BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Bayan fitan bariki Alh madu murmushi yayi wanda nidai ban gane na miye ba, na mamaki ne? kona nadama ne? kona shirin wani tuggu ne? oho …… Koma dai miye zamu gani in yaji gargadin bariki ko kuma zai sake bibiyarta

Bariki tana zuwa kofar gidansu na u/kanawa ta hango motar Yarima a fake, wanda shi d’aya yazo….. Mamaki abun ya bata Toh Mai yasa bai kirata ba, kuma wayarta na hannunta, tace may be yanzu yazo…… Gaba tayi tazo zata wuce cikin gidan tayi kaman bata ganshi ba, shima yana kallonta baice mata komai ba harta shige cikin gidan….. Murmushi Yarima yayi tare da d’aukan wayarshi ya tura mata message kamar haka……

 Ko in tafi ne??? 

Bariki ganin message dinshi yasa tayi dariya tare da fitowa waje ta sameshi inda yake bud’e motar tayi ta shiga

Kallonta yayi tare da fad’in kina ganina kika wuce

Tace Yarima yaushe na ganka??

Murmushi yayi tare da fad’in my princess inafa kallonki, harda wani kawar dakai Kalan baki ganni ba

Tace Yarima nidai naga mota amma ban San Waye a ciki ba, ko kana son inyita kallon maza ne ??

Bai san lokacin da yayi dariya ba, tare da fad’in koda yaushe kin San hanyar da zaki Kare kanki…

Shuru tayi tana tunanin I wish Yarima yasan gaskiya ya fara sona, hawaye ne ya gangaro mata a ido da sauri tasa hannu ta goge dan karya gani tare da d’ago kanta taga koya gani…. Kur taga yana kallonta…… Da sauri tayi k’asa da kanta

Yarima Aliyu yace Zainab a kullum nazo Wajanki kina Sani fargaba, Wai Mai kike boyemin ne?? Kina sani tunani Kala Kala plz tell me Mai yake damunki banso ki barni cikin duhu…..

Kuka ta farayi tare da fad’in Yarima tunda nake ban taba jin son kowa ba sai Kai, ina jin tsoran abunda zai faru in kasan gaskiyan al’amarin da nake boye maka……. Karan wayan Yarima ne ya Katseta

D’aukan wayan Yarima yayi ganin Sunan waziri ne, ji nayi Yarima yana fad’in ok gani nan zuwa, har kun karaso?…. Kashe wayan yayi tare da kallon zainab yace Bari inje in dawo yanzu.

Bariki tace ok tare da fad’in saika dawo sannan ta fara kokarin fita daka motar…..

Hannunta ya ri’ke tare da fad’in haka zaki fita Fuskanki yana hawaye??….. Janyota yayi jikinsa tare da goge mata hawayen fuskanta yace plz my princess kibar wannan kukan yanzu zan dawo sai muyi magana Kinji?

Kaita d’aga Mai alaman eh.

Murmushi yayi tare da fad’in dat my girl, inna dawo zan fad’a miki albishir

Murmushi tayi tare da fad’in saika dawo sannan ta fita.

Yarima direct u/sarki ya nufa inda Zai had’u dasu waziri a nuna mishi filin da Mai martaba ya bashi sannan suje asibitin shi y’an jarida su d’auka domin a tallata asibitin duk da Yarima baiso hakan ba, amma waziri yace ayi tunda yace zai Fara aiki na wata uku kyauta akan matsalolin mata tunda shi likitan mata ne, ta gidan tv da radio mutane za suji marasa karfi su zo….. Asibitin ba Yarima kadai bane zaiyi aiki a cikinsa ba harda wasu likitoci na fanni daban daban……

Bariki bayan ta shiga cikin gida, ummanta tace Zainab Yadai har Yarima din ya tafi?

Tace eh amma zai dawo…. Wai har yanzu habib bai zoba? Tun dazu yake cemin yana hanya…..

Sallaman habib dinne yasa tayi shuru ya shigo yana gafaran ku dai masu gida

Shiga d’akin dasu bariki suke yayi yana fad’in in shigo ko in jira a kimtsa….

Bariki tsaki taja Tana fad’in Asara, bayan ka shigo din kake tambaya koka shig……

Waige ya farayi yana duba dawa bariki take magana, yaga babu wani namiji a wajan yace ke dawa kuma?? Naga banga ko wani namiji a nan ba

Bariki tace dakai nake mana…

Yace Wlh bariki zan miki rashin mutunci miye wani ka? Mai yakai mace jinsin maza, gskya banso yana maganan yana hura hanci Kalan ranshi ya baci…..

Umman bariki ta Karya babu abunda take sai dariya, tace Zainab gskya bakya kyautawa taya zaki dinga kiranta dana miji Bayan kin San macece y’ar uwarmu….

Habib yace fad’a mata dai

Bariki dariya tayi tare da fad’in ni bama wannan ba kawata kina ji??

Habib yace kunne aike ji

Bariki bashi Labarin yanda sukayi da Yarima tayi Kafin yace zaije ya dawo, taci gaba da fad’in Wlh Ina son fad’a mishi gaskiya Kinga sai muyi aurenmu lafiya ba tare da matsala ba…..

Habib gyara zama yayi yace lallai Bariki, ban taba sanin baki da wayau ba sai yau. Ke kina tunanin in kika fad’ama Yarima gaskiya zai aureki?? Kin bashi iyayen karya tare da Labarin karya ke kina tunanin duk son da yake miki zai yarda ya aureki? Karki manta kina fad’amin yanda yake kyaman mace mazinaciya, sannan kike gigin son fad’a Mai gskya? Toh inma shi Yariman ya yarda ya aureki kina tunanin iyayenshi zasu yarda??? Bariki kin San Gidan sarauta kuwa?? Shawaran da zan baki shine kiyi shuru da bakinki kiyi yanda kika tsara in an d’aura aure kya fad’a mishi gaskiya tunda naga kina mishi son tsakani da Allah kuma naga kina son zaman auren, kuma nasan bazai sakeki ba tunda ya aureki kuma basa saki….. Yau inda bakya sonshi Kinje gidan da wani manufa ne sai kice mai fyad’e aka miki, amma tunda son gaskiya kike Mai saiki fad’a mishi gaskiyan koke wacece.

Mahaifiyar bariki ta Karya, tace bariki gaskiyan habiba ne, wlh Indai kika fad’a mishi gaskiya zaki iya rasashi kuma na har abada, gidan sarauta zasu iya yarda su rasa d’ansu akan ace ya auro musu karuwa domin abun kunya ne, ki duba kiga su ko aure kayi a gidan sarauta sai Anga jini shine kin Kai budurci… Bayan bako wace mace ke jini ba kuma budurwa ce

Habib ya tabe baki tare da fad’in nidai Allah yasa ina d’aya daka cikin mata masu zubar da jinin, Kar insha gorin miji …. Dan mazan nan ba mutunci garesu ba…..????????????????

Bariki tace toh kuna ganin inna aureshi na fad’a mishi zai hakura dani?

Habib yace insha Allah, dole ma ya zauna dake tunda bada gardi ya kamaki ba, ai yanda kikaji dad’i al’adan gidan basa saki, sai an kamaka da gardi kuma kince kin tuba…..kuma na tabbata koda yayi fushi zai sauko tunda ya aureki zaki san hanyar da zaki janyo hankalinsa ma dole ya sauko, domin ya sami. santaleliyan yarinya son kowa k’in Wanda ya rasa…… Toh Bari dai mu gani bariki zata fad’ama Yarima inya dawo koko ta d’auki shawaran habib au???? Anty habiba…..

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 11*

Dariya bariki tayi tare da fad’in, amma ina tsoran irin fushin da Yarima zaiyi, Wlh ban son inga ya shiga wani hali, bazan iya jura ba, ina sonshi da yawa…..

Habib yace Toh fah, yau Ina ganin bariki…. Toh yanzu dai Mai kika yanke….??

Bariki tace abunda kuka fad’amin dashi zanyi aiki, ranan da aka d’aura aurenmu aka kaini ranan zan fad’ama Yarima gaskiya…..

Habib shewa ya saki tare da fad’in Aiko ki tabbatar kin fad’a mishi tun Kafin ya shiga yaji ya shige zirif kaman bakin gate…..

Bariki duka takai ma habib iya karfinta tare da fad’in rafi ne ba gate ba

Habib ya ri’ke wajan da takai Mai duka yana fad’in na shiga uku zata kassarani….. Amma dai kekam bariki baki da mutunci yanzu ki takarkare iya karfinki ki sakan min wannan uban dukan yanzu inda kin sameni a wajan nono Nafa? Bayan kin San sarai ance a nan rayuwar mace take, salan kije ki kasheni Banyi aure ba naji yanda ayabar nan take ba……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button