BARIKI NA FITO 1 & 2
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
*PAGE 23*
Kuka tayi Sosai lallai Yarima shine mai Sonta na gaskiya, duk namijin da zai maka hidima ba tare daya nemeka ba, shine masoyinka, mazan yanzu basa abu dan Allah sai dai in Sun miki Suma suna so kiyi musu, mata Kwadayi maza kuma shegen sha’awa, daka ya baki abu kin amsa in baice miki wani abuba toh gobe zaice dan ba’a banza yayi miki ba, wannan shi ake kira trade by barter, wani irin son Yarima yake kara shigarta, ido ta lumshe mai yasa na kasa fad’a ma Yarima gaskiya? Saboda ina tsoran in rasa shi, saboda ina sonshi….. D’aukan wayanta tayi da sauri ta kira Layin Yarima amma still switch off, d’an shuru tayi tana tunani kallon lokacin data kirashi tayi dazu taga wajan 39mnt, tace ya isa ace yakai gida yanzu coz daka kaduna zuwa Zaria 30mnt ne, kara kira tayi amma a kashe tayi mugun shiga damuwa, mai yasa Yarima ya kashe waya Bayan yasan zata kira, sannan yasan sa’kon daya tura mata dole hankalinta zai tashi, gashi na kira yaki d’auka daka karshe ya kashe waya….. A hankali ta furta Yarima plz ka kunna waya ina cikin damuwa….
Yarima Aliyu Bayan sun karasa direct masallaci yayi cikin sauri dan yin sallah isha’i, duk da sanda suka isa an idar da sallah din, direct gefenshi yayi toilet ya fad’a yayi wanka sannan ya fito yasa jallabiya, falo ya fita inda yaga an jera Mai abinci zama yayi kuyangi suka zo suka suba Mai sannan suka bar wajan, Fara ci yayi yana cikin cin abinci saiga usman d’an waziri ya shigo
Usman zama yayi kusa da Yarima yana fad’in Wai kwana biyu Ina kake zuwa ne haka?
Yarima baiko Kalli usman ba balle yasa ran samun amsa.
Usman bai damu da hakan da Yarima yayi mishi ba dan dama yasan hali, inda Sabo ya saba, ganin Yarima bazai yi magana ba yasa yaci gaba da fad’in Yarima ya kamata ka rage fita kasan Idan gimbiya tazo jibi maganan fita ya Kare sai kuma Bayan aure….
Yarima ajiye spoon din dake hannunshi yayi tare da fad’in akan wani dalili?
Usman yace domin haka shine al’adan masarautar
Yarima yace thank god al’ada ce ba addini ba, da za’a rufe mutum a hanashi fita like a prison person
Usman murmushi yayi tare da fad’in Yarima kasan wannan masarautar bata wasa da al’ada domin an dauketa da muhimmanci, kuma ina mai baka shawara daka bi wannan al’adan Indai bason ganin fushin Mai martaba kake ba
Yarima Aliyu tashi yayi tare da fad’in nifa ban son takura a Bari inji da wannan auran da ake kokarin cusa min mana haba kodan Anga nayi shuru
Usman yace shurun shine Alheri Yarima, kuma ina mai baka shawara daka girmama zabin da iyayenka suka maka, Indai kana son ganin farin cikin su, kuma kana son Kaga dakyau
Yarima Aliyu yace naji zaka iya tafiya
Usman yace Allah ya huci zuciyar Yarima, dama nazo ne akan kazo muje Kaga gefen ka, domin ance tunda aka fara aikin baka le ‘ka ba, ya kamata kazo muje ka gani in yayi maka
Yarima Aliyu yace basai Naje ba, komai akayi yayi dai dai
Usman yace Yarima Mai martaba da kanshi yayi min magana akan muje in kaika ka gani.
Jin umarnin mai martaba ne yasa Yarima fad’in muje
Fita sukayi har zuwa gefen da akama Yarima dan gajeren ginin gidan sama, tsarin ginin ya had’u falo suka fara shiga wanda yana da girma Sosai, kofofin da suka gani a falon suka bude bedroom ne guda biyu a k’asa da kuma kitchen da dinning area, sai sama kuma d’aki uku ne da falo d’aya, ko wani d’aki yana da girma Sosai gidan dai yayi kyau Sosai
Usman yace ya Kaga gidan ina fatan yayi maka kyau
Yarima yace babu laifi
Usman yace gobe za’a zuba kaya domin da mai martaba yaso Asa sarkin katsina yace abarshi domin shi zai saka komai, duk da Mai martaba ya nuna a barshi amma sarkin katsina yace yariga yasai komai, d’azu masu deco suka zo suka duba komai gobe zasu zo su saka kayan
Yarima bai ce komai ba sai waje da yayi…
Ganin haka usman ya bishi yana fad’in Yarima gaba d’aya kayan da zaka saka an kammala su, ranan da gimbiya zata zo nan akwai kayan da zaka sa….
Tsayawa Yarima yayi tare da kallon usman yace akan wani dalili? Kayan da zansa ma sai an zaba min? Ni Mai yasa za’a kawo ta jibi, a Bari sai an d’aura auren mana
Usman yace Indai zaka auri y’ar gidan sarauta toh dole haka za’ayi wacce ba y’ar gidan sarauta bace za’a kawo ta Bayan an d’aura aure
Yarima yace I don’t know why kuke d’aukan al’ada kaman addini
Usman yace haba Yarima ai dad’i ya kamata kaji, gimbiya ce fah za’a kawo maka
Yarima bai kulashi ba yayi gaba abunsa
Usman dariya yayi dan yasan Yarima baya son auren kawai dauriya yake
Yarima na shiga d’akinshi wayanshi ya kunna, yana kunna wayan sa’ko ne sukai ta shigowa bud’ewa yayi yaga na mutane ne Kala Kala sai kuma na princess dinshi, nata ya shiga ya fara karantawa…..
Yarima kasan hankali na a tashe yake? Ka d’aga min hankali shine ka kashe waya dan Allah Yarima ka kunna waya bazan iya bacci ba yau har sai…… Bai karasa karanta message din ba kiranta ya shigo
Murmushi yayi tare da kashewa sannan ya kira ta….
Tana ji ya d’auka ta fashe mishi da kuka
Yarima hankalinshi yayi mugun tashi dan jin Zainab dinshi na kuka
Yace my princess what happen? Plz stop it.
Batai magana ba sannan bata daina kukan ba
Ido ya lumshe dan baya son kukanta ko kad’an, yace tunda ba zaki shuru ba gani nan zuwa yanzu
Da sauri tace ni karka zo, kasan zan damu shine ka kashe waya kasan tun yaushe nake cikin damuwa, dan Allah Yarima karka karamin irin haka bazan iya jura ba Ina Sonka Yarima ban son wani abu ya sameka n…. Shuru tayi cikin jin nauyin abunda taita fad’a gashi ance magana zaran bunu
Yarima kam jin kalmanta na karshe yasa shi jin wani irin dad’in da bai taba jiba, ina Sonka Yarima, ban son wani abu ya sameka, murmushi yayi tare da fad’in ina jinki….
Kit ta kashe wayan domin wani irin kunya taji, tana kashe wayan ta Fara dukan kanta kai na kwafsa… Shuru kuma tayi tana mamaki yau itace take jin kunya dan tace Tana son wani, ikon Allah ita da take tubewa tsirara gaban namiji duk bata ji kunya ba sai dan tace Tana son Yarima. Kai gaskiya Yarima kai daban kake Sonka a jini na yake.
Yarima kam jin ta kashe wayan yasa ya saki wani irin murmushi mai cike da farin ciki kara kiranta yayi….
Ido ta bud’e dake lumshe tare da d’auka bata ce mishi komai ba
Yarima yace kara fadamin abunda kika ce d’azu
Tace Mai nace ni na manta
Yace oh I see, bari in tuna miki…
Da sauri tace Yarima saida safe bacci nake ji
Murmushi yayi dan yasan so take ta zille bata son ya tuna mata… Jin ana mishi nocking yasa yace ok baby good night dream about me, nd tell me tomorrow yana fad’in haka ya kashe wayan tare da tashi dan yaga Waye ke mishi nocking
Bariki bayan ya kashe wayan, murmushi tayi tare da fad’in ina Sonka Yarima gaba d’aya kasa na canza daka abunda na fito ina fatan kaima zaka amshi kaddara Kar kaki amsa kaman yanda akaki amsanta a baya hawaye ne ya zubo mata ….. Ganin tunanin da bata son yi yana son tayi shi yasata tashi tayi waje dan bata son tunawa da baya ko kad’an