BARIKI NA FITO 1 & 2
Sallah Yarima yayi azahar da la’asar Bayan ya sallame yasa wata farar shadda tare dasa ba’kin hula yayi kyau Sosai sai gashi ya fito falo gimbiyar na kwance akan kujera tana danna waya….
Jin motsin mutum tare da kamshin Yarima yasa ta tashi da sauri ganinshi tayi cikin shiri…..
Kallonta yayi tare da fad’in where is my phone?
Ganin jikin nashi ya watsake yasa tace Bari in d’auko maka, sama ta haura Jim kad’an sai gata da wayoyin Yarima, bashi tayi ya amsa …..
Tare dayin gaba ya fara tafiya…
Da sauri tace Yarima Ina zaka? Ga abinci a dinning…
Yace Nop am not hungry yana fad’in haka yayi gaba abunshi domin babu inda yake son zuwa sai kaduna wajan Zainab domin yasan yanzu tana can tana tunanin ko lfya may be ma tayi fushi dashi koda ya fita fadawa suka zube suna Mai gaisuwa tare dayi mishi kirari, ganin yayi gaba yasa suka tashi suka bishi direct wajan motocinshi ya nufa tare da shiga wacce ake fita dashi in zasu fita amsan key din yayi tare da fad’a ma fadawanshi bana bukatar ku biyoni yana fad’in haka ya tada motar yayi gaba abunshi
Gimbiya kam ita a halin yanzu bata damu da fitan Yarima ba tunda bai gane ita ba virgin bace farin ciki ne fal cikinta kiran gimbiya Amina tayi tare da fad’a mata ta shigo dan Allah Yarima ya fita
Bariki na zaune ita da habib wajan cin abinci, bariki dai ci kawai take amma ba dad’in abincin take jiba, dan gaba d’aya bata jin dad’in komai a bakinta, burinta kawai taji yarima ya kirata…….
Shi kam habib ci yake cikin jin dad’i da kwanciyan hankali, ganin bariki bata ci yasa ya tabe baki tare da fad’in iska na wahalar damai kayan kara, ni Wlh yanda nake dinnan banga saurayin da zaisa in dinga shiga wannan halin ba , haba bariki dan Allah kici abinci mu tashi mu tafi kin San yau akwai wasa zamu gwaggwaje duwai
Bariki tace Kai gskya ba tare zamu koma ba, dan Yarima yace min zaizo kuma na tabbata zaizo…
Habib yace kince wayarshi a kashe? Taya zaizo Kinga in zaki tashi ki tashi muje yanzu karfe nawa da har kike tunanin zai zo dan Allah tashi muje yau y’an nishad’i aka kira Wasan zaiyi dad’i yau.
Bariki tace uhm nifa yanzu kasan ban cika…….
Habib yace miye wani ka? Waye ka Ina mace akan wani dalili zaki dinga kaini jinsin da ba nawa ba ? Gskya banso yana maganan yana bata fuska…..
Zatai magana karan da wayarta ya farayi yasa hankalinta yayi wajan wayar tare da d’auka da sauri dan taga Sunan Yarima ne akan screen din wayar…. Tasa a kunnanta tare dayin sallama
Amsawa yayi har tana jiyo ajiyan zuciyarshi alaman yaji dad’i data d’auka yace my princess Ina gab da gidanku plz ki zauna da Phne dinki dan bazan gane ba ko kisa wani yazo bakin titi ya tawo dani
Tace ok bari habib yazo muna tare shima yazo tayani murna mumma fita amso Abu ne yanzu zamu dawo saiya tsaya ya jiraka
Yace OK tare da fad’in saina karaso
Bariki kallon habib tayi tace Yarima na hanya muyi sauri zaka tsaya a titi ku karaso gidan tare
Habib yace oh ni habiba yanzu Ina gansamemiyar budurwa in tsaya a bakin titi sai kace na fito good evening, tabe baki yayi tare da fad’in hakanan zanyi hakuri in tsaya tunda Yarima ne zai zo, zadai kisa y’an Maza suyi ta kallo na
Bariki dai bata ce komai ba tayi gaba ganin haka shima ya bita kud’in abincin ta biya sannan suka fita suka hau keke napep direct u/kanawa sukayi inda aka sauke habib a bakin titi ita kuma aka karasa da ita
Koda suka isa ta biya kud’in Keken tayi cikin gidan inda taci Sa’a duka iyayen bariki din data samo suna nan harda namijin yana zaune yana kallo zama tayi ta musu bayanin Yarima yana nan tafe, ta kalli mahaifin nata na Bariki Mlm musa tace dan Allah kayi komai yanda na fad’a ma ban son a sami matsala
Mlm musa yace baki da damuwa zainabu daka yanzu Ina son ki dinga cemin Abba ita kuma ya nuna Uwar bariki ta Karya yace ita kuma ki dinga ce mata Umma dan Kar mutane su gane kin San Gidan akwai mutane, sannan Idan Yarima din yazo ya tafi akwai wasu shawarwari da zan baki
Bariki tace hakane Abba ngd….. Suna cikin haka saiga habib ya shigo yana fad’in tashi kije yana waje yana jiranki
Tashi bariki tayi ta feshe jikinta da turare sannan ta kalli habib tace karka manta kayi komai yanda muka tsara
Habib yace babu damuwa komai zai tafi dai dai amma ki daina cemin kai kice min ki
Bariki dai fita tayi tunda ta fito idon Yarima Aliyu yake kanta ya rasa wani irin so yake mata da baya ji baya gani, tabbas yana son zainab wanda Abunda yasa yake kara Sonta harda irin shigar mutuncin da takeyi komai nata a rufe, ba irin y’an matan yanzu ba da suke nuna tsiraici a waje ba a gniñsu hakan shine Wayewa koyin haKan shi zaisa su sami mazajan aure,Wanda duk wani namiji mai kishi bazai auri macen dake fito da tsiraici waje ba sai dai yayi lalata da ita inma kikai shigan mutunci mutumin banza shakkar yi miki magana zaiyi dan baiga fuska ba domin yana yin shigarki zai bashi tsoro, duk namiji mai kishi bazai auri mace Mai fidda tsiraici waje ba, mace Mai tallan kanta waje ba….. Zuwan bariki ne ya Katse mishi tunani
Da sallama ta shigo cikin motar tare da rufe kofar motar,
Amsawa Yarima yayi tare da fad’in my princess Barka da yamma? Ya taro?
A hankali tace Alhmdlh tare da fad’in ya amarya?
Murmushi yayi tare da fad’in amarya tana lafiya.
Bariki ta d’anji haushi amma saita dake dan karya gane tana kishi
Yace nasan my princess ta gaji yau Sosai
Cikin ranta tace uhm maza kenan, Allah kadai yasan irin abunda yayi da matarshi Kafin yazo nan amma yazo yana mata dad’in baki yanzu…..
Karan wayanta ne ya Katseta kallon wayar tayi taga Alh madu ne da sauri ta kashe karan, tare da tunawa yace Mata yau zai zo,
idon Yarima na kanta yace pick your call
Kafin tayi magana wani kiran ya shigo kallon Yarima tayi taga shima ita yake kallo, kara kashe wayan tayi karan ya d’auke….. Hannu ya bata alaman ta bashi Phne din
Gabanta taji ya fad’i, sai tayi kaman bata ga hannun ba
Duk abunda takeyi idon Yarima na kanta murmushi yayi tare da fad’in Zainab mai kike boyewa bani phone dinki……
plz kuyi min hakuri ba kullum zan dinga muku posting ba saboda wani dalili amma inna sami lokaci zan dinga kokari Inayi kullum din
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
BOOK 2
*PAGE 4*
MAZA KUJI TSORAN ALLAH LOKACIN DA KAKE NEMAN MACE KOMAI TACE TANA SO SAIKA MATA, WANI ABUN MA BATA TAMBAYA KAKE MATA, IN ANYI AURE DUK HIDIMAR DA KAKE MATA SAIKA DAINA, KUMA BAWAI DAN BAKA DA HALIN YI DIN BANE, IN BAKA KYAUTATA MA IYALINKA BA WA ZAKA KYAUTATAMA, SAI KAJE KANA FAD’A AI BATA KWALLIYA BATA MAKA ABU KAMAN DA KAFIN KA AURETA, HMMM TAYA ZATA MAKA KWALLIYA TAYU KUD’IN POWDER DINMA BAKA BATA, KO KUD’IN KITSO A INA KAKE SON TA SAMI KUD’I TAYI??? DA LOKACIN DA TAKE GIDANSU TANA DA KYAU KOMAI NATA ABUN SHA’AWA AMMA KA AURETA KA MAIDATA TSOHUWAR KARFI DA YAJI, BABU KUD’IN LALLE, BALLE NA TURARE???? HABA MAZA MAI YASA KUKE HAKA?? IN KAJE GIDAN ABOKIN KA YA BAKA ABINCI MAI DAD’I SAI KAZO KANA ZAGIN MATARKA BATA IYA GIRKI BA, BAYAN KAINE BAKA BATA KUD’IN CEFANE WANDA ZAI IYA HAR AYI MAI DAD’IN BA, WLH KUJI TSORAN ALLAH MAZA MASU IRIN WANNAN HALIN DAKA RANAN DA AKA BAKA ITA A MATSAYIN MATARKA KOMAI NATA YA RATAYA AKAN KA, ABUNDA MUTUM YAKE GANIN BA KOMAI BANE ZAI IYA KAISHI GA HALAKA, IN KANA DA HALI KA FARANTA MA MATARKA YANDA INTA FITO ZA’A CE MATAR WANCAN NE SABODA AN GANTA FES, AMMA IN AKA GANTA SABANIN HAKA ZAGINKA ZA’AYI TUNDA ANSAN KANA DASHI PLZ MAZA KU GYARA DOMIN ALLAH ZAI TAMBAYEKU TUNDA KANA DA HALI DAMA BABU NE SAI AYI HAKURI