BARIKI NA FITO 1 & 2
Habib yace bariki kin kamu da sonshi
Kai ta girgiza alaman a’a tace ba sonshi nake ba, ina mamakin kasa gaya mishi abunda Nayi niya ne Bayan daka ni sai shi, tunda na fito bariki ban taba had’uwa da mutum Wanda naji ya cika min ido ba sai yau, Indai bazan iya gaya mishi koni wacece ba ya zama dole inyi nesa dashi Kar in kara Bari mu had’u……
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
TO ALL MY FANS INA MATUKAR JIN DAD’IN COMMENTS DINKU SOSAI DA SOSAI ALLAH YABAR KAUNA MASU TURU MESSAGE SUCE AITA TURAWA HAR YAZO INDA NAKE INA GANIN SA’KON KU INA MATUKAR YINKU IRIN SOSAI DIN NAN
*PAGE 16*
Habib kallonta yayi yace bariki Wlh son Yarima kike.
Bariki hararan shi tayi tare da fad’in tunda ni na fad’a haka koh? Kawai daka had’uwa na dashi sai in fara sonshi.
Habib tabe baki yayi tare da fad’in, toh mai yasa kike cewa zaki gujeshi saboda kin kasa fad’a Mai gaskiya?
Bariki shuru tayi tana nazari….
Habib ya Katseta tare da fad’in in bakya sonshi Mai yasa kike tsoran fad’a mishi gaskiya? Saboda kina tsoran ki rasa shi koh?
Da sauri ta kalli habib
Murmushi habib yayi tare da fad’in Kinji na fad’a miki abunda ke ranki koh? Toh Bari kiji gwara da baki fad’a mishi koke wacece ba, domin na tabbata dan gidan sarauta bazai auri karuwa ba, balle ke da kikai suna cikin wannan anguwan
Bariki tace nace miki auranshi zanyi ko cewa nayi ina sonshi? Dan Allah tashi ni mubar wannan gidan in koma d’aki na Ina bukatan in huta.
Habib dariya yayi tare da d’aukan Mata ledan da Yarima ya bata, yace duk dai boye boyen mai ciki dole wata rana ya fito, fita yayi tabi bayanshi har d’akinta habib yakai mata kayan sannan ya fita tare da fad’in ina da ba’ko zanje in Kai mishi yarinya sai na dawo nazo mu tattauna.
Bariki tace toh tare da rufe kofarta..
Habib yace bariki ki gama Munafuncin ki, Danni tuni na baro jirgin soyayya ta kama ki, yana tafiya yana magana tare da bokare duwawu Wai shi a dole yana rangwada.
Bariki kwanciya tayi tare da lumshe ido duk abunda ya faru ita da Yarima Aliyu yake dawo mata, da sauri ta bud’e ido tare da tashi d’auko card din daya bata tayi ta bud’e wanda yake ta faman kamshi Fara karantawa tayi kaman haka……..
I have liked many but loved very few. Yet no-one has been as sweet as U. I would stand and wait in the worlds longest queue. Just for the pleasure of a moment with U.
Ido ta lumshe Bayan ta gama karantawa a hankali ta furta so romantic, ledan daya bama habib ya bata, ta Fara bud’ewa, kwalin waya ta farayin karo dashi iPhone Xmas, sai su turare masu tsadan gaske kuma duk Arabian perfumes ne, a kalla sun Kai Kala goma sha biyar, banda su body spray, murmushi tayi domin a duniya tana son kamshi, d’aukan kwalin wayan tayi ta bud’e tare da sawa a caji, ba karamin jin dad’in kyautar tayi ba, wannan ne karo na farko da namiji ya bata kyauta harta yaba kuma taji dad’i Sosai, d’aukan wayanta tayi tare da shiga wajan message ta Fara rubutu kaman haka….
Naga sa'ko nagode Sosai ban San wani irin godiya zanyi ba, Allah ya biyaka da gidan Aljanna, amma wannan kayan kaman sun min yawa Yarima na.
Tunani tayi ta tura mai ko Karta tura, tayi wajan minti biyar tana tunani sannan ta tura mai.
Harga Allah ansha yi mata kyauta Kala Kala, toh mai yasa bata jin dad’i irin haka sai wanda Yarima ya Mata? Ido ta lumshe tare da fad’in kodan shi ba irin sauran samari na bane? Kai ta d’aga alaman hakane shine wanda ya fara min kyauta tunda na fito bariki ba tare daya nuna yana son wani abu daka gareni ba. Murmushi take tayi tuna firanta dashi ga kamshin turarenshi da har yanzu yana hancinta yaki tafiya, lokaci d’aya kuma ta dan gimtse fuska data tuna yace Mata auranshi rana ita yau, tabbas ya kamata inyi gaggawan rabuwa dashi tun Kafin ya zaman min matsala a cikin rayuwa na, tashi tayi ta d’auki wayanta tare da dannawa taga har yayi mata reply da cewa….
My princess I really miss you, komai na baki u deserve it, so ban son daka yau ki karamin godiya, love you so much, I will call you when I arrived home, take care.
Ido ta lumshe lokaci d’aya kuma ta bud’e idon tare da kashe wayanta…. Tace Yarima bazan cuceka ba,nasan da kyakyawan zuciya kazo min, rayuwa ta abun kyamace ga duk wani namiji mai kishin kanshi, na tabbata rabuwa dakai shine Alheri a tare dani, domin bazan iya fad’a maka wacece ni ba, infact ma babu tsarin aure a rayuwa na, Indai har zanyi tunanin haka burina bazai cika ba, bazan so hakan ba kuma wani hawaye mai zafi ya zubo mata, lokaci d’aya tasa hannu ta goge tare da fad’in Yarima na Barka daka yau bazan kara sauraranka ba, dan had’uwa na dakai na rana d’aya yana kokarin canza min tunani…..
Yarima Aliyu ya karasa gida gab da magrib, bai shiga ciki ba, masallaci ya shiga inda yayi alwala dan yana jira a kira sallah sai ya shiga gaba d’aya, har sai da akayi sallah isha’i sannan ya shiga gida, direct gefen shi ya shiga ya fad’a toilet, shower ya saki ya dad’e ruwa yana dukanshi ba komai yake tunani ba saina gimbiyarsa ya dad’e a haka Kafin ya fito, jallabiya ya saka, dan shirin kwanciya, falo ya nufa inda yaga an jera Mai abincin dinner a table, zama yayi kuyangi har biyar suka zo domin zuba mai abinci, zuba mai abinci sukayi suka gama, sannan sukai dan nesa dashi, bai wani ci da yawa ba ya tashi yabar wajan domin yana bukatar jin muryan princess dinshi…..
Yana shiga d’aki ya doka Mata kira, amma sai me?
Yaji ance number din a kashe, abun mamaki ya bashi dan haka ya kara kira amma switch off, d’an shuru yayi alaman damuwa, tare da fad’in maiya sami wayanta? Kiran Layin habib yayi
Habib d’auka yayi tare da fad’in Allah ya taimaki Yarima.
Yarima Aliyu amsawa yayi da ngd, maiya sami wayan zainab I try her line but switch off.
Habib yace Wlh Yarima na fita ,amma anjima kad’an zan koma, ina tunanin babu wuta ne, hala bata da caji.
Yarima yace ok bari in kira a kawo muku yana fad’in haka ya kashe wayan.
Habib tashi yayi daka inda yake domin ya koma yaga lafiya bariki ta kashe waya dan yasan haka kawai ta kashe badan bata da caji ba, sallama yayi ma mutumin da yakai ma mata har biyu zai kwanta dasu, d’auko kud’i yayi yaba habib sannan yayi gaba.
Yarima Aliyu shugaban Nepa na kaduna state ya kira, bayan ya d’auka sun gaisa da Yarima Aliyu, yarima yace Ina son a kaina maraban jos wuta, yanzu akwai….. Sai kuma yayi shuru…..
Shugaban Nepa yace ranka ya dad’e ai suna da wuta, banyi ko minti biyar da gama waya da wani dan uwana dake Jaji ba, kuma duk hanyar su d’aya tun daka Barakallahu birnin yaro har zuwa jaji.
Yarima Aliyu yace ok nagode tare da kashe wayan, d’an shuru yayi cikin mugun damuwa, maiya sami wayanta? Kara kiran layin habib yayi.
Habib ya d’auka tare da fad’in Allah ya taimaki Yarima, ina hanya na kusa zuwa Gida.
Yarima yace ok am worried Sosai na kira ance akwai wuta, na damu da naji wayanta a kashe.
Habib yace Ina zuwa zan kira in bata.
Amsawa Yarima yayi da fad’in OK tare da kashe wayan.
Yarima Aliyu shuru yayi yana tunani wai yau shine yake kira akan mace, dan kawai ya jita shuru, ido ya lumshe, yana tuna yanda take magana cikin nutsuwa, tunawa yayi sanda tace mishi Yarima na. Bai san lokacin daya saki murmushi ba…….
Habib Bayan ya karasa gida, direct d’akin bariki yayi, nocking ya fara mata