BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Bariki tace hjyta babu inda zani domin wlh ni aure zanyi kuma istabra’i nakeyi dan so nake inyi tsarkakken aure…..

Hjy babba yace au me????!

Tace aure…….

Yace gaskiya banji dad’in wannan maganan ba Wlh Ina ke ina wani aure yanda kike da kyau da lafiya ga kuruciya, gskya banji dad’in jikina ba wai mahaukaciya taji duka…… Gaskiya bariki ki canza shawara ai yanzu ne kike da dama kuma shi komai na duniyar nan lokaci ne gwara kici naki lokacin daka baya kyayi auren in kin daina tashe amma haka kawai tsigai fiyau kina tashe ki wani cuta kanki Muma ki cucemu dan abunda muke samu saboda ke mu daina samu, ki makale waje d’aya da Sunan kinyi aure gskya raina ya baci

Bariki tace hjyta nidai bacci nakeji yanzu wlh kuma shi nakeyi kika tasheni dan Allah hjyta ki bari in koma bacci

Hjy babba yace oh yau naga ikon Allah, amma dai wlh bariki kin canza kuma Nasan yanzu bakya d’aukan maganan kowa saina Shegiyar habiba Dan naga yanda take shige miki, karki manta Nina Fara saninki Kafin habiba kuma saboda ni kike nan gidan…..

Bariki tace hakane hjyta kena Fara sani Kafin habiba, and kuma kinmin hallaci Wanda bazan manta dake ba, sai yasa har gobe nake mutuntaki hjyta

Hjy babba yace bariki Indai kina ganin mutuncina kizo muje wajan alh madu ni koda bazaki yarda dashi ba, dan Allah kizo muje Yadai ga na kawo mishi ke domin yana ganin mutuncina ko so kike ya daina, sannan inma Kinje shida kika ce ayabar tashi kaman ta yara Aiko yayi ba komai za kiji ba….

Bariki tace nifa hjyta gskya babu inda zani domin na riga na yanke hukunci kuma na fad’a ma driver dinshi sa’ko ya bashi, wato shine daya fad’a Mai shine ya Aiko ki, Toh wannan karan zaisha mamaki domin babu inda zani kuma na fad’a

Hjy babba yace oh na shiga uku an fasa aurena haka gasau kike fad’a babu inda zaki??…. Amma kam in kikai haka baki hallaci ba bariki ki duba fah har kyautar mota yayi miki……

Bariki tace Aiba ro’kansa nayi ba shiya d’auka ya bani Dan haka kuma ta bayu,.

Hjy babba yace dan Allah bariki Kar kisa nidai ya daina ganin mutuncina ki daure kizo muje koda zaginshi za kiyi nidai yasan na kawo ki, sannan in Kinje kya fad’a mishi abunda ke ranki Kinga tayu ya barki ya nemi wata……

Jin haka yasa bariki tace muje, inji uban Mai yasa ga mata Nan a gari wanda suka fini iya zuba bariki bai nema ba sai ni, muje inji dalili Danni Wlh na gaji da wannan iskancin nashi…. D’akin ta koma tasa hijab dogo har k’asa akan rigan baccinta tare da rufe d’akin tace ma Hjy babba muje…….

Bakin titi suka nufa da yake garin yau ake wasa akwai mutane birjit, samun Abun hawa bai musu wuya ba, inda suka sami Mai keke napep suka shiga, direct gidan alh madu ya kaisu hjy babba ya biya kud’in sukai nocking Mai gadi ya bud’e dan yasan hjy babba da bariki, kofar falon alh madu a bud’e yake dan haka suka shiga baya falo bariki bedroom dinshi tayi taganshi tsirara yana video call daka gani da wata mace yake, alh madu waya yake bai Masan bariki ta shigo ba saida yaga hasken wayarta alaman an d’aukeshi hoto…… Da sauri ya tashi yaga bariki ce murmushi ya saki tare da fad’in Kaga manyan mata maganin kanana, nufanta yayi tare da janyota jikinshi Wanda babu kaya yace Bari in d’auke mu kit kit ya fara d’aukansu a wayarshi bariki kokarin Jan jikinta ta farayi tare da fad’in miye haka ne Dallah sakeni, andai ji kunya wlh kaje can ka karata da sauran y’an iskan y’an matanka badai bariki ba womanizer kawai fuuuuuu ta fita ta barshi yana kiranta ganin ta fita yasa ya fara saka kaya da sauri dan ya cin mata dan yasan Indai ta zille Mai shida ya kuma ganinta sai anji jiki tunda yanzu tazo yau yake son sanin Mai take nufi domin ya shirya Mata kota yarda ta aureshi kota fasa maganan auren da take fad’in za tayi suci gaba da cin juna babu aure, kuma yayi alwashin cikin biyu dole ta zabi d’aya…….

Ina masoya novel’s dina ina muku albishir da novels din da nayi baya wanda babu su a Wattpad zan fara sa muku su wanda na fara sa muku AMINIYA TA CE ,inna Gama sashi zan d’aura muku wani shima insha Allah

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 7*

Alh madu riga kawai ya iya samu yasa ya fito…..

Bariki fuuuu ta fita Hjy babba ya bita yana fad’in bariki Yadai Anya lafiya kuwa?

Bariki bata kulashi ba taci gaba da tafiya cikin sauri

Yace bariki Wai Mai ya faru koya mutu ne Alh madun ???

Bariki tace Aidama mutuwar yayi da nafi kowa murna dan iskan tsoho tsinanne…..

Hjy babba yace oh ni amma gaskiya bariki baki da hali…..

Hango Alh madu tayi yana nufosu da sauri ta fita daka gidan….

Hjy babba ya bita yana fad’in ta tsaya mana ga Alh madu dinnan ya fito yana kiranta….

Ko kallon hjy babba batayi ba ta wuce abunta tako yi Sa’a taga wani mai mashin da sauri ta tsayar dashi tahau, tana fad’a Mai inda zai kaita, mai mashin yace dubu d’aya bata musa ba dan itama tasan dare yayi ba kowa bane zai kaita maraban jos yanzu a mashin ba……

Hjy babba wajan Alh madu ya koma wanda shima alh madu ya koma yasa wando ya fito……

Alh madu bayan ya fito ya kalli hjy babba yace tana Ina??

Hjy babba yace aita wuce ta sami Mai mashin tahau.

Kai Alh madu ya d’aga alaman yaji tare da cema hjy babba ina zuwa, bedroom ya shiga sai gashi ya fito da bandir din dubu d’aya dubu d’ari kenan yaba ma Hjy babba tare da fad’in kaje zan nemeka…..

Hjy babba amsa yayi yana ma alh madu godiya tare da fita……..


Bariki ce kwance a d’aki tana ta kiran number din Yarima ya’ki d’auka Dan tsaki taja tare da fad’in bazan kara kira ba, in kaga dama ka kirani, sa wayar tayi a silent ta fad’a toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata jallabiya yayi mata kyau ta yafa gyalen jallabiyan ta d’auki jakarta da wayanta ta danna ko zataga miss call din Yarima amma shuru babu ma wanda ya kirata, tsaki taja sannan ta fita cikin damuwa, had’uwa sukayi da hjy babba……

Ja yayi da baya ya kama kugu kaman wanda zaiyi dambe, yace amma ke kam bariki ko ri’kakkiyar y’ar iska, in banda iskanci da wulakanci ki k’ekashe ido kici min mutunci, Nina rasa mai yasa kika tsani wannan mutumin yana sonki kina gudunshi kaman Kinga kashi……

Bariki tace haba hjyta wannan jaraban fah da tujara da sassafe?

Hjy babba yace aike kika so wlh bariki baki da hali, gwara ki canza wannan ba’kin halin naki tun wuri….. Yana fad’in haka yayi gaba yana ta surfa bala’i shi’a dole bariki ta bata mishi rai gwara yayi gaba karma ya tsaya bata ma kanshi lokaci wajan magana da ita…..

Bariki ganin haka ta girgiza kai tare dayin gaba tana fad’in kaji dashi wai anyi ma mai dami sata….. Bama Alh madu ba babu wani namiji da zai kara sanin ko ita wacece domin ta tuba abunda ta aikata baya shima tana ro’kan gafaran uban giji akan ya yafe mata duk da itama inta zauna wani zubin takanyi mamakin irin abunda ta zuba a matsayinta na y’a mace Mai shegen kunya a da, amma lokaci d’aya ta sauya Wanda har yanzu ta kasa gane dalili, sai dai wani zubin takan kalli abun a matsayin Tana son musguna ma iyayenta ne sai yasa take hakan, duk da shima hakan bawai ya tabbatar mata a rai bane kawai inta fad’i hakan ne take ganin hakan shine silan fad’awanta wannan mummunan harkan…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button