BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Bariki jikinta yayi matukar sanyi Sosai lallai Yarima in yasan wacece ita ya barta har abada….. Tsayawa tayi da kukan amma hawaye na zuban Mata a ido Sosai amma yata iya tata kaddaran kenan dole ta fad’a mishi gaskiya domin hakan shine zai sa ta sami salama duk da itama ba zata iya juran rashin Yarima Aliyu a rayuwarta ba, domin so ya mata shigar sauri sonshi ya shigeta Sosai wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba…….

Katse mata tunani yayi tare da fad’in Zainab tell me plz….

Shuru tayi tana kokarin yin magana amma ta kasa domin muryanta ya dashe……

Ganin haka yasa Yarima fad’in kiyi shuru kibar wannan kukan plz Kinji my princess?

Kaita d’aga mishi alaman toh

Yarima Aliyu idonshi na kanta ya tabbata akwai abunda take boye Mai, but koma miye zai sani….. Ganin tasa hannu a kanta alaman yana mata ciwo yasa yace my princess ciwo Kai din yake miki?

Kaita kara d’aga Mai alaman eh , bud’e kofar motar yayi ya shiga wajan driver ya kunna motar,

Da sauri ta d’ago ta kalleshi ganin yaja motar yasa ta kura mishi ido, taga Ina zashi da ita…… Karan wayanshi ne yasa ta dawo daka duniyar tunanin data fad’a

D’auka yayi tare da fad’in USMAN sorry yanzu zamu dawo, zan kaita pharmacy ne a bata magani she has a headache….. Yana fad’in haka ya kashe tare da fad’in Ameen

Yarima cikin gari suka shiga inda aka bama Zainab magani, tare da sai mata kayan fruit sannan suka kamo hanya, bayan sun karaso Bariki suka gaisa da USMAN sannan Yarima yayi mata sallama akan taje tasha magani, ta kwanta ta huta sai sunyi waya……

Bariki gidanta take ta koma ta shiga d’akinta ta kwanta bayan tasha magani bata dad’e ba bacci yayi awon gaba da ita

Usman tun a mota yake tsokanan Yarima Aliyu, akan dole ya mutu akanta yarinyar tana da kyau sai dai karama ce ba wata babba bace……

Yarima dai banza da USMAN yayi domin haushin yanda yake ta fad’in Tana da kyau yakeyi, d’an tsaki yayi cikin ranshi yace bazan kara zuwa dashi ba, tunda Kalle min Mata yake tayi…

Yarima bayan sun koma direct gefenshi ya nufa inda yayi bedroom dinshi yayi wanka, yana cikin sa jallabiya danya kwanta

Gimbiya zinatu ta shigo d’akin tare da fad’in Yarima …..

Yace ya akayi….

Tace ina son magana dakai

Baice mata komai ba sai zama da yayi akan gadon d’akin tare da d’aukan wayarshi yana dannawa…..

Kollonshi tayi cikin jin haushin rashin kulata din da baiyi ba, tace haba Yarima wai mai yasa kake haka, yau kwana na uku a gidan nan a matsayin matarka, amma baka da lokaci na, kullum inka fita sai dare, karka manta wannan baya d’aya daka cikin abunda miji ya kamata yayi ma amaryanshi, duk wani ango zama yakeyi a gida in yayi aure ya dinga kula da matarshi, yau koda bazawara ka aura ai kayi d’auki balle ni budurwa….

Yarima Aliyu kallonta yayi tare da d’an sakin murmushi yace d’auki?? Akan me? Bayan har yanzu ban San maina aura ba……

Cikin faduwan gaba tace kaman ya Yarima ban gane ba …

Idonshi na kanta domin yana son yaga yanda zatai reaction amma ga mamakinshi sai yaga batai yanda yake zato ba, kenan gimbiya budurwa ya sameta dagaske, inko hakane ya kamata ya dinga bata hakkinta duk da bawai yana jin Sonta bane a ranshi, amma tunda ta kawo budurcinta sai yaji tayi girma a idonshi, duk da Abun ya bashi mamaki, dan baiyi zaton haka dinba……

Jin kukan gimbiya zinatu shiya sa yarima ya dawo daka duniyar tunanin da yake…… Ganin yanda take kuka yasa zuciyar Yarima tayi karaya tare da tausayinta , tashi yayi ya ka mota ya kwantar da ita akan jikinshi yana fad’in plz ki daina wannan kukan…..

Cikin kuka take fad’in haba Yarima dole inyi kuka, yanzu Yarima ace Ina amarya amma kullum saika fita, kuma inka fita sai dare, har an fara magana akai na, ana fad’in baka d’auki na , kasan gidan sarauta akwai ya’da magana haba Yarima mai yasa baka sona? Maina rasa……

Hannunshi yasa akan bakinta yace ya isa haka,

Ganin kaman Yarima ya tausaya mata yasa taita Mai juye juye a jiki,

Nan sha’awa ta motso ma Yarima Kafin ace Mai har an fara harka…….


Alh madu ne shida hjy babba kallon hjy babba alh madu yayi yace abunda yasa na kiraka dagaske ne bariki zatai aure ko wasa takeyi??

Hjy babba yace haka tace kuma ina ganin kaman dagaske take, dan naga gskya yanzu bata bin maza, inma tanayi Toh a boye takeyi….

Murmushi Alh madu yayi tare da fad’in ok, ina son kayi min bincike akan wa zata aura sannan a ina yake, ina nufin Ina dai son sanin Waye shi da kuma sanin daka inda ya fito…..

Hjy babba yace an gama ranka ya dad’e

Kud’i alh madu yaba hjy babba, sannan ya tafi

Alh madu yace bariki Nasan bana gamsar dake, amma ni kina gamsar dani, inko dai bani zaki aura ba, shima wanda yake son canza ki dole ya rasa ki,inko na bari kinyi aure toh sai dai in zaki amince ko kinyi aure kici gaba da bina murmushi ya saki tare da fad’in zan nuna miki ni Alh madu ba’amin wargi………

AYSHA BAGUDO….. na amsa sa’ko Ina matukar godiya Allah yabar k’auna da zumunci, Allah yasa zumuncin mu har abada Allah ya tsole idon makiya, Wlh naji dad’in sa’kon da kikayi min Sosai ngd ngd, ina matukar kaunarki kaman yanda kike kaunata Allah ya biya miki bukatunki na alkhairi, makwabciyata ta gidan Aljanna insha Allah

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 9*

Bariki bata farka ba sai da asuba, jin kiraye kirayen sallah shine yasa ta farka, kuma bata tashi da ciwon kai dinba, tashi tayi ta fad’a toilet, alwala tayi tazo tayi sallah, tare da ro’kan Allah akan ya shiga lamarinta…… Koda ta idar kasa komawa bacci tayi sai kayanta na sawa data fara sawa cikin karamin akwatinta domin zuwa wajan iyayenta na bariki danta d’an Fara kwana a can, gashi yarima yace ta koma yau dinma.

Bayan ta d’iba kayanta na kwana biyar tasa cikin akwati ta rufe tare da ajiye akwatin a gefe, kwanciya ta koma amma ta kasa bacci domin ba komai take ba sai tunani, a duk lokacin da taso ta fad’ama Yarima gaskiya saita kasa, sai kuka yazo mata in tayi kokarin ta daure ta fad’a mishi saiya kashe mata Giwa da fad’in bazai auri mazinaciya ba… Wani hawaye ne ya zubo mata Mai zafi, Tana son Yarima bata son rasa shi, lallai Indai tana son samun Yarima a matsayin miji shine ta boye mishi labarinta har abada….. Da sauri ta girgiza kai tare da fad’in labari na bazai taba boyuwa ba domin komin daran dad’ewa sai gaskiya ya fito, lallai fad’ama Yarima gaskiya shine mafita amma sai bayan na aureshi, zanyi kokarin in fad’a mishi gaskiya ranan daya aureni Nasan May be yayi min uzuri, tunda ba haka nake ba, kaddara ce ta fad’amin wanda nida kaina bazan iya cewa ga abunda ya faru ba, koda za’a samun wuka a wuya ban San yanda Abun ya faru ba……


Haulat ce take jan akwatinta daka gani tafiya za tayi….

Hjy habiba tana bayanta tana fad’in yanzu sai yaushe kuma?

Haulat tace mum sai dai munyi waya, kawai

Farhan ne ya fito tare da fad’in muje in kaiki train station…..

Hjy habiba tace farhan ka Bari driver ya kaita mana,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button