BARIKI NA FITO 1 & 2
Habib yace oh dama tare kuke Aida kamin bayani tun Farko muje.
Yarima duk wannan abunda suke yana kallonsu amma baya jin abunda suke fad’a, danko bai tambaya ba yasan habib dan daudu ne domin yanda yaga yana abu, sannan kan Yarima ya fara kullewa domin ganin irin mutanan dake sintiri a wajan.,
Toh miye tsakanin yarinyar daya gani da wannan dan daudu din?
Jin bud’e motar yasa Yarima ya dawo daka duniyar tunanin daya Fara.
Habib ne ya shigo motar sanyin AC ya dukeshi ga kamshi na tashi, yace oh aljannar duniya Mai kud’i bai kwana da haushin kowa ba.
Kallon Yarima yayi wanda yaga ya mishi kwarjini, yace ranka ya dad’e barka da zuwa, ina fatan dai lafiya?
Yarima Aliyu yace lafiya, ina da tambayan da nake son maka ne.
Habib kasa cewa komai yayi duk da yarima yace mishi Kai ba ke ba, sai fad’i yayi Ina ji.
Yarima Aliyu yace kwanakin baya nazo wucewa na ganka tsaye kaida wata yarinya tasa hijab a bakin titi….
Tun Kafin Yarima ya karasa magana habib yace bariki kake nufi?
Yarima yace what bariki kaman ya?
Ganin yanda Yarima ya shiga da yaji yace bariki yasa ya gane badan hannu bane, saiya wayince yace Ina nufin gidan duniya kaman bariki ne zaka ga mutane da yawa sai yasa nace bariki kake nufi ina nufin ni inada mutane Kala Kala.
Jin haka yasa Yarima hankalinshi ya kwanta dan da har yaji kirjinshi ya fara bugawa da karfi
Yace baiyi sati biyu ba na ganka kaida wata tasa hijab ta ri’ke akwati daka gani bakuwa ce.
Habib yace au kodai Zainab kake nufi? Tasa hijab blue koh?
Yarima yace eh itace
Habib yace Zainab baiwar Allah Aiba a nan take ba, gidansu yana cikin gari, tana zuwa wajan y’an uwanta ne a nan.
Yarima yace ko zaka iya kaimu gidansu?
Habib yace Kai Anya zata kulaka kuwa?
Inaga ka bani number dinka inna mata magana sai in tura maka number dinta, sai ku Fara magana koh?
Yarima yace hakan yayi bashi card dinshi yayi tare da dauko kud’i bandir d’aya y’an dubu d’aya d’aya ya bashi dubu d’ari kenan.
Habib amsa yayi tare da zabga Mai godiya yace saika jini ranka ya dad’e.
Kai yarima ya d’aga tare da fad’in ka tsaya a baka babban riga, inka fita kama driver dina magana.
Habib sai murna yake tare da godiya.
Habib fita yayi ya Kalli driver din Yarima, tare da Galla Mai harara yace ana magana dakai.
Driver din bud’e motar yayi
Ban San mai yarima yace Mai ba sai gashi ya rufe motar tare da bud’e booth din motar da wasu fadawa ke ciki ya d’auko kaya a Leda ya mi’ka ma habib tare da fad’in gashi Hjy.
Habib amsa yayi tare da fad’in dan rainin wayau.
Murmushi driver din yayi tare da fad’in Allah ya shirya, mota ya shiga suka wuce.
Shiko habib gidan ya koma, cikin murna, direct d’akin bariki ya nufa.
Nocking yayi tace Waye?
Yace bud’e mana.
Jin muryan habib yasa ta bud’e kofar.
Shiga yayi yana fad’in bariki bariki gskya inda ban sanki ba, da Nayi Asara.
Kallonshi tayi tace maiya faru haka? Wannan ledan fah?
Dariya yayi tare da fad’in kyauta aka ban duk saboda ke.
Tace ni? Waya baka?
Zama yayi tare da ajiye ledar yace d’an Sarkin Zazzau Yarima, shida kanshi yazo nemanki.
Tace kaman ya?
Labarin abunda ya faru ya bata, tare da fad’in Kinga kyautar da yamin ya nuna mata kud’in da Yarima ya bashi, tare da bud’e ledar shadda ce dinkakku har Kala biyu kuma duka gezna, habib yace oh Kinga Abun arziki, ni Ina mace anban kayan y’an maza.
Bariki dariya tayi tare da fad’in wato shi ustaziya yake so? Dariya ta kuma saki oh hijab ya gani shi’a dole yaga Kamila matar aure, dariya take Sosai harda hawaye lallai sai yanzu na gane maganan nan da ake cewa karka taba shaidan mutum domin baka san maike zuciyarsa ba, lallai inda yasan wacece ni da bai kawo kanshi ba.
Habib yace Kedai kina da matsala kin ganshi ne? Wlh ya had’u na tabbata irin mijin da zaki burin aure bee, sai dai gskya ina tsoran Idan yasan koke wacece ban tunanin zai aureki.
Bariki dan shuru tayi can tace, toh ai nima ba aure nace ina so ba, bariki na fito, .
Habib yace oh ni habiba rabo na kiran mutum yana gudu, wlh zaki ci dukiya iya dukiya ga sarauta, ga guy din ya had’u, amma naga akwai miskilanci.
Bariki tabe baki tayi, tace habib kasan n……..
Dakata Mlm habib ya Katseta, wlh zan miki bura uba, wai mai yasa kike min haka y’ar A dince kike kyashin karasawa, gaskiya banso yana maganan yana wani daure fuska tare da hararan bariki shi’a dole ranshi ya baci.
Bariki tace yakuri kawata
Tabe baki yayi tare da fad’in hakuri kaya ne.
Bariki tace kawata babu abunda na tsana kaman in yaudari mutanan kirki, kince wannan badan hannu bane, aurena yake son yi?
Habib yace kwarai dagaske.
Bariki tace bazan iya soyayya dashi ba, yafi karfina.
Habib ya tabe baki, tare da fad’in kaman ya yafi karfin ki? Haba bariki ai babu namijin da yafi karfin ki, kalli madubi ki gani mana kina da kyau na bugawa a jarida.
Bariki tace hakane, niba mutuniyar kirki bace, bazan yaudari mutanan kirki ba, hawaye ne ya zubo mata a ido, da sauri ta goge dan Kar habib ya gani, but is too late dan ya riga da ya gani.
Yace Mai zan gani haka? Bariki Kece kike hawaye? Babban magana, toh amma miye dalilin ki na cewa ba zaki yaudari mutanan kirki ba, aiba ke kika ce kina sonshi ba.
Bariki tace kawata mutanan kirki suna da kyakyawan zuciya, suna saurin yarda da Abu, in zaki fad’i gskya kawata keda kanki kin San mutumin kirki kamili bai dace dani ba.
Habib yace a’ah Wlh.
Bariki tace nidai yanzu bazan ganshi ba dan ban shirya aure ba.
Habib yace ban son bariki Mlm, Kar kisa ya maidani karamar mace, mai magana biyu, dan kawai nace miki kamili ne, Aiba daka nan yake ba, ki bari ki had’u dashi sai ki gane ko Waye shi.
Bariki shuru tayi tana nazari, can tace hakane zan had’u dashi, ka bashi number dina zan gane koshi Waye.
Habib yace yanzu naji Batu.
Bariki tace yau wani mai kid’a ne zaiyi wasa?
Yace masu kid’an kwarya yau muka gayyato.
Bariki tace Kai yau zamu ra’kashe.
Yarima ya koma Gida, koda ya isa gefenshi ya shiga domin yayi matukar gajiya, yana shiga bedroom dinshi kwanciya yayi akan gadon d’akin tare da lumshe ido, yau yana cikin farin ciki domin nan bada dad’ewa ba zaiga yarinyar da yake burin gani wajan shekara da shekaru.
Ya dad’e yana kwance yana tunanin bariki, son yarinyar yana kara shiganshi koda yaushe, d’auko drawing dinshi yayi yana ta kallon fuskanta yanda take murmushi saiya kara mata kyau, jin karan wayanshi yasa ya ajiye hotan tare da d’aukan wayan, limam ya gani da sauri ya danna tare da d’auka, ban San mai limam yace mishi ba naji yace OK gani nan zuwa, tashi yayi tare da shiga toilet yayi wanka Jim kad’an sai gashi ya fito, shiryawa yayi cikin wata shadda Mai ruwan sky blue ba karamin kyau yayi yasa hula ya fita domin gidan sarauta Indai zaka wajan Mai martaba ko Yarima dondole sai mutum yasa hula, fita yayi dan zuwa wajan limam.
Koda Yarima ya karasa suka gaisa da limam cikin girmamawa.
Limam gyaran murya yayi tare da fad’in Nakira ka kaman yanda nace zan nemeka.
Yarima yace hakane Allah gafarta Malam.
Limam yace akan maganan da mukayi dakai kwanaki akan yarinyar daka fad’amin, Nayi istahara naga akwai alherai da dama a tare da ita, sai dai abunda ban gane ba shine akwai wani boyayyan abu a tare da ita wanda in ba’ai wasa ba zai iya hana ka samunta, inaso ka dage da addu’a akan zabi mafi alkhairi.