BARIKI NA FITO 1 & 2
Yarima bayan ya bud’e kofa sisters dinshi ya gani su duka, wani irin murmushi ya saki cikin jin dad’i tare da fad’in saukan yaushe?
Hafsat tace bros tun dazu suka zo, suna ta jiranka baka dawo ba
Salamatu tace wai ina kaje ne
Yace Kai sis wannan tambayar ai sai ku Bari a gaisa dariya duka suka saki tare da shiga falo din suka zauna
Yarima kallon y’an uwanshi yake yana jin dad’i, yau gasu su duka sun had’u, rukkaya, salamatu, Fatima, nd lil Hafsat dinshi, yarima yace shine kuka zo da wuri haka?
Fatima tace bikin fah saura kwana biyar Aini da naso inzo tun yana sati biyu
Dariya Yarima yayi Sosai kaman ba shiba, yace sai kace Kece maman ango ba
Tace ai yayar ango kaman uwa ce
Yarima murmushi yayi
Zama sukayi suna ta fira cikin so da kauna tare da tsara irin abubuwan da za ayi duk da dama sun shirya komai,
Shidai Yarima jinsu kawai yake dan baya son ana firan bikin kwata kwata
Katsina
Gefen amarya wato gimbiya zinatu Anata shirye shirye Sosai musamman ma ita amaryan inda take ta gyaran jiki
Gimbiya zinatu ce a d’aki daka ita sai wata kawarta kallo d’aya zaka ma kawar ka gane itama suna da sarauta domin yana yin shigarta da kuma yanda takeyi alaman akwai giyan sarauta akanta, y’ar sarkin bauchi ce yarinyar gimbiya Amina
Kallonta gimbiya zinatu tayi tace my love kina ganin duk abunda na tsara zai bada matsala kuwa?
Gimbiya Amina tace bana tunani amma Idan kika wuce gonarki zai iya bada matsala dan haka kiyi taka tsan tsan
Murmushi gimbiya zinatu tayi tace karki damu, baza’a samu matsala ba, tare da d’aga ma gimbiya Amina gira
Gimbiya Amina wacce take magana kaman bata son yi tace ina fatan haka, dan Idan aka sami matsala daka Wajanki toh karki ce ban fad’a miki ba
Murmushi gimbiya zinatu tayi tace, haba haba ai ko d’aya na iya taku na
Gimbiya Amina tace da sauranki dai domin naga kina ta rawan kai nidai ki kiyaye tana fad’in haka ta tashi tayi toilet dan tayi wanka
Ganin ta shiga toilet yasa gimbiya zinatu fad’in my love ko rigima….. Toh fah wannan wani abu ne ake cewa gimbiya tayi taka tsan tsan????
Gaba d’aya masarautar Zazzau ta kidime wajan hidiman bikin tilon d’anta guda d’aya wato yarima Aliyu d’a d’aya namiji a wannan masarautar mai albarka
Yau za’a kawo gimbiya zinatu cikin wannan masarautar ita da y’an uwanta har sai Bayan an d’aura aure zasu wuce abar amarya a nan, an ware musu gefe guda .
Yarima ne zaune akan gadon d’akinshi yana ta faman yin tsaki ga kayan da zaisa an ware Mai, gashi yana ta kiran gimbiyarshi Zainab wato bariki taki d’auka message ya Mata tare da fad’in
Pick my call
Reply ta mishi da fad’in
Sorry I can’t pick your call now har sai bayan bikin ka karmu shiga hakkin amarya
Yana karanta message din ya buga hannunshi biyu domin yana bala’in son jin muryanta, gashi daka yau babu inda zashi har sai an d’aura aure, tashi yayi tare da fad’in Indai bazaki d’auki wayana ba dole In Karya wannan al’adan inje in ganki tunda ba addini bane…. Shuru kuma yayi ance gimbiya nan da 30mnt zasu karaso kuma shi zai tarbeta… Dan shuru yayi yana nazari d’aukan key din mota yayi daka gani shi kadai zai fita yace I have to see my princess
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
*PAGE 24*
Fita yayi ya bud’e kofarshi ganin fadawa a wajan yasa yayi tsaki, domin ya tabbata bazasu Bari ya fita shi d’aya ba and inya fita dasu akwai matsala, dan shuru yayi sannan ya dake tare da fitowa,
nan suka zube suna gyara kimtsa Allah ya taimaki Yarima Mai jiran gado takawarka lafiya…..
Dakatar dasu yayi alaman ya isa, gaba yayi suka tashi suna kokarin binshi ya dakatar dasu tare da fad’in bana bukatar ku bini.
kansu na k’asa suka amsa da fad’in komai Yarima yace dole mubi
Murmushi yayi cikin jin dad’i tare dayin gaba, mota ya shiga kiran VENZA gaba d’aya motar tinted ne baka ganin wanda ke cikin motar saboda tinted din but na motar na ganinka, harya tada motar saiga
Usman nan kaman daka sama bud’e motar yayi ya shiga, tare da fad’in ina zaka? Gimbiya ta karaso kai ake jira
Yarima Aliyu tsaki tayi tare da kashe motar ya fita cikin takaici
Ganin ya fita yasa usman binshi a baya
Direct d’akinshi ya shiga kayan da akace shi zaisa in gimbiya tazo shiya sa, sannan ya fito a falo yaga usman baiko kulashi ba yayi waje abunshi
Ganin haka yasa usman ya bishi a baya yana murmushi.
Koda Yarima ya fito fadawa suka bishi direct wajan motocinshi ya nufa suka bud’e Mai ya shiga, usman shima da sauri ya shige aka ja dan zuwa gidan sarkin katsina dake nan domin suje su tawo dasu.
Koda suka karasa duka mutane suna mota, gimbiya ce ta fito fadawa suka mata Iso har motar da Yarima Aliyu yake ta shiga ta zauna a baya, usman kuma ya koma wata motar
Gimbiya zinatu Bayan ta shiga ta kalli Yarima cikin murmushi tare da fad’in wow my handsome….
Ido ya rufe cikin takaici, jiba yanda take abu a gaban driver
Jan motar akayi suka fara tafiya, hannunta tasa cikin na Yarima
Kallon hannun yayi tare da kallonta ya watsa mata wani irin kallo da sauri ta cire hannunta ganin irin kallon da yayi mata, ganin yanda ya d’aure fuska yasa taji ya bata tsoro yasa ta kame bakinta tayi shuru
Bayan sun karasa masarautar tasu, aka bud’e musu Mota suka fito, su mum ne a tsaye dasu fadawa domin tarban su, gimbiya da Yarima suka fito tafiya suke a tare har inda aka ware musu, wajan babba ne gefen gimbiya da kawayenta babba ne sannan gefen danginta shima daban, Bayan gimbiya zinatu ta shiga ciki zama tayi Yarima fita yazo….
Tayi caraf tace Yarima ba yanzu zaka fita ba sai wani ya shigo
Yace Aiba gadinki aka bani ba yana fad’in haka yasa Kai ya fita a falo yaga su mum suna kokarin shigowa ciki
Mum ganin ya fito tamai wani irin kallo alaman ya koma, ranshi a jagule dole ya koma ciki, tare suka shiga gimbiya zinatu gaida mum tayi cikin girmamawa
Mum amsawa tayi tare da fad’in tubarkallah, su Hafsat zama sukayi suna dan Jan gimbiya da fira duk da tana yi tana d’an jin kunya kaman dagaske, mum ita da Yarima suka fita
Mum d’akin yarima sukayi tace Yarima Wai mai yake damunka ne? A haka kake son in bari ka kara aure jiba yanda kakema wannan ma Anya zakai adalci kuwa?..
Da sauri yace mum kiyi hakuri, yau raina a bace yake amma ai kin San your son zaiyi adalci mum
Murmushi mum tayi tace waya batama Yarima rai?
Dan shuru yayi Kafin yace mum Zainab taki picking calls dina, wai sai Bayan biki na, gashi babu inda zani Har sai an d’aura aure
Murmushi mum tayi danta gane itace wacce d’an nata yake so, tace bani number dinta in kira maka ita..
Kaman yana jira da sauri ya karanto ma mum number din, dialing mum tayi ringing biyu bariki ta d’auka tare dayin sallama dan tunda taga number din take tunani dan taga special number ne sai yasa tayi sallama
Amsawa mum tayi tare da fad’in my daughter, Yarima ya kawo karanki kinki d’aukan waya.
Jin haka yasa ta gane mum dinshi ce, da sauri ta gaida mum cikin girmamawa.