BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Muryanta da yaji tana fad’in plz ka sake min hannu shine ya dawo dashi daka duniyar tunanin daya fad’a, ido ya bud’e tare da d’auko wani Leda, ciro wani karamin kwali yayi anyi raping dinshi, bud’ewa yayi ya d’auko wani diamond ring, saka mata yayi a hannunta das ya shige kaman an gwada, yace this ring is my heart, ina fatan zaki ri’ke min shi dakyau?

Murmushi tayi tare da saka hannunta a kafanta tana kallon zoban mai shegen kyau Wanda Yarima Aliyu ya kira da zuciyar shi ce.

Ganin idonta nakan zoban tana kallo kobai kara cewa komai ba yasan ya samu shiga.

A hankali tace Yarima wannan ring din bai dace dani ba, hawaye ne ya fara zuban Mata Sosai

Ganin haka hankalin Yarima Aliyu ya tashi Sosai tare da fad’in Zainab mai yasa kika fad’i haka?

Cikin kuka tace Yarima ni dakai bamu dace ba baka dace dani ba kafi karfina ba Irina ta dace dakai ba nasan in…..

Dakatar da ita yayi tare da fad’in ya isa haka zainab. Tissue ya d’auko ya fara goge mata hawayen da takeyi yace kalla yanda kika batamin Fuskanki da hawaye, yana maganan ne yana kallon ta, yace Zainab shi so babu ruwanshi dako Waye mutum, Zainab ina sonki dagaske bada wasa ba, tun Kafin in ganki nake sonki tun cikin mafarki na, bana tunanin akwai abunda zai saka in daina sonki, zainab yau had’uwa na dake da nayi na fuskanci abubuwa da dama, kina da addini kin fito gidan mutunci iya wannan ya isheni, zainab duk irin yanda nake son matar da zan aura ta kasance kina dashi, ina da kishin abunda nake so, ina son mace Mai suturta jikinta Wanda ke gashi ko a cikin mafarki na da hijab kike zuwa har a zahiri ma da hijab na ganki, wannan abubuwan ya isa duk wani namiji yayi burin samunki a matsayin matar auransa kuma Uwar y’ay’ansa, I don’t care ko daka ina kika fito ke nake so bawai wani abuba, inda kin San yanda nake jinki a raina da baki tunanin wani abuba so plz karki kara fad’in ni dake bamu dace ba, d’an matsawa yayi kusa da ita yace kalleni kiga bamu dace ba? Ganin taki d’ago kai yasa yayi murmushi yace ban taba ganin couple din da suka dace ba kaman ni dake.

Bata san lokacin da dariya ya sakar mata ba domin maganan shi ya bata dariya.

Ganin tayi dariya shima yayi murmushi tare da fad’in yauwa na saki dariya am happy now.

Murmushi tayi tare da fad’in babu kyau son Kai, ai bakai zaka fad’a ba wani ne zai fad’a yace mun dace ko bamu dace ba.

Murmushi yayi tare da fad’in Toh Kema ya akayi kika san bamu dace ba?

Kanta na kasa tace saboda naga haka dinne.

Shima yace nima na fad’i hakan ne dan Ina ganin mun dace

Murmushi tayi

Sunanta ya kira yace Zainab Ina son fad’a miki magana Mai muhimmanci.

Gabanta taji ya fad’i, amma saita daure tace inaji.

Yace biki na ranan Friday din nan rana ita yau.

Dam taji gabanta ya fad’i Wanda bata san dalili ba tare da kallonshi da sauri ganin Sun had’a ido domin shima ita yake kallo yasa tayi kasa dakai.

Yace Zainab iyaye na sun sha bani mata amma naki yarda burina kullum in ganki dan muyi aure sai yasa bana yarda da duk wani zabin iyayena, mahaifina ya gaji da zama na haka babu mata, musamman daya kasance nine d’ansa namiji guda d’aya yana bukatan ganin jikansa, sai yasa ya yanke bani auran y’ar sarkin katsina gimbiya zinatu, bayan na amince da auran domin ko ban amince ba dole Ayi tunda mahaifina bada wasa yake ba, kawai sai na ganki keda wancan guy din ya nuna mata habib dake waje yana hararan driver dinshi, Zainab na fad’a miki wannan maganan ne saboda ina sonki ban son boye miki komai dake tare dani , ina son Kema ki fad’amin abunda kike ji a game dani.

Bariki kanta na kasa tunda Yarima ya Mata maganan auranshi rana ita yau, ta shiga damuwa wanda ta rasa dalili, ganin yayi shuru ita yake saurara yasa tace ina son ka bani lokaci kad’an inyi tunani akai

Yace Zainab when no one’s around but you and me. A lokacin zaki iya tunanin mai kike ji a kaina. Kiran sunanta yayi cikin wani irin murya

d’ago dakai tayi suka had’a ido da sauri ta sauke idonta ta rasa mai yasa bata iya kallonshi gabanta faduwa yakeyi Sosai, jin hannunshi tayi akan nata…..

Yace my princess zan baki lokaci amma fah bamai yawa ba, kwana biyu kawai na baki kiyi tunani akai na Zanzo inji amsa daka gareki.

Kasa motsi tayi sai gabanta dake faman dukan uku uku, Mai yasa na kasa fad’a mishi abunda Nayi niya Mai yasa bana jinshi kaman sauran mazan da nake hulda dasu? Mai yasa ya banbanta dasu? Ga hannuna a ri’ke da nashi amma na kasa yin abunda nayi niya ido ta lumshe domin ta rasa amsan wannan tambayan nata .

Ganin tayi shuru yasa yace my princess karki manta kwana biyu na baki Zanzo inji daka gareki jibi kenan, sannan Saturday shine ranan waliman ki koh?

Kai ta d’aga alaman eh.

Yace Allah ya nuna mana ranan, jin kiran sallah la’asar yasa yace bari muyi sallah sai mu kama hanya.

Tace toh Bari a kawo maka ruwa, bud’e motar tayi ta fita cikin gidan ta shiga da sauri habib yabi bayanta..

Tana ganin habib tace yauwa Kai ma Yarima ruwa yayi alwala, amsa yayi ya fita tare da kaima yarima ruwan

Sannan ya koma ciki, inda ya sami bariki na sallah itama, zama yayi yana jira ta idar, Bayan ta gama.

Habib yace ya kukayi?

tace Kai baka je masallacin ba, d’aure fuska yayi tare da fad’in in banda rashin mutunci kin taba ganin mace a masallaci? Gskya banso.

Bariki tace Allah ya shirya, jin wayanta yayi kara alaman sa’ko ya shigo yasa ta duba taga Yarima ne yayi mata message come out my princess murmushi tayi tare da tashi ta d’auko jakarta ta fesa turare sannan ta fita, motar ta bud’e ta shiga inda ta ganshi zaune yana waya taji yana fad’in lil yanzu zan dawo nace kuyi komai keda usman Kafin in dawo, kashe wayan yayi sannan ya kalli bariki

Yace my princess zan tafi, sai nake ji kaman mu tafi tare.

Murmushi tayi tare da fad’in in lokacin hakan yayi zamu….. Da sauri tayi shuru dan maganan da taji tana niyan fad’a

Ganin tayi shuru yasa Yarima Aliyu yayi murmushi tare da fad’in ina ji karasa abunda kikai niya.

Hannunta tasa a fuska alaman jin kunya

Yarima dariya yayi Sosai abunda bai taba yima wani ko Wata ba sai yau, d’auko wani card yayi ya bata tare da fad’in plz in kin shiga Gida ki turomin Abokina habib

Tace toh har zata fita ya kira sunanta waigowa tayi

Yace Zainab Waye habib a wajan ki?

Tace d’an uwana nane yaron kanwar mama nane.

Yarima yace ok na gane I love you

Dariya tayi tare da fita da sauri tayi cikin gida.

Ko minti biyu batayi da shiga ba saiga habib yazo, yarima wani Leda ya bashi babba tare da fad’in kaba ma my princess wannan, wata karaman Leda ya d’auko tare da bama habib yace ga naka.

Habib amsa yayi yana ta godiya sannan ya fita

Su Yarima hanya suka kama yana kallon gidan da zainab dinshi take har suka wuce.

Koda habib ya shiga gida bama bariki sa’kon da Yarima ya bata yayi, bud’e nashi yayi yaga agogo Mai shegen tsada da kud’i dubu d’ari biyu ihu ya saki tare da fad’in oh wannan koh dan arziki. Ganin bariki tayi shuru kaman mai tunani yasa yace bariki lafiya kuwa?

Bariki tayi firgit tare da kallon habib tace ina son fad’a mishi gaskiyan koni wacece amma na kasa, mai yasa baiyi min kaman yanda nake ganin sauran maza ba, ya banbanta dasu, na rasa gane mai nake ji a kansa, na tsinta kaina da tsoran fad’a mishi koni wacece, Nasan zai tsaneni…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button