BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Da fad’in my princess Wai Mai yasa kika kashe waya? My princess kin San sonki yasa Ina Karya al’adan masarautar mu koh kina son Mai martaba yasa a rufe nine?

Dariya tayi tace a’ah baza’a rufe Yarima ba Ai sai dai a rufe ni a madadinka

Yarima yace Kai taya za’a rufe gimbiya Zainab, ya shirin Walima gobe ne koh?

Tace eh insha Allah, harna kosa ayi Wlh hankali na duk ya tashi sai naga an gama zan sami nutsuwa

Yarima yace hakane Allah ya taimaka amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai dai

Tace hakane insha Allah

Yace baki fad’amin dalilin kashe wayanki ba jiya

Tace Yarima banda caji ne shi yasa

Yace OK nasha ko Nayi laifi ne ai

Tace a’a koh d’aya baka laifi ango ne fah Kai

Murmushi yayi tare da fad’in hakane fah, kina ina?

Tace ina gida yanzu nake son inje kasuwa in siya wasu abubuwa da zanyi amfani dasu gobe

Yace ki tura wani yaje miki mana, ban son shiga kasuwan nan, Kar kije ayita kallonki

Dariya tayi tace haba Yarima Waye zai kalleni Bayan Ina da K….. Shuru tayi tana murmushi

Yace karasa mana my princess

Uhm kawai tace

Ajiyan zuciya yayi sannan yace when zan ganki?

Tace sai Bayan biki

Yace wani bikin kuma?

Tace naka mana

Yace bikin da aka gama, na fad’a miki rannan gobe zan zo in ganki so ki zama ready ki bani address din gidanku

Tace toh zan tura maka anjima, amma inaga tunda muna waya Ai basai ma na tura ba

Yace Nop ban yarda da hakan ba inna kira sai Anga dama ake d’auka balle gobe kina fama da mutane ai ban tunanin ma zaki d’auki waya

Murmushi tayi tare da fad’in zan d’auki wayan Yarima mana, amma tunda kace haka anjima zan tura maka address din

Yace ok bari in kwanta in huta for now

Tace bacci yanzu? Babu kyau fah yin bacci Bayan la’asar

Yace my princess hakane amma na gaji ne Sosai yanzu hotel na gudo dan in huta tunda aka fara bikin nan ban huta ba gashi Kema kina samin tension inta kira k’ik’i d’auka

Tace nifa ina d’auka sai dai in bana kusa

Murmushi yayi tare da fad’in in kika samin hawan jini ai shikenan

Da sauri tace dan Allah Yarima mubar wannan maganan bazan saka maka komai ba sai dai so na

Murmushi yayi tare da fad’in really

A hankali tace yes tare da fad’in bari in Bari ka huta

Yace OK tare da fad’in I love you

Tace thanks

Ya kara cewa I love you

Dariya tayi dan tasan yana son itama tace I love you too ne ba thanks ba …. Dan haka tace I love you too tare da kashe wayan

Murmushi yayi yana jin Sonta na kara shiganshi

Bariki fita tayi Bayan sun gama waya d’akin habib ta nufa tana nocking fitowa yayi duk yayi zufa, bariki tace lafiya kuwa naga duk kayi zufa??

Yace bariki Wlh ban son iskanci akan me zaki dinga kaini jinsin da ba nawa ba

Tace yakuri naga kinyi zufa kaman ana cinki

Habib yace inma cina ake Ai hq dina ne bana wata ba

Bariki tace kyaji dashi muje ciki muyi magana tare da shigewa d’akin habib

Habib na kokarin tsaidata amma tayi wuf ta shige

Tana shiga taga jamil tsirara ayabar nan tashi a tsaye, bariki kallon ikon Allah take wato dama cin junansu suke jamil da habib sai yasa habib ya fito duk yayi zufa da yake y’ar bariki ce saita basar tare da fad’in ke kuwa jamila kin saki hq kaman wacce akama fyade?

Da sauri jamil ya tashi yana saka wando tare da fad’in wannan ai iskanci ne zaki shigo d’aki babu sallama gashi kinzo Kinga min tsiraici da mutunci na

Bariki tace naga Ai habiba Mai d’akin tasan na shigo kuma miye dan nagani ai duk abu d’aya garemu

Habib dake tsaye yace maiya faru kika fad’o mana kaman saukan Aradu

Bariki tace sa kaya muje muyi magana a waje

Jallabiya yasa sannan sukai waje

Bayan sun fita tace ya maganan gidan kin basu kud’in?

Habib yace na basu mana Sun amsa har anyi fenti sai ki shirya muje kiga gidan, sannan ssuma iyayen bariki na musu magana na sami wani Dattijon da wata mata itama sune iyayenki saina miji guda d’aya shine yayanki anjima sai muje ku tattauna

Bariki tace yauwa hakan yayi Toh maganan Walima fah ka sami mutane da zasu zo kasan hijab nake son su sa

Habib yace bariki sanin kanki kin San banda mutunci akan me zaki dinga kaini jinsin y’an maza Ina mace

Bariki tace yi hakuri dan Allah kin sama min mutanan?

Habib yace ai naga abun naki ne yafi karfin kakata naji kina hijab sanin kanki ne ban hulda da irin mutanan nan inda masu 3quater kika ce ko mini skirt Aida kin gansu Kala Kala amma kyace masu sa hijab Mai ya had’a doya da manja??

Bariki tace kin fa San duk wannan Abun yana cikin tsarin aurena da Yarima naga Ina kaiki gabas kina yamma

Habib yace Toh shi Yariman zuwa zaiyi Aiba zuwa zaiyi ba inma yazo muda muke ciki kuna waje, muna ciki muna karkad’a duwawu da nono tunda ba ciki zai shigo ba, zaki wani kakaba mana sa hijab kaman wasu y’an makaranta , gaskiya ni bana haka ance da tsohuwa tayi zina

Tsaki bariki tayi

Habib yace tsaka ma da tayi Allah tsine Mata yayi

Bariki tace Wai Mai yasa kike son bada matsala ne dan Allah? Kin fah san saboda yanda nake sa hijab Yarima yake sona kuma gashi nace gobe zanyi sauka ai nasa kawayena suyi shigan mutunci tunda har kud’i Yaban inyi Walima ni bama mutane da yawa nake so ba kaman mutum goma ko shabiyar sun isa su zo mu d’auki hoto in an gama Inba ko wacce dubu biyar tasai abinci shikenan an wuce wajan

Habib yace yanzu naji Batu kodan kud’in da zaki basu zasu zo sannan zasu sa hijab din ko nikaf kika ce zasu sa tunda aikin kud’i za suyi

Bariki tace toh mutum shabiyar sunyi yanzu sai muje muga gidan dan Asa kayan d’aki daka nan kasuwa za muyi

Habib yace muje toh

A motar bariki suka je tana tuki habib yana gaba suna tafiya har unguwar kanawa inda habib ya kama mata Haya.

Bayan sun karasa bariki taga gidan tace Wai gaskiya gidan ya tsufa da yawa.

Habib yace dakyar ma na sami gidan Wlh Allah yaso ma mutum uku ne a ciki kune na hud’u zaki iya yima wajan gidan fenti ai

Bariki tace gaskiya hakan ya kamata dan gobe yarima zai zo gwara yaga gidan da fenti zai d’auka saboda murnan saukana akayi fenti din mu shiga inga d’akin in yaso saiki kira mai Fentin yazo yayi

Habib yace an gama Kinga masu gidan za suji dad’i

Gidan suka shiga d’akuna hudu ne amma gidan fes dashi duk da babu plaster an share gidan yyi kal dashi ko wani d’aki ciki da falo ne akwai Rijiya a gidan sai bayi biyu na wanka dana bahaya, d’akin suka shiga yayi kyau anyi mishi fenti d’akin siminti ne kasan sai silin din da dinnan duk ya tsofe, bariki tace babu laifi muje kasuwa musai kujerun hannu da gado na hannu haka suka nufi kasuwa bariki tasai kayan hannu harda tv karami da ledan d’aki sai karamin fridge shima na hannu Bayan sun gama akasa kayan a mota su bariki na gaba mota na binsu har gidan aka shigar da kayan aka saka d’akin sai yayi kyau da aka sa kayan d’aki y’an gidan suna ta le’ke Bayan an shirya kayan suka rufe d’akin sukai gaba

Bariki tace saura wajan iyayen nawa na bariki koh

Habib yace eh can zamu nufa yanzu

Bariki sunje Sun tattauna da iyayenta na bariki sunyi na’am kuma taga babu laifi sunyi kama da mutanan kwarai sai dai maganan yayanta tace a Bari zata ma Yarima karya akai dan gwara mama da baba sunfi muhimmanci, sunyi akan gobe za su zo su daukesu su kaisu gidan da bariki ta kama


Gimbiya zinatu ce zaune a cikin dangareren ginin da aka Mata, gefenta gimbiya Amina ce sai kuma wasu kawayenta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button