kyakyawan fahimta, na kasance Ina cin amanarka cikin kuka take maganan

Jin abunda ta fad’a da sauri yasa ya tashi yana mata wani irin kallo, cikin kuka taci gaba da fad’a mishi irin abubuwan data aikata, tun sanda take neman maza harta dawo hulda da Mata.

Innalillahi’wa inna ilaihirajiun ya iya furtawa, zama yayi tare da zabga tagumi, alaman yama rasa abunda zaice mata, baka jin sautin komai saina ‘karan Ac da kuma sautin kukan hjy habiba, saida yayi wajan minti Goma Kafin ya d’ago ya fara magana kaman haka, lallai zina mugun alkaba’i daka shirka zina zai biyo baya cikin manyan laifuka, sai yasa Allah (S W A) Yace kada ku kusanceta, saboda munin laifinta, sai yasa akace Idan Matar aure tayi zina kona mijin auren da yayi zina hukuncin jifa ne a kansu, idan kuma saurayi ko budurwa tayi zina a musu bulala d’ari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button