BARIKI NA FITO 1 & 2

Shuru yayi ba tare daya tanka musu ba danshi rashin d’aukan wayan zainab yana sashi cikin wani hali
Bariki kam tana kallon kiranshi taki d’auka domin wani irin azabban kishi take ji, danya fad’a mata yau za suyi mothers day tasan muddin ta d’auka sai taji wani abun ta rasa mai yasa ta kasa controlling kanta tana matukar kishin Yarima, wani hawaye ne ya zubo mata tare da fargaban duk ranan da Yarima yasan tana bin maza ta shiga uku, kirgawa ta farayi rabonta dana miji tace dole ina gama istabra ‘I muyi aure karya ja wani lokaci Kafin a sami masu bakin jaba su fad’a ma Yarima ya fasa auranta, tunawa tayi sanda yake fad’a mata zina kawai zaki aikata in fasa auranki…. Lallai Yarima in yasan nabi maza bazai aureni ba, dole insa Ayi bikin da wuri in yaso Bayan bikin zan fad’a mishi komai da baki na tabbas dole auran ya zama na sirri ba kowa zai san da auran ba sai an d’aura a hankali ta furta karuwanci baiyi ba yaune rana ta farko da tayi data Sani tare da biye ma zuciyarta data ingizata tace mai yasa na yanke hukunci cikin fushi kuka ta saki mai taba zuciya …..
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
*PAGE 25*
INA MIKA SA’KON TA’AZIYA GA UMMU ABDALLAH TARE DA SAURAN MEMBERS DIN GROUP DIN BARIKI NA FITO FAN’S 1 WANDA TAYI RASHIN D’ANTA GUDA D’AYA TILO ABDALLAH????????????????ALLAH UBAN GIJI YAJI QANSHI YASA MAI CETO NE ALLAH YA BAKI HAKURIN RASHI????????????????
Babu abunda take a halin yanzu saida na sani, duk da abunda aka mata yasa ta aikata hakan ido ta lumshe tana kokarin tuna baya, da sauri ta bud’e idon dan bata son tuna abun ba’kin cikin daya faru da ita, lallai mutane basa ansan kaddara Idan ya faru akan wani sai dai in akansu ne mai yasa ba’a amshi abunda ya faru da ita a matsayin kaddara ba kuka ta saki mai sauti, ina gatan da aka nuna mata ina kulawan da aka nuna mata Mai yasa da kaddara ya fad’a mata ba’a amsheta ba n……. D’an tsagaita wa tayi da kukan da takeyi tare da fad’in lallai shima Yarima ban tunanin zai amshi kaddara tunda iyayena sun kasa amsa lallai Yarima shida ya ganni daka sama bazai amshi kaddara ba Mai yasa na rayu Mai yasa ban mutu ba tun ranan dana had’u da wannan mummunan abun Mai yasa naci gaba da rayuwa kuka ta kuma saki mai sauti…
Kuka take Sosai lokaci d’aya idonta ya kumbura tare dayin ja, duk duniya babu wanda yakai mahaifinta Sonta inta cire mum dinta, haka shima mahaifinta duk duniya yafi Sonta cikin yaranshi amma shine mutum na farko daya Fara kyamarta da mummunan kaddara ta sameta Wanda bata san Ya akai ya sameta ba, mahaifinta shine mutum na farko daya Fara nuna mata kyama saboda gudun kunyar duniya duk da mutum ne mai sani amma baiyi amfani da sanin shiba la…. Jin karan wayanta yasa hankalinta yayi kan wayar Sunan Yarima ta gani harya tsinke bata d’auka ba kara kira yayi shima bata d’auka ba
Ido ta lumshe son Yarima Aliyu yayi mata yawa tana matukar sonshi sai dai bata tunanin shima zai amsheta a yanda take Dan yanda yake ta nanata mata bazai auri mace mazinaciya ba ido ta lumshe mai yasa son Yarima yayi saurin shigana? Mai yasa so yayi min shigan sauri tana maganan tana kuka Jin karan wayanta alaman sa’ko yasa ta d’auka ta bud’e ganin Yarima ne yasa ta bud’e dan taga Mai yace….
Zainab maina miki? Yau true out kinki d'aukan phone dina, kin San yanda nakeji kuwa? And I know kina ganin kirana in baki d'auki phone dina ba zaki ganni cikin daren nan.
Tana karantawa ta Fara kokarin kashe wayanta saiga kiranshi nan ya kuma shigowa k’in d’auka tayi dan a halin da take jinta yanzu bata tunanin zata iya magana gashi inta d’auka yaji muryanta saiya tambaye ta Mai yasa take kuka, wata zuciyar tace in yazo fah? Da sauri ta doka Mai kira k’in d’auka yayi sannan bai kirata ba ganin haka ta kara kiranshi amma ya’ki d’auka hankalinta ne ya tashi cikin sauri tasa dogon hijab tare da d’aukan wayanta tayi waje tana fita koh tayi Sa’a taga habib shida jamil suna zaune da sauri ta nufesu taja hannun habib sukai gaba
Habib yace lafiya kuwa? Kike jana kaman wata kububuwa?
Bariki cikin dashewan murya tace yarima, yarima
Habib yace maiya sami Yariman?
Tace yana hanya zai iya fad’owa koda yaushe
Habib yace na shiga uku cikin wannan tsohon daren karfe Goma saura fah yanzu Mai zai zo yayi miki kodai shima kin bashi zumar ne yasha?
Bariki tace a’ah saboda ya kira naki d’auka S….. Karan wayan habib ne yasa bariki yin shuru
Ciro wayan habib yayi cikin wata karaman jaka daya rataya yace lah Kinga d’an halak Wlh shine ke kira na, d’auka habib yayi ban San mai Yarima yace Mai ba naji yace eh Tana nan maraban jos, tare da kashe wayan. Habib kallon bariki yayi yace toh Yarima dai yana hanya dan haka saimu karasa gidan da yake ganinki
Bariki tace dare yayi bari in kara kiranshi banso yazo yanzu Kar wani abu ya sameshi….. Kiran Yarima tayi harya tsinke bai d’auka ba message ta mishi tare da fad’in
Plz Yarima pick my call, plz am begging you pick my calls
Kara kira tayi baiyi picking ba, gaba d’aya ta shiga damuwa message ta kara mai
Plz Yarima karka zo dare yayi karka biyo hanya plz
Shima shuru babu reply
Kallon habib tayi tace ina tsoran ya taso yanzu dare yayi karfe nawa zai zo Ya koma dan Allah kirashi kace karya zo…..
Habib yace nifa bariki ban son rashin mutunci na fad’a miki ki daina kaini jinsin da banawa ba
Bariki tace yakuri dan Allah ki kira min shi
Tabe baki yayi tare da fad’in yanzu kikai zance tare da Doka ma Yarima kira harya tsinke bai d’auka ba, habib yace Kinga Ya’ki d’auka nasan yana hanya dan haka sai kizo mu karasa
Babu yanda ta iya dole gidan suka karasa inda suka shiga ciki dan gidan na wata tsohuwa ne da y’arta guda d’aya itama y’ar duniya ce amma tana da aure basu yi koda 20mnt ba saiga Yarima yana kiranta da sauri ta d’auka….
Kafin tayi magana ya rigata da fad’in come out Ina waje yana fad’in haka ya kashe wayan
Kallon habib tayi da yake ta fira shida masu gidan tace ina zuwa yazo yana waje
Habib yace ok bari in jiraki a nan
Fita tayi amma abun mamaki bata ga motocin Yarima ba sai wata mota data gani kiran jeep tana shek’i gashi motar gaba d’aya baka ganin wanda ke ciki, har zata koma taji ana mata horn ganin haka yasa ta gane Yarima ne a ciki motar ta nufa tare da bud’e baya taga ya’ki buduwa gaban motar taga an bud’e gaban ta shiga tare da mamaki ganin shi yayi tukin yazo ba tare da kowa ba…
Kallonta yai tayi idonta duk ya kumbura yayi wajan 3mnt yana kallonta ba tare da yace komai ba, haka itama tunda ta shigo bata ce mishi komai ba
Hannunta ya kamo tare da janyota jikinshi yayi hugging dinta, baka jin karan komai saina motar dan a kunne yake saboda AC yana kunne, sai kuma sautin numfashin su….
A hankali yace my princess Mai yasa kika k’i d’aukan wayana? Kin San yanda na damu kuwa? Mai yasa kike son d’agamin hankali? Kin San yanda nakeji Idan na kiraki baki picking ba? Dame kike son inji da auran da ake kokarin…… Shuru yayi tare da d’agota daka jikinshi yace my princess tell me maiya faru yasa kika k’i d’aukan wayana? Tell me