BARIKI NA FITO 1 & 2

Amsawa yayi tare da fad’in morning stolen princess.
Tace stolen princess? Tayi maganan ne kaman zatai kuka.
Murmushi yayi tare da fad’in yes u stole my heart… Nd u don’t want to give me urs
Bata san lokacin data sake wani murmushi ba tare da lumshe ido….
Yace Zainab u r d first girl dana ke zama da ita inyi fira haka, nd Kece mace ta farko dana Fara rubuta ma Text messages in my life, Zainab what I knw iz dat sonki yasa nake miki haka, and I can’t do anything just to have you.
Bariki jin maganan Yarima take har cikin ranta da duka gangan jikinta, takan rasa mai Yarima yake dashi da yafi sauran samarinta, ita dai tasan bawai tana sonshi bane, amma shine kadai yake magana da ita taji bata son ya Bari sannan takan sami nutsuwa Idan suna waya, takan rasa mai yasa ko wace kalma Indai ya fito daka bakinshi take jin dadinta ba, ta rasa dalilin hakan ga wani irin kwarjini da yake mata Sosai……
Katse mata tunani yayi da fad’in my princess ya ake ciki da maganan saukan ki? Mai kike son shiryawa?
Gabanta taji ya fad’i, domin tama manta data mishi karyan zatai sauka, tace Yarima babu abunda nake shirin yi, kawai ana sallaman mu a islamiyya Indai na amshi shada ta, shaidan tayi sauka kenan, shikenan.
Yace no Ina son kiyi wani abu, karki manta koke matar Waye, I knw ur friends zasu zo miki gida, so zaki shirya musu Walima.
Tace Yarima bani da burin inyi h……
Yace enough my dear, gobe in nazo zami arranging, so amma ina so kisa a ranki dole zaki Walima domin a tayaki murna, al’qur’ani fah kika haddace, ba karamin abu bane, ake murnan birthday ba balle wannan mai dalili.
Murmushi tayi tare da fad’in hakane Yarima.
Yace yau baki ce Yarima na bah?
Tace uhm sai kazo zance
Yace shikenan babu damuwa Ina zuwa shi zaki fara fad’a min….. Dan shuru yayi sannan yace my princess Mai kike ji a kaina?
Shuru tayi ba tare da tace komai ba domin ta fad’a duniyar tunani, Yarima bazan iya cewa Ina jin wani abu a game dakai ba, nd kuma bazan iya cewa bana ji ba, dan a halin da nake yanzu Ina cikin rudani a game dakai…..
Katse mata tunani yayi da fad’in tell me dear.
A hankali tace Yarima our promise is 2moro koka manta ne? Gobe kace ka bani in fad’a maka mai nake ji.
Murmushi yayi tare da fad’in u r right, hakane, Bari nayi hakuri zuwa goben.
Murmushi tayi tare da fad’in Allah ya kaimu.
Ya amsa da Ameen, tare da fad’in bari inje inga mum da Abba, I will call you later.
Tace OK ka gaida mun su.
Yace insha Allah tare da kashe wayan.
Bariki kallon wayan tai tayi domin ta rasa mai yasa Yarima Aliyu ya banbanta da sauran mazan data Sani, shi d’aya ne yake mata abu taji dad’i Sosai, sannan shine mutum na farko tunda ta fito bariki wanda tayi ma karya, ido ta lumshe tare da tambayan kanta Mai yasa? Mai yasa kodan shi bada iskanci yake nema na ba?
Yarima Aliyu Bayan ya kashe wayan tashi yayi ya nufi gefen mum dinshi, inda ya sameta tana waya da sister dinshi rukayya dake aure a garin katsina, yaji mum Tana fad’in rukayya tun gobe zaku tawo, mai yakon ku bari saura kwana uku biki? Ban San mai take fad’ama mum dinba naji tace eh hakane bikin yarima na guda, Allah ya kawo ku lfya.
Bayan mum ta kashe waya ta kalli Yarima da yake ta wani cin magani.
Tace lafiya kuwa Yarima?
Yace mum kin tuna alkawarin da kika min?
Tace name fah?
Yace kince Indai na sami wacce nake so zaki tsayamin?
Mum tace ban manta ba Ina sane yarinyar an yarda tayi aure ne yanzu?
Yace eh mum Ina son yarinya ya……
Mum tace ya isa Yarima ban son shirme, ai sai kayi hakuri har a gama bikin ka sai Ayi wancan maganan, Indai an bincika yarinyar tana da hali Mai Kyau tunda inda sun yarda tun Farko aida da ita za’ayi.
Yace mum halinta yana da kyau domin ranan Saturday dinnan ma zata haddace al’qur’ani Mai girma.
Mum tace Masha Allah, hakan bada kyau, ashe hafiza Yarima na zai auro kai Masha Allah naji dad’i Sosai sai dai Ayi fatan Allah yasa karatun nata ya amfani al’umman musulmai baki d’aya.
Ya amsa da Ameen.
Sannan mum din tace Indai kana son inyi maganan auranka da ita, sai ka bada hadin kai wajan wannan bikin naka, kasa hannu Ayi komai dakai, ni kuma Na maka alkawari bayan bikin ka da wani lokaci zansa Ayi bincike Indai babu matsala sai ayi komai.
Hugging mum dinshi yayi tare da fad’in babu ma matsala insha Allah my mum, Nasan zaki yima Mai martaba bayani.
Murmushi tayi tace insha Allah, kai dai kawai ka saki jiki Ayi komai dakai…..
murmushi Yarima yayi domin yasan tunda mum tace haka kaman ya gama samun Zainab dinshi ne, dan yasan koda anyi bincike bata da wani mugun hali, yarinyar dako magana kunyan yinta takeyi…..
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
*PAGE 18*
GAISUWA GA DUKA MASOYA NOVEL DIN BARIKI NA FITO, HARGA ALLAH BANYI NIYAN CIGABA DA RUBUTA WANNAN LABARIN BA, BUT A RAYUWA YAU IDAN AKACE MAKA ALLAH DA ANNABI WLH AN GAMA DAKAI, YAU KODA MARINKA MUTUM YAYI YACE DAN ALLAH YA KURI KASAN CUTANKA YAYI AMMA TUNDA YACE ALLAH TOH YA KAMATA KA HAKURA, ALHMDLH DA FARKO RAINA YA BACI SOSAI AKAN ABUNDA WASU TSIRARUN MUTANE SUKAMIN, BUT DAKA JIYA ZUWA YAU NA GANE CEWA MASOYA NOVEL DINA SUNFI MAK’IYANSHI YAWA, A YAU LARABA TABAWA RANAN SAMU NI MARYAM NA DAU D’AMARA WAJAN D’AUKAN ALKALAMINA WAJAN CI GABA DA RUBUTA MUKU LABARIN BARIKI NA FITO, KUMA INSHA ALLAH BAZAN TSAYA BA HAR SAI NA DIRE, INDAI INADA RAI DA LAFIYA, MASU ZAGINA KUMA KOFA A BUD’E TAKE DAN ALLAH KUCI GABA, BARIKI DAI YANZU NA FARA, DUK WANDA BAI MISHI BA ZAI IYA BARI KAMAN YANDA NA FAD’A TUN FARKO AM WARNING OOOO COZ DIS TYM BAZAN D’AUKI NONSENSE BA DOMIN DUK ABUNDA ZAKU FAD’A SAI NA RUBUTA BAZAN BARI BA EHEM????♀ SANNAN INA MAI BADA HAKURI YANZU BA KULLUM ZAN DINGA POSTING BA SABODA WANI DALILI NAWA BUT ZAN DINGA KOKARI INAYI INDAI NA SAMI LOKACI
Mum ta kalli Yarima da yake ta murmushi, itama murmushin tayi domin tasan d’an nata yayi nisa cikin son yarinyar da yake son aura, cikin ranta take wannan tunanin tace Allah ka bashi ikon yin adalci a tsakanin matayen nashi.
Tashi Yarima yayi tare da fad’in bari inje inga Usman lil sis tace yana ta nemana.
Mum tace ok ni kwana biyu Ina kake zuwa ne?
Yace mum inada wani abune da nake zuwayi yana maganan ne tare da Sosa Kai.
Murmushi mum tayi.
Fita Yarima yayi direct wajan sister dinshi ya nufa Hafsat.
tana ganinshi ta tashi da sauri tana fad’in bros kasan fah komai saida taimakon ka zamu iya, amma kana ta share mu.
Yace lil mai kuke shiryawa? tunda gani nazo ai komai ya wuce
Tace bros event din da za’ayi mun shirya komai harta kayan da bride din zata saka da wanda kai zaka saka duk an shirya.
Yace taya kukai haka?
Dariya tayi tare da fad’in ai kace mu shirya komai, tunda ka bamu power ai kasan zanyi maka komai my bros tare da saka hannunta a wuyanshi tana ja.
Dariya yayi tare da fad’in Kar kiji min ciwo plz, gobe zanje wajan princess dita.
Tace katsina zaka gobe kuma? D’aga gira tayi tare da fad’in bros bazaka iya hakuri har a kawo ta bah?