BARIKI NA FITO 1 & 2
Bariki dariya tayi can kuma tayi shuru tace gobe alhamis jibi jumma’a alh madu zai zo jibi, gobe Ya kamata inga Yarima, Tana shiga d’akinta ta doka ma habib kira tare da fad’in kawata zo d’akina dan Allah tare da kashe wayan.
Ba’a wani dad’e ba saiga habib yazo yana fad’in lafiya wannan kiran kaman na kashe miki wani.
Bariki tsaki tayi tare da fad’in kawata kina da matsala
Habib tabe baki yayi tare da fad’in tsaka ma da tayi Allah tsine Mata yayi.
Bariki tace Ka dai ji dashi.
Tashi yayi tare da ri’ke kugu yace bariki Wlh kina kaini bango zan miki tujara a cikin d’akin nan, yana maganan ne tare da hararan bariki
Bariki tace sorry kawata zauna kiji abunda yasa na kiraki,
Zama yyi tare da fad’in wlh bariki Kar ki bari in miki tujara dan banda mutunci, akan wani dalili zaki dinga had’ani da y’an maza Ina mace na.
Bariki tace Kedai baki da hakuri
Yace zawo ne ni.
Tace ni bari kiji kiran da nayi miki akan maganan Yarima ne, ina son gobe mu had’u a wani Gida zamu hadu?
Habib yace ah Allah sarki kice dan mutunci, karki damu kawai goben ki bashi dama zan shirya komai
Tace an gama, message tayi ma Yarima tare da fad’in gobe insha Allah zamu hadu da yamma.
Habib yace bariki harna kosa goben yayi ki ganshi kiga yanda ya had’u kai inama ni yace yake so Aida na aureshi da yaga yanda ake zuba soyayya????????
Bariki dariya take Sosai har tanayin kasa dan dariya…… ????????????????????
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
*PAGE 14*
PLZ KUYI HAKURI DA TYPING ERROR, BANI DA LOKACIN EDITING, NASAN KUNA GANEWA
Ganin bariki na dariya.
Habib yace miye kike dariya haka? Naga kin samu dama kina son wasa dashi, wlh dani yace yana So da yaga yanda ake zuba soyayya, baki ga yanda ya had’u ba, kai akwai y’an maza kyawawa fah, kaman yanda muma muke jerin kyawawan Mata.
Bariki taci dariya Sosai, sannan ta tsagaita tace yanzu miye Abun yi?
Yace kawai ki zama ready goben, zamu wani Gida saiki fito daka cikin gidan kaman nan ne gidan y’an uwan naku.
Bariki dariya ta saki tare da fad’in Kai kawata kanki naja fah Sosai.
Habib yace Toh an fad’a miki nita wasa ce, wai mai kika kawo mana ne? Yunwa nake ji wlh.
Bariki tace tea nake son sha, Bari in had’a mana.
Habib tabe baki yayi tare da fad’in sai kace wasu ‘konannu, Musha tea da wannan daran, bada niba sa lallan kaza.
Bariki tace toh mai kake so? Ni tea din kawai garan indomie nama ta Kare.
Habib yace tashi za kiyi muje wajan mai shayi ya soya mana indomie da kwai.
Tace Kai kawata kije ki siyo mana Wlh na gaji, ni zan fara shan tea Kafin ki kawo indomie din dan Wlh bazan iya jira ba, wani irin shegen yunwa nake ji, kaman hanji na zasu fita.
Tashi habib yayi tare da fad’in kyaji dashi yanzu inda wani tsohon kwarto zai kiraki ai nasan tashi za kiyi ki tafi.
Bariki mi’ka ma habib kud’i tayi tare da fad’in zani mana da gudu Indai ayabarsa tamin, ki siyo mana da kaza.
Habib yace oh Ina mace santaleliyan budurwa zani siyan nama, salan kisa su kwa’kuleni.
Bariki tashi tayi tasa ruwa a heater tare da fad’in dan Allah kije ki dawo.
Fita yayi yana fad’in sabon salon iskanci, sai kace Nina aikeki kije tama d’id’i.
Bariki had’a tea tayi tana sha, jin karan wayanta yasa ta d’auka taga Yarima ne, da sauri ta danna tare da sawa a kunne.
Sallama tayi cikin sanyin murya.
Amsawa yayi tare da fad’in Barka da dare, hope baki Fara bacci ba na tada ki?
Tace a’a bacci tun yanzu, karatu ma nakeyi yanzu Ina shirin in ajiye qur’ani sai ga kiranka.
Yarima murmushi yayi cikin jin dad’i domin duk Sanda zaiyi magana da Zainab dinshi wato bariki sai yaji tana abun islamiya abun addini dai, yace yanzu naga message dinki, so gobe around 2 zaki ganni.
Tace Allah uban giji ya nuna mana goben lafiya.
Ya amsa da Ameen, tare da fad’in ta ina gidan yake?
Tace karka damu Idan kazo bakin titi ka kirani zansa habib ya kawo ku dan ban san yanda zan maka kwatance ba.
Yace ok babu damuwa gimbiya Zainab
Dariya tayi tace Yarima niba Mai sarauta ba amma kaban sarauta.
Yace mijinki ai mai sarauta ne, Kinga Kema sarauniya ce koh?
Uhm kawai tace alaman taji kunya….. Nocking aka fara Mata,
Yarima jin kaman ana nocking yace ba’ki kikai cikin daren nan?
Tace ba’ki kuma ina tunanin mum ce, take nocking Bari in gani.
Yarima yace ok take care tare da kashe wayan.
Tashi tayi ta bud’e kofar.
Habib yace bud’e kofar ma sai an batamin lokaci?
Tsaki tayi tare da fad’in waya nake kin zo kina buga kofa kaman nayi sata.
Habib tabe baki yayi tare da ajiye ledan kayan daya siyo, yace kyaji dashi, bud’e ledan yayi ya d’auko indomie ya fara ci.
Ita kam bariki Naman ta d’auka tana ci tare da fad’in Yarima na yanzu ya kira.
Habib dariya yayi yace amma bariki Keko y’ar duniya har wani suna kika samai Wai Yarima na.
Bariki tace eh mana Yarima na Mai son ustaziya
Dariya suka saki Sosai
Sannan habib yace ai Wlh har na kosa goben yayi ku had’u ku tattauna inga yanda zata kaya.
Bariki murmushi tayi tare da fad’in Nasan muddin na fad’a Mai gskya koni wacece Zaima gudu ne, dan bazan bari ma muyi nisa ba.
Habib yace amma dai Keko anyi mara wayau, akan wani dalili zaki fad’a Mai koke wacece?
Bariki tace kawata ban son in cutar dashi in…..
Habib ya Katse bariki da fad’in ya isa dan Allah ni Kinga saida safe kiyi duk abunda ya dace tashi yayi ya fita yana gantsaro duwawu.
Bariki rufe kofarta tayi tare da fad’in shege kana son in cuta mutum, kai ai saika aureshi, Bayan ta gama abunda take ta kwanta abunta.
Hjy Umaima tunda ta shiga d’aki ta tsure Sosai dakyar nutsuwa ta dawo mata tare da fad’in yau na d’auko ruwan dafa kaina, oh Allah ya soni na tsallake Rijiya da baya, wannan kyan nata ai dole aljanu su shigeta, kasa fita tayi dan tsoro ranan ko bacci ta kasa, tana tsaye wajan window da safe taga bariki ta fita, tana ganin haka ta kira security tace karsu bari yarinyar nan data fita yanzu ta kara shigowa.
Suka amsa da ok ma.
Kiran Hjy habiba tayi tare da fad’in kawata jiya naga bala’i yarinyar nan dana tawo da ita ashe aljanu gareta, baki ga yanda tamin ba Wlh nayi mugun tsorata.
Hjy habiba tace Innalillahi, ya kuka kaya?
Labarin abunda ya faru hjy Umaima ta bata.
Hjy habiba tace Allah ya kyauta ga yarinya kyakyawa, toh amma sai naga kaman y’ar hannu ce, kawai dai Nasan an sami matsala ne aljanunta suka tashi, amma bari in tambayi daughter na, tashi tayi ta nufi falo inda haulat ke zaune tana breakfast, tace haulat Wai bariki kawarki tana da aljanu ne?
Haulat dariya tayi tare da fad’in injiwa?
Hjy habiba ta bata Labarin abunda hjy Umaima ta fad’a mata.
Haulat taci dariya Sosai sannan tace bariki ko y’ar iska, toh Wlh bata da komai, nidai Ina tunanin bata lesbians dan zama na da ita ban taba ganinta tayi ba, ita kawai barta da bin mazanta.
Hjy habiba tace kenan tayi ma Hjy Umaima hakan ne danta kwaci kanta, Allah ya kyauta itama Hjy Umaima ta cika jaraban tsiya Wlh tana da y’an mata kala Kala, amma daka taga wasu ta dinga rawan jiki kenan Allah ya kara mata Kinga aita had’u da cikakkiyar y’ar bariki tayi maganinta ta rage zari ai yanzu….