BARIKI NA FITO 1 & 2
Kokarin magana takeyi amma ta kasa domin muryanta a dashe yake ganin haka yasa ta fashe da kuka….
Yarima Aliyu gaba d’aya ya shiga damuwa, yace Zainab plz stop it, mai yake faruwa?
Ganin taki magana kuma taki daina kukan yasa ya d’aura hannunshi akai cikin damuwa kanshi yaji yana juya Mai ga sautin kukanta da baya son ji….. Matsawa yayi kusa da ita ya rungumota tare da fad’in plz stop it bana son jin kukanki tell me maike damunki plz my princess…
A hankali tace Yarima Ina tsoran abunda zai faru gaba Ina Sonka ban son in rasaka, ina tsoran kaki amsan kaddara Nasan ban dace dakai ba m…..
Dakatar da ita yayi tare da fad’in wani irin kaddara? Kalli idona tell me maike damunki nd i promise zanyi accepting dinki a duk inda kike saboda ina sonki
Tace you promise komai nace zakai accepting dina koda nace na taba zina….
Ido ya lumshe cikin bacin rai yace my princess I have tell you so many times ki daina danganta kanki da wannan kazaman Kalman, karki manta na fad’a miki zina kawai mace zata aikata in fasa aurenta domin masarautar mu bazatai accepting haka ba, let me tell you something Idan mace tayi aure a masarautar mu bama saki har sai kayi laifi biyu shima sai an ganka zina da kisan Kai wannan laifin shine zaisa a saki mace, Kinga zina tana d’aya daka cikin manyan laifi ko a addinance bazan iya auren macen data bada mutuncinta a waje ba na tabbata Zainab ke bakya d’aya daka cikin wannan matan marasa kamun kai kin samu tarbiya….
Ina da matukar kishin abunda nake so, Zainab mai kike son fad’a min?
Bariki jikinta yayi sanyi, domin jin kalaman Yarima lallai Indai masarautarsu basa saki ya kamata ta aureshi kaman yanda ta tsara tun Farko fad’a mishi yanzu babu abunda zai haifar sai dai ma yasa ya tsaneta ko kuma ya barta har abada, lallai ya kamata in boye komai sai bayan auranmu in bashi Labarin kaina…..
Katse mata tunani yayi da fad’in ina jinki….
Tace Yarima Ina tsoran Kar y’an uwanka Suki yarda dani a matsayin matarka iyayena basu da karfi, na shiga damuwa Sosai Yarima kafi karfina sai yasa nake son ka amshi kaddara kayi hakuri dani ta karasa maganan cikin kuka
Ho ho ho ho zo kuga yanda Yarima ya rud’e tare da fad’in my princess saboda wannan abun kike ta saka kanki cikin damuwa, yace kalli idona, bata ko motsa ba balle ta kalli idon nashi Dan bama iya kallo za tayi ba
D’ago Mata da fuska yayi suka had’a ido tana kokarin kawar dakai ya ri’ke mata fuskan tare da fad’in don’t move, yana magana yana kallon idonta yace I can’t live without you my princess you are the girl that I love in my life, ki daina tunanin akwai abunda zai sa in fasa aurenki how I wish aurenmu za’ayi jibi, dana nuna miki how much I love you, but lokaci kad’an nake jira soon u will be mine forever, ke nake so only you ba wani abu ba, bana bukatar komai sai ke.
Tunda yasa idonshi cikin nata gaba d’aya ta daburce, domin ta rasa mai yasa Yarima Aliyu yake mata kwarjini Tana jin abubuwa da dama akanshi Wanda bata ji a sauran mazan da tayi hulda dasu, ido ta lumshe domin bazata iya juran kallonshi cikin ido ba .
Ganin ta lumshe ido yasa ya saki murmushi tare da fad’in my shy Princess Bride to be Mrs Yarima Aliyu insha Allah
Bud’e ido tayi tana murmushi
Yace baby ina bukatar inzo Walima dinki, u say ranan Saturday right? Baki bani Kati bama ko am I not invited?
Murmushi tayi tare da girgiza kai tace u r invited but amma na yafe basai kazo ba, tunda I promise zan tura maka komai na wajan, Walima din
Yarima yace hakane but ranan dole In ganki coz Nima zan tayaki murna tunda an hanani zuwa wajan walima
Murmushi tayi tare da fad’in ai yanzu ni ban isa ince karka zo ba inma nace sai dai in ganka
Dariya yayi tare da fad’in toh ya zanyi your love drive me crazy bana ji bana gani, Indai Anga nutsuwan Yarima Toh yaga zainab dinshi
Dariya tayi tare da fad’in Rufamin asiri
Yace ai a rufe yake my princess
Tace Yarima dare fah yana yi, wlh Ina tsoran dare Kaga kuma kai d’aya kazo ko in had’aka da habib ku koma tare?
Murmushi yayi tare da fad’in ashe you care for me
Uhm kawai tace
Yarima yace my princess karki damuwa zan koma ni d’aya, tare da danna wayanshi yaga 11:15 yace Kai dare yayi Sosai ashe har 11:15
Bariki tace toh kazo ka koma Mai yasa kazo kai d’aya?
Yace ke kika sani mana tunda bakya d’aukan wayana, ai dole inzo in ganki inga ko lafiya
Tace Bari in shiga ciki saida safe koh?
Murmushi yayi yace korana kikeyi?
Tace a’a ni inda babu damuwa Aida ban Bari ka kama hanya ba, saboda ina tsoro
Yace Toh ko zaki raka ni?
Ido ta zaro alaman ni kuma, lokaci d’aya kuma tace a’ah kaga saida safe tare da kokarin bud’e motar d’ayan hannunta ya kamo
Yace korana dai kikeyi yau
Tace Yarima ba haka bane dare yayi kuma you are alone Kaga yanzu lokaci tare da danna wayanta 11:20 tace dan Allah Yarima ban son ka kara bata lokaci a nan
Yace OK my princess peck ya Mata a hannu tare da fad’in good night saura in kira k’iki picking
Tace dole inyi
Murmushi yayi tare da jan motar yayi gaba.
Saida ta Bari ya fita daka Layin Kafin ta shiga cikin gidan
Tana shiga tace ma habib muje tare da yima masu gidan sallama.
Bayan sun fita habib yace wai bariki ya kuke ciki ne da Yarima?
Tace kawata ai yanzu abunda muke ciki shine ka nema min wanda zasu tsaya a matsayin iyayena sannan a anguwan kanawa kasan nace mishi nake, ina son gidan da zamu zauna ya zama na talakawa Sosai sai mu kama haya
Habib yace an gama karki damu zan sami dattawan mutunci masu kamala su tsaya a matsayin iyayenki sannan zani wajan sarkin anguwan kanawa muyi magana saiki tanadi kud’i dan kin San abun na kud’i ne
Bariki tace indai kud’i ne Babu damuwa ko nawa zan kashe Indai zan sami Yarima na
Habib yace ah Yarima yayi sa’ah ayabarsa tama bariki
Duka takai ma habib tare da fad’in ban son iskanci, yauwa Ina son in dan had’a Walima amma fa na mutunci dan hijab za’a saka
Habib yace na shiga uku an fasa aurena miye wani hijab za’a saka kice wannan ba namu bane yana maganan yana bud’e hanci ,wlh bariki naga kina neman komawa ta Allah
Tace toh da ni ta wacece
Habib yace kin fini Sani
Tace Yarima na kira na kaga nayi gaba da gudu tayi gaba dan ta isa Gida Kafin kiran ya tsinke…..
Not edited????
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
*PAGE 26*
Gudu bariki take amma Kafin ta shiga cikin gidan kiran ya tsinke, bayan ta karasa ciki ta shiga d’akinta ta rufe sannan ta doka Mai kira harya tsinke bai d’auka ba sai daka baya ya kirata ta d’auka tare dayin sallama
Yace my princess gudu kikayi naji kina ta nishi
Tace a’a Yarima gudu cikin wannan daren, ka kai gida ne?
Murmushi yayi tare da fad’in sai kace a duniyar aljanu yaushe na tafi kawai nace bari in kiraki kiyi ta tayani fira har inkai gida
Tace driving fah kakeyi taya za muyi tayin waya haka plz kayi hakuri in kaje gida muyi waya plz Yarima Kaga yanzu dare ne gashi kana hanya