BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Haka dai suka barshi Ina shekara shabiyar a duniya Ummaa ta rasu ????????, naji mutuwar Ummaa Ina tunanin Nafi jin Nata akan sanda naji mutuwar mum dina, har saida na kwanta a asibiti, a lokacin na k’ara yarda ba mutuwa akema kuka ba, shakuwa ce da Sabo akema kuka, haka na k’ara fad’awa cikin gararin rayuwa tare da kadaici, mahaifina yana matukar jin tausayina Sosai…..

Bayan rasuwan Ummaa family din dad dina suka k’ara taso mishi da maganan aure, wannan karan basu mishi da wasa ba, kusan duka y’an uwanshi suka had’u harda mamanshi wato kakata tunda mahaifinshi ya dad’e da rasuwa, dole yasa ya amince ganin yanda suka nuna fishinsu akan ya k’ara aure…….. Wata y’ar uwarshi aka aura Mai Mai suna Falmata wacce mijinta ya rasu ya bar mata yara biyu Mata, ganin abbana yana da kud’i yasa akace zai iya ri’ke yaran dan haka tare aka kawota da yaran, gidan dad dina dake Abuja.

Falmata Tana nuna min so Sosai, bata Bari koda kud’a ya tabani, mahaifina yana jin dad’in hakan, sannan komai zai mana tare yake mana da Kananan yaranta, haka dai rayuwa taci gaba dad dina wata rana ya d’aukeni mukaje bank aka bud’emin account, gaba d’aya kud’in da mum dina ta bari aka samin kud’i masu uban yawa a lokacin kusan 20mil banda kadarori data bari tare da gidan gona Wanda kullum cikin samun kud’i ake, komai na mum dina dad dina yace cikin account dina za’a dinga sawa…. Na nuna ma dad dina daya Bari a wajanshi amma yace a’a in ri’ke hakki nane…….. Mahaifina yana nuna min tsantsar so Sosai har baya iya boye son da yakemin gaban kowa kullum magananshi ni tare da fad’in irin tausayi na da yake ji……… Dad dina yana yawan zuwa gari gari wa’azi da kasashe, ganin matarshi Tana kula dani yasa ya yarda yake tafiya yabar mata ni….

Lokacin da nake shekara Goma sha bakwai komai nawa Ya fito, kyau diri Kirjina komai nawa dai tubarkallah, Falmata duk kawayenta kana kallonsu zaka gane y’an duniya ne, sannan basa zuwa gidan sai dad dina baya k’asar……..

Wata rana Ina d’aki na fito daka wanka daka ni sai towel, ina zaune ina shafa mai saiga Falmata ta shigo, da sauri na tashi Ina kokarin in d’auko abu in rufe jikina A Kai rashin Sa’a towel din ya fad’i, gaba d’aya idon Falmata na kaina, da sauri na shige towel na rufe Ina kuka domin naji kunya Sosai ranan

Ranan dai a d’aki na wuni banko le’ko ba

Washegari na fito da yake lokacin ina zana waec kuma ranan shine paper na karshe na fito zani skul cikin jin kunya, saiga Falmata tazo ta ri’ke min hannu tare da fad’in haba zainab, mai yasa tun jiya kika k’i fitowa nifa mamanki ce kiyi hakuri dana shigo ba tare dayi miki nocking ba, tunda ta ri’ke min hannu sai wani murmurzawa take kaman filo ta ri’ke, ganin zanyi lati gashi tana ta wani shafa min hannu yasa nace ummi zanyi lati.

Murmushi tayi tare da fad’in muje in rakaki mota, har mota mukaje ta sani tare da fad’ama driver ya kaini a hankali

Tun daka ranan Indai Falmata zata min Abu saita tabani ban taba zarginta da wani abu ba, duk tunani na tanayi ne saboda in saki jiki da ita, domin tunda Abun nan ya faru nake jin kunyanta Sosai, haka zatai taja na da fira ni gashi ban cika son magana ba……

Wata rana dad dina yaje saudiya umra ,ina d’aki ina karanta wani hadith daka ni sai kayan bacci a jiki na, kawai Falmata ta fad’o d’akin dama kwana biyu ban cika bari muna had’uwa ba inma mun had’u nesa nesa nake da ita domin ban son yanda take yawan tabani….. Ganin ta shigo d’akin yasa na tashi tsaye domin taban tsoro irin kallon da take min….. Nufoni tayi tana y’ar murmushi tare da fad’in baki bacci ba har yanzu?

D’an murmushi nayi tare da fad’in eh ummi.

Matsowa tayi gab dani tare da min wani irin kallo da yasa gabana ya fara fad’i….

Tace Zainab nazo ne muyi wata magana wacce nake fatan zaki amince min??

Cikin rawar baki nace eh ummi insha Allah

Shafamin fuska tayi tare da fad’in yauwa my daughter

D’an ja baya nayi kad’an

Murmushi tayi tare da matsowa kusa dani ta janyoni jikinta ta rungume har ina jiyo sautin ajiyan zuciyarta, a hankali tace Zainab plz ina son ni dake mu dinga biya ma juna bukata, Wlh sonki ya kamani dan Allah ki yarda kiban had’in Kai…..

Da sauri na fara kokarin tureta amma na kasa domin tayi min ru’ko Sosai, bakinta take kokarin kaiwa nawa ina kuka ina tureta har Allah yaban Sa’a na cije ta a hannu da sauri ta sakeni, na shige toilet na rufe, kuka nake Sosai tare da tsoro da mamaki, dama ummi tana yin mad’igo Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, ranan na tsorata Sosai tare da k’ara jin tsoran duniya….. Tunawa da irin azaban da Allah ya tanadar ma masu yin mad’igo sannan zamanin annabi ludu an kifa duniya saboda luwadi da mad’igo, yau shine ummi take aikatawa…… Tunawa tayi da sanda malaminsu yake musu wa’azi akan masu aikata mad’igo ko luwadi…… Inda yace

Mad’igo ko luwadi babban zunubi ne a musulunci, wanda za’a iya cewa Idan aka cire shirka, da kafirci to yana iya biyo baya…….

Sannan hukuncin wannan mummunan aikin luwadi ko mad’igo yana kusan dai daine da mutumin daya zagi Manzon Allah….. Kuma Kun San hukuncin Wanda ya zagi Manzon Allah…..

Manzon Allah (S A W) yace

Mafi girman abunda yake jin tsioranshi akan Al’ummata shine aikin mutanan Annabi LUD….

mai nene aikin mutanan Annabi LUD??…… shine luwadi da mad’igo Allah ya tsare…..

A wani hadisi so uku ajere Manzon Allah yana tsinema Wanda yake aikata irin aikin mutanan Annabi LUD…..

Manzon Allah (S A W) Yace….

ALLAH YA TSINEMA WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANAN ANNABI LUD, ALLAH YA TSINEWA WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANAN ANNABI LUD, ALLAH YA TSINEMA WANDA YAKE AIKATA AIKIN IRIN MUTANAN ANNABI LUD
Asara da tabewa ta gama tabbata akan mutumin da Manzon Allah ya jera Mai tsumuwa har guda uku akanshi.????????????

Sannan Manzon Allah yace…. Duk Wanda kuka samesu suna aikata irin aikin mutanan Annabi LUD to kukashe maiyi da wanda akeyi dashi

Sai dai a cikin hadisai ana samun rauni da wanda bai inganta ba…….

Sannan malamin mu ya kara dacewa duk mai aikata luwadi ko mad’igo hukuncin shi Indai aka kamasu wasu sunce……..

A jefesu wasu kuma sunce a k’ona su, wasu kuma sunce a sami bene ginin gidan sama wanda yafi tsawo a jefo su aita musu haka har sai Sun mutu???????????????????? Wlh muji tsoran Allah, y’an mata da samari kunji wannan babban laifi ne wlh masuyi ku tuba ????????????????

Bariki kuka take Sosai tare da tsoran Falmata lallai Asara da tabewa ya tabbata akanta aikata lesbians, kuka take Sosai tare da burin Dad dinta ya dawo ta fad’a Mai……

May be anjima inyi muku wani ko gobe da safe

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 20*

WARNING: DUK WACCE TAKE GROUP DINA, DAKA YAU DUK WACCE TA K’ARA TURO NOVELS DIN DA AKACE NA KUD’I NE WLH ZAN CIRETA KO WACECE, NAGA WASU ABUN NASU YANA YAWA, ANCE NA KUD’I NE NA KUD’I NE, IN BAZAKA BIYA BA KARKA KARANTA SAI KACE DOLE, NIDAI NA FAD’A DUK WACCE TA K’ARA TURA NOVELS DIN DA AKASA NA SIYAR WANE CIKIN GROUP DINA WLH SAI NA CIRETA????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button