BARIKI NA FITO 1 & 2
Yarima ido ya fara bud’ewa a hankali yana ganin dishi dishi, akan gimbiya zinatu idonshi ya Sauka wanda yake ganin yayi mafarkinta yana kokarin sex da Zainab dinshi saida ya shiga yaga ashe gimbiya ce….. Dan shuru yayi tare da sauke numfashi da sauri da sauri ba komai ya tuna ba illar mafarkin da yayi ya sadu da gimbiya zinatu yaji ba virgin bace…… Idonshi ya kara kaiwa kanta inda ya ganta cikin rigan bacci duk jini ya bata rigan gabanshi yaji ya fad’i tare da tambayar kanshi Mai ya faru tsakaninshi da gimbiya????
Kodai ba mafarki yayi ba? Kai she is not a virgin a mafarkin da nayi so how come?? Naga jini a jikinta alaman jinin budurci ne?? Lokaci d’aya yaji kanshi ya fara mishi ciwo domin tunanin da yaita yi ya akai yayi wani abuda gimbiya bai Sani ba anya yana lafiya kuwa? Mai nasha Toh dahar na kasa tuna komai?? Ganin inya ci gaba da wannan tunanin ciwon kan da yakeji k’aruwa yakeyi sai yasa ya basar da tunanin, tare da tursasa ma zuciyarshi ta yarda da cewa yayi wani abu da gimbiya kuma ya sameta a budurwa…….
Gimbiya zinatu ganin irin kallon da yake mata yasa gabanta yaita dukan uku uku gashi baice mata komai ba sai ido daya kura mata, wanda a duniya idon Yarima Aliyu yana sata cikin wani yanayi Indai ta kallesu…..
Ganin ya tashi ya fara tafiya yasa ta kura Mai ido har ya kusa kofar toilet yayi taga taga kaman zai fad’i da sauri ta nufeshi tare da taro shi tana fad’in Yarima lafiya kuwa???
Yarima Aliyu wani irin jiri yake gani ga kanshi dake faman Sara mishi Wanda yake ji kaman zai fita dan ciwo, dakyar ya iya fad’in help me with my phone…..
D’an sakinshi tayi amma ganin ya kasa tsayuwa yasa tace muje in kaika toilet sai kayi wanka May be kaji karfin jikinka
Yarima Aliyu bai musa ba haka ta taimaka Mai sukai toilet tare da zamar dashi akan toilet, kallonshi tayi tace zaka iya wankan da kanka? Oh should I help you??
Dakyar ya d’aga kanshi ya kalleta, sannan ya girgiza mata kai alaman taje zaiyi da kanshi
Murmushi tayi sannan ta fita, bayan ta fita ta rufo Mai kofar toilet din, ta buga wani uban tsalle cikin jin dad’i domin abunda gimbiya Amina tayi Mata yasa Yarima kasa gane komai akanta, ta tabbata Yarima yana kallonta a matsayin budurwa ya sameta a hankali ta furta Kalman Alhmdlh in Allah ya rufa maka asiri babu wanda ya isa ya tauna shi…… Toh gimbiya dai kiyi a hankali karki manta Allah yana yafe laifi tsakanin bawa dashi, amma baya yafe laifin bawa da bawa har sai wanda ka cuta yace ya yafe maka…… Kuma shi Allah ba azzalumin kowa bane sai wanda ya cuci kanshi, da kaji kunyar lahira gwara kaji ta duniya…… Jin karan wayanta alaman sa’ko ya shigo yasa ta nufi wajan wayar da sauri,d’auka tayi taga gimbiya Amina ce da sauri ta bud’e sa’kon kamar haka….
Hey Wat up? Komai ya tafi dai dai kuwa ta wajan Yarima? Gashi a nan ana ta fad'in kin Kai budurci
Murmushi gimbiya zinatu tayi tare da bata amsa kaman haka…..
Eh komai ya tafi dai dai domin dai Yarima bai gane komai ba, jinin da nayi amfani dashi yasa yake tunanin ni budurwa ce, baki ga yanda yake ta kallona ba ko mamaki yake oho, amma fah tun jiya ashe a sume yake, ina tunanin maganin dana bashi yayi mishi karfi, saida nasa mishi ruwa ya Farfado, sannan har yanzu baya jin dad'in jikinshi, dan dakyar yake tafiya saida na taimaka na kaishi toilet dan yayi wanka....
Gimbiya Amina tayi Mata reply da fad’in Alhmdlh tunda shima ya yarda karki damu Idan ya sami bacci Sosai zai daina jin jirin, ki barshi ya kwanta ya huta inda so samu nema ki kashe wayanashi yanda zai samu yayi bacci Sosai Kar a dameshi, sannan kije ki tayashi wanka din…….
Tana gama karanta sa’kon Gimbiya Amina ta ajiye wayar tare da neman wayar Yarima danta kashe a kan kujeran d’akin taga wayoyinshi har guda biyu d’auka tayi taga yana da misscall da message bata tsaya duba waya mishi ba ta kashe wayoyin duka tare da ajiyesu inda bazai gani ba, toilet din ta nufa tare da bud’ewa inda ta barshi haka ta ganshi sai dai yanzu yasa hannunshi akanshi alaman yana mishi ciwo Sosai, ganin haka yasa ta karasa da sauri tana fad’in Yarima maike damunka? Bai kulata ba balle ya d’ago dakai ganin haka yasa tace Bari in maka wankan
bai musa Mata ba dan yana son yayi sallah dan baiyi ba,
Gimbiya ta taimaka mishi yayi wanka tare da alwala, Bayan sun fito ta d’auko mai jallabiya tasa Mai Yarima a zaune yayi sallah dan jiri yake gani bazai iya tsayuwan ba, yana idarwa ya fara kokarin tashi…..
Nufanshi tayi tare da kamo shi ta kwantar dashi akan gadon data canza zanin gado dan wancan tasa jini akai,.
A hankali yace give me my Phne
Tace ban San inda ka ajiye ba ka kwanta ka huta, Kaga baka jin dad’i
Ido ya lumshe tare da tunanin maike damunshi shidai tun jiya ya kasa gane komai, ga zainab dinshi da yake son gani…… A hankali yace yau Walima dinta and I promise to see her today, yun kurin tashi yayi amma ya kasa dole ya hakura tare da cema gimbiya ta duba mishi Phne dinshi ta kira Mai Dr ko kuma tama jakadiya magana a kira mishi Dr yanzu, yana maganan ne hannunshi na kanshi tare da cije lebe
Gimbiya tace ok bari inyi wanka insa kaya sai inje in fad’a a kirashi
Ido ya lumshe sannan ya bud’e alaman OK
Toilet ta nufa tana murmushi
Yarima kam ido ya bita dashi, ya rasa mai yasa duk yanda yaso ya yarda da gimbiya zinatu ya kasa, maiya sameshi jiya da daddare? Indai yayi sex da gimbiya zinatu tabbas abunda yake ganin mafarki ne gaskiya ne gimbiya ba budurwa bace… Toh Inba budurwa bace taya naga jini a jikinta sannan Nima gashi jinin ya batamin riga??? Yarima kanshi yaji ya kara Sara Mai da sauri ya kawar da wannan tunanin domin lafiyanshi yafi Mai komai a halin da yake ciki gashi ya rasa mai yasa tunda ya farka yake jin sha’awa gashi baya tunanin zai iya tabuka komai dan jikinshi babu kwari sannan uwa uba yana son ya gane maiya faru tsakaninshi da gimbiya zinatu Kafin ya kara kulata dan Indai bai gano komai ba baya tunanin zai iya yarda da ita harya saki jikinshi da ita, yanzu burinshi Dr yazo ya dubashi yaga mai yake damunshi da yasa jikinshi yayi weak yake ganin jiri daka nan yaje yaga zainab dinshi, ido ya lumshe domin tunawa da yayi rabonsu da waya tun jiya da rana sanda yake hotel, hakoranshi ya cije da lebenshi tare da fad’in nasan may be tana ta expecting call dina, Allah yasa Kar tayi fushi………
Gimbiya zinatu ta d’auki lokaci a toilet Sosai koda ta fito cikin shiri tasa wata doguwar riga yayi mata kyau, gani tayi Yarima yana bacci, daka gani baccin saceshi yayi bawai yana son yi bane, dan yanda ya kwanta ya nuna mata alaman haka, dan haka saita Fara komai a hankali dan karya farka daka karshe ma d’akin ta Bari tayi falo inda taga an jera kayan abinci a dinning…..
Kaman yanda habib da bariki suka tsara hakan ko akayi habib ya kawo mata duk sunsha hijab da nikaf, kaman dagaske gidan su bariki sukayi da suka kama haya a u/kanawa harda iyayen bariki din anyi ma kofar gidan fenti yayi kyau Sosai kaman bashi ba.
Barika kam gaba d’aya ta shiga damuwa na rashin samun Yarima a waya, toh maiya faru dashi Anya yana lafiya kuwa? Na tabbata akwai wani abu haka kawai Yarima bazaiki kirana ba sannan bazai kashe waya haka ba……
Habib ne ya Katse Mata tunani da fad’in bariki kizo Ayi hotunan mana dansu samu su wuce
Tashi tayi jiki babu kwari habib yaita d’aukansu hoto da aka gama bariki ta sallamesu suka wuce ya rage daka habib sai iyayen bariki na karya
Habib kallon bariki yayi tare da fad’in wai lafiya naga yau duk kinyi wani sororo kina tunani kin kasa sakin jikinki?
Bariki tace uhm Yarima rabona da muyi waya tun jiya da rana gashi wayanshi tun dazu nake kira a kashe
Habib tabe baki yayi tare da fad’in toh yana can wajan amarya ana soyewa yaushe zai tuna dake…..