BARIKI NA FITO 1 & 2
Yace Toh maiya sami idonki naga kaman sun kumbura? Ko kuma kikayi?
Tace Yarima wani mafarki nayi Wanda Yaban tsoro cikin mafarkin Wai nida kai muna fad’a har kace bazaka aureni ba saboda an fad’a maka mugayen Abu a Kai na kum……..
Hannunta ya ri’ke Wanda yasa tayi shuru daka abunda tayi niyan fad’a, yace my princess bana tunanin akwai abunda wani zaice a kanki in fasa auranki Abu d’aya za kiyi wanda ko a masarautar mu babban laifi ne kuma yana d’aya daka cikin laifin Wanda Idan ka aikata dole kabar masarautar shine zina, wannan abun ne kad’ai zaki aikata na fasa auranki domin ni namiji ne mai kishi Sosai ina da kishin abunda nake so, wanda na tabbata ke bakya d’aya daka cikin masu aikata alfasha sai yasa a kullum nake kara sonki, ban kasance mazina ciba sai yasa a kullum nake ro’kan Allah ya bani mace tagari wacce ta tsare kanta daka rudin zamani
Wani hawaye ne ya silalo daka fuskan bariki wanda bata san sun zubo ba …..
Jin hannun Yarima tayi akan fuskanta yana share mata hawayen tare da fad’in baby maiya faru?? Ki daina wani tunani ina tare dake nazo jin amsa kona karbu Ashe an dad’e dayin accepting dina.
Murmushi tayi cikin sanyin jiki ba tare da tace komai ba, domin gaba d’aya maganan Yarima yasa ta fita hayyacinta tare da neman hanyan mafita, tabbas Idan Yarima yasan ita wacece bazai taba auranta ba, kenan mafarkinta gaskiya ne?…..
Katse mata tunani yayi da fad’in my princess tell me Mai kike ji a kaina?
Murmushi tayi tare da fad’in ai kace ka sami amsa
Yace eh but Ina son in kara tabbatarwa
Tace Yarima tabbatarwa ya wuce yardan da nayi za muyi aure Tana maganan ne tana rufe fuska alaman kunya take ji
Matsawa yayi kusa da kunnenta ya fara mata magana cikin rad ‘a tare da fad’in I need my kiss…
Tana jin haka tayi saurin matsar da kunnenta Tana fad’in zan koma Gida
Murmushi yayi tare da fad’in yau babu inda zani har sai anyi min abunda nake so, sannan kema kina nan babu inda zaki
Tace Yarima ko gaisawa ba muyi ba.
Murmushi yayi dan yasan Tana son su canza zancen ne sai yasa tace basu gaisa ba , yace oh hakane fah bamu gaisa ba
Tace eh Ina wuni? Da fatan kazo lafiya
Murmushi yayi tare da fad’in lafiya qalau, toh mun gaisa yanzu koh?
Tace eh cikin murmushi
Yace Toh am waiting for it
Tace what???
Yace kiss
Ido ta lumshe ba tare da tace komai ba, wani irin son Yarima yake fusganta sai yau ta kara tabbatarwa da tana sonshi tunda ta ganshi taji wani irin sonshi na fusganta
Shima haka ta gefenshi wani irin sonta yake ji har cikin ranshi ji yake kaman ya tafi da ita ace yau mallakinshi ce da yafi kowa murna, daya nuna mata so Wanda bazata taba samun wanda zai Mata shiba, amma dai a kwana a tashi burinshi insha Allah zai ciki, ya tsara musu abubuwa da dama shida ita ya tanadar mata soyayya tsantsa Wanda zai nuna mata inya mallaketa
Bariki ido ta bud’e ta kalleshi ta gefen ido taga ita yake kallo, da sauri ta kara lumshe ido, tare da tunanin abubuwa da dama, lallai Idan Yarima yasan wacece ni Toh daka ranan na rasa shi, maiya kamata inyi? Hawaye ne ya silalo mata a fuska……
Janyota yayi jikinsa tare da share mata hawayen yace mai yake damunki ne yau my princess?
Tunda ya janyota jikinshi ya saka mata kanta a kirjinshi ta lumshe ido domin gaba d’aya jikinta ya mutu ga kamshin turarenshi dake dad’a tayar mata da hankali, yau ce rana ta farko da namiji ya Mata haka taji har tana sha’awa da sauri ta Fara kokarin Jan jikinta daka nashi amma saiya kara manneta dakyau
Ta gefen Yarima kam shima jinshi yake wani iri, ya rasa wani irin so yake mata, kwata kwata baya son ganinta cikin damuwa ko kad’an baya son yin nesa da ita akan dole yake tafiya ya barta, yau ne rana na farko daya kosa ayi bakinshi da gimbiya zinatu dan Ayi maganan auranshi da zainab dinshi….
Bariki ce ta katse shi da fad’in Yarima wayanka na wuta kaman ana kira.
D’aukan wayan yayi yaga gimbiya zinatu ce, murmushi yayi tare da d’auka har yanzu bariki na manne dashi yaki sakinta. Yace gimbiya Barka da yamma… Yana maganan ne yana Satan kallon bariki dake manne a jikinsa ban San mai gimbiya tace mishi ba naji yana fad’in saura kwana nawa a kawo ki kaman jibi ne koh? Tunda anan za’ayi komai…..
Bariki dake kwance a kirjinshi taja jikinta da karfi har wayan tayi kasa ta silale daka hannunshi, kallonta yake tayi yanda yaga ta murtuke fuska abun yaso ya bashi dariya amma saiya dake dama da biyu yayi hakan, wayan yake kokarin d’auka bariki kuma tana kokarin bud’e kofar, hannunta ya ri’ke Bayan ya d’auko wayan kashe wayan yayi gaba d’aya, ya kalli zainab dinshi yace Ina zaki?
Tace zani gida in d’auko Abu ne tunda naga kana waya
Yace Toh yanzu na gama
Tace ina zuwa yanzu zan dawo
Yace OK tare da sakar mata hannu,
Fita tayi tana shiga cikin gidan ta fashe da kuka, yanzu dan wacce zai aura ta kirashi nake wannan kishin shifa Idan yaji na bayar da mutunci na ga wasu mazan ya zaiyi? Kuka ta kuma saki Sosai tare da fargaban abunda zai faru in Yarima yaji wannan zancen…….
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
*PAGE 22*
Kuka tayi Mai isarta, sannan ta wanke fuskanta tare da shafa powder dan Kar Yarima ya gane, saida ta tsaya ta seta kanta sannan ta fita…..
Tunda ta fito yake kallon fuskanta wanda dama tunda ta shiga idonshi nakan kofar gidan, tun Kafin ta karaso ya gane tayi kuka domin idonta yayi ja, dan farar mace Indai tayi kuka sai an gane dan fuskanta zata canza tayi ja ja……
Isowarta ne yasa tunanin da yake ya kawar
Bayan ta bud’e motar ta shiga da sallama muryanta a dashe….
Amsawa yayi tare da fad’in my princess yau kwata kwata na rasa gane maike damunki? Mai yasa kikai kuka da kika shiga ciki?
Gabanta taji ya fad’i ya akai yasan nayi kuka toh kodai ya biyoni ciki ne kai Anya a’a Toh y……
Katse mata tunani yayi tare da kiran sunanta da zainab
Da sauri ta d’ago ta kalleshi dan tasan magana zai Mata Wanda yake bukatan hankalinta tunda ya kirata da sunanta….
Yace I don’t know why yau kaman you are not happy, plz Idan kina da wani matsala ko damuwa let me know, ban son kiji shakkan fad’amin wani abu da kike bukata ko kunya, plz tell me maike damunki?
Muryanta na rawa tace Yarima Ina son inyi maka wata tambaya, ina son Kuma ka bani amsa…
Murmushi yayi tare da fad’in go ahead….
Tace kasan al’amarin aure yana da abubuwa da dama, yau Idan akace mutum zaiyi aure sai ayita kushe shi, ko kuma azo ana ya’da Labarin karya akan mutum yan…..
Dakatar da ita yayi da fad’in enough my princess it seem like wannan mafarkin da kikayi yasa kike wannan maganan, na fad’a miki zina ne kawai zaki aikata in fasa aurenki….. Bayan haka banga abunda zaki aikata ba ince na fasa auranki ba, sannan ina so ki sani sonda nake miki ba Wanda wani zaizo ya fad’a magana akanki bane in yarda I trust you nasan bazaki taba bani kunya ba
A hankali tace in fah wani yazo yace maka ni karuwa ce ya Z……..