BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Hjy habiba tace wannan wani irin abune ke har kina tunanin zan Bari ya aureta haba never Wlh, taya zan bar d’ana ya auri haulat?

Hjy Umaima tace toh miye danya aureta ni banga illan hakan ba

Hjy habiba tace ina tunanin kin manta miye tsakani na da haulat koh? Karki manta love muke nida ita, sannan har kiyi tunanin in d’auki d’ana na ciki na in bashi aurenta Kema kin san wannan abun bamai yihuwa bane har abada

Hjy Umaima tace ki roki Allah Kar ace yana Sonta domin na tabbata inma baki yarda ba mijinki toh zai yardan mishi ya aureta

Hjy habiba tace mubar wannan maganan dan Wlh duk yanda zanyi sai Nayi Kai Tashin hankali AI Wlh koda zan rasa shi ban tunanin zan Bari ya auri haulat dole in korashi ya koma inda ya fito Wlh inya gama karatun ya dawo gaba d’aya

Hjy Umaima murmushi tayi tace amma kam habiba kaman kinso kanki da yawa ,amma dai bari inyi shuru kawai ki roki Allah Kar abunda kike tunani ya zama gaskiya dan na tabbata bazaki iya juran rashin tilon d’anki ba

Hjy habiba tace Kinga mu canza firan a ina kika samo wannan yarinyar kuma Uwar kwashe kwashe?

Hjy Umaima tace Kedai bari daka Kano tazo min jiya a instagram muka had’u, hotunan ta na gani sukai min kyau shine na gayyato ta, gashi kuma babu laifi ta iya love, Bari in kirata ku gaisa Tana yana yi da bariki naga kaman suna dan kama

Hjy habiba dariya tayi tace kawai bariki dince a ranki sai yasa kike ganin kaman suna kama, wlh ki rage kwashe kwashe Inba haka ba wata rana sai kinci mushen hq sai kin had’u damai warin hq kuma haka zaki ci tunda kin jajibo

Hjy Umaima dariya tayi tare da fad’in Wlh bazan ciba Tashin hankali AI Ina jin wari zan korata Wlh Ina zan iya AI ban son harkan wari

Dariya suka saki su duka tare da shewa


Karfe 7 dai dai amarya ce zaune gimbiya zinatu cikin wani shegen material dinkin doguwar riga kasan yayi fad’i saman ya tsuke anyi rigan kaman wedding gown gashi daka Bayan yayi tsawo dole sai an ri’ke shi kayan ake ta kokarin gyara mata anyi mata makeup tayi kyau Sosai, bayan an gama gyaran suka fara shirin fita dan zuwa hall din da za’ayi dinner UKBRIDE a nan za’ayi dinner din, kuyangi ne suka kama ma gimbiya zinatu kayanta ta baya su duka sunsa kaya iri d’aya fita sukayi inda mota ke jiranta Bayan an bud’e Mata kofar taga Yarima a ciki shiga tayi ta zauna ko kallonta baiyi ba aka tada motar sukai gaba

Yarima yasa suit fari domin kayanta black ne sunyi matukar yin kyau Sosai koda suka karasa a mota suka zauna Kafin abokanan shi da kawayenta suka zo inda suka fito suka jera tare dan shiga cikin hall din Wanda yayi mugun had’uwa

Bayan sun shiga aka dinga watsa spray sama abun gwanin sha’awa aka saka musu cool music saida amarya da ango suka zauna a wajan da aka tanadar musu sannan suma abokanan ango da kawaye suka zauna a inda aka tanadar musu domin wajansu daban an rubuta bride friends na abokan ango kuma ansa groom friend, harta wajan dangin ango daban dana dangin amarya, ciki harda team din gimbiya zinatu Suma an basu nasu wajan daban dan na hango ummu Muhammad Anata zura abinci ita a dole biki nasu ???????????? sai dai banga team din bariki ba da alama suna can suna tayata dannan kirji ko kuma suna can suna shirye shiryen Walima suda su hjy babba da habiba y’an mata????????????????
Watsi ake da naira kaman babu gobe ga abinci nan Kala Kala sai Wanda kaga daman ci, amarya da ango sun fito dan suyi rawa fuskan yarima dai a d’aure suna rawan gimbiya na manne a jikinshi tace Yarima plz ka sake fuska mana mutane suna kallo kodan mutane plz yanda kuka san ta kara zugashi akan ya tamke fuska ganin haka yasa taja baki tayi shuru an raba abubuwa Kala Kala Anci ansha kowa ya kama hanyar gida a mota gimbiya taita ma Yarima kuka wai ya kamata ya sauko tunda gobe za’a d’aura musu aure Nasan baka so na amma tunda Allah yasa saika aureni aiko dan darajan mutane zaka sake….. Ganin tana ta zuba surutu ga driver a motar yasa ya janyota jikinshi tare da fad’in ya isa haka plz ki bari in munje gidan muyi magana…..

Bayan sun karasa mota na fakawa yayi gefenshi gimbiya ganin haka ta saki kuka tayi nasu gefen inda aka saukesu

Yarima yana shiga d’aki bariki ya kira wayanta a kashe tsaki yayi tare da jefar da wayan akan gadon d’akin

Koda Gimbiya ta shiga gefensu Tana hawaye gimbiya Amina tace lafiya?

Gimbiya tace Wlh Yarima na rasa mai yasa yake min haka

Tsaki gimbiya Amina tayi tare da shiga toilet

Yarima kam ranan haka yayi bacci cikin rashin jin dad’i wayan bariki a kashe gashi ya kira habib yace ta koma gidansu

Bariki kam ba komai yasa ta kashe wayan ba sai kishi domin gani take yana can suna soyewa da amarya ita kuma ko oho ranan taci kuka tare da fad’in yanzu ana d’aura auren Allah kadai yasan Mai yarima Zaima amaryanshi Kut kunji bariki fah

Toh masu iya magana dai sunce rana bata karya sai dai Uwar d’iya taji kunya a yau juma’a aka d’aura auren Yarima Aliyu da gimbiya zinatu akan sadaki naira dubu hamsin domin ance karanci sadaki shine albarkan aure…… Toh andai d’aura auren Yarima Aliyu da gimbiya zinatu zamu ga yanda zata kaya in an bama Yarima Aliyu gimbiya zinatu a matsayin mata ????????

Not edited

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

                 *PAGE 27*

END OF PART 1

DAN TSOKACI GAME DA MASU CEWA YARIMA BAI KAMATA YA AURI BARIKI BA TA ZUBAR DA MUTUNCINTA YANZU INDA YARIMA NE YAKE DA HALIN BARIKI NA TABBATA ZAKU DINGA CEWA YA AURI BARIKI INDA UZTAXIYA CE, ZA’A SAMU MASU CEWA INTA AURESHI ZAI SHIRYU DA SAURANSU WHAT A FUNNY WATO SHI NAMIJI KARYA AURI Y’AR ISKA MACE KUMA TA AURI D’AN ISKA DAN TAYI SANADIN SHIRIYAN SHI KOH? HABA WAI MAI YASA MU MATA BA’A MANA ADALCI NE? BAWAI INA MAGANA AKAN INA SON BARIKI DA YARIMA SUYI AURE BANE, NOP INA MAGANE NE AKAN RASHIN ADALCIN DA BA’A MANA MU MATA, HABA MUMA FAH MUTANE NE, KUDAI KAWAI KUCI GABA DA BINA

Yarima Aliyu Bayan an d’aura auren da mutane yaita gaisawa ana tayashi murna duk yanda yaso yabar wajan babu dama domin mutane ga kuma Mai martaba dake wajan haka ya hakura yana ta murmushin Ya’ke, bashi ya sami kanshi ba sai Bayan sallah la’asar yana idar da sallah ya samu ya silale a motar usman ya nufi hotel ya kama d’aki danya huta kuma yaji muryan bariki duk da bai tunanin zata d’auka inya kirata.

Toilet din hotel din ya shiga dan yayi wanka, domin yayi mugun gajiya dan tsaki yayi tunda aka fara wannan bikin mutum bai huta ba, wanka yayi Bayan ya fito ya kuma sakin tsaki dan babu kayan da zai canza dole wanda ya cire zai maida, boxers da singlet yasa sannan ya kwanta tare da d’aukan wayanshi ya kira princess dinshi yaci Sa’a a kunne ringing biyu ta d’auka tare dayin sallama

Amsawa yayi tare da fad’in baby kina ban wahala

Murmushi tayi tare da fad’in congratulations ango Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a dayyiba.

Amsawa yayi da Ameen my princess

Ido ta lumshe Wanda yake a kumbure cikin kishi domin amsan daya bata yana nuna mata alaman yaji dad’in addu’an data mishi, uhm maza kenan yanzu yazo yana mata wani dad’in baki anjima kuma ya nuna ma matarshi soyayya….. Katse mata tunani yayi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button