BARIKI NA FITO 1 & 2

Driver din alh madu ne yake mata magana, yace sannu hjy tun dazu nazo ai inata jiranki, mai gida yace ya kira baki d’aga waya ba, gashi hjy babba wayanshi shima baya d’aga wa.
Bariki tace Indai wajan hjy babba kazo yana filin rawa Nasan zaka iya dubashi a can , Tana fad’in haka tayi gaba ……
Binta driver din yayi yana fad’in a’ah Wajanki nazo oga yace inzo in d’auko ki sai yasa nazo…….
Bariki tace kaje kace Mai nace bazan zo ba, and kuma daka rana irin tayau karya kara kirana domin ni yanzu Allah ya shiryar dani na daina wannan banzan rayuwar aure zanyi
Driver din alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad’i Sosai, dama Wlh tunda na ganki naji Ina takaicin wannan rayuwar da kikeyi gaki yarinya karama amma babu daman inyi magana karki fad’ama oga ya koreni, wlh Ina takaicin wannan abunda yakeyi Wlh sai muje garin abuja muyi wata biyu uku amma baije yaga iyalanshi ba, sai dai wancan macen tazo wancan tazo ta sameshi a guest house dinshi, ni Kece ma naga yana bi kina Mai wulakanci, gashi mutum ya girma Mai yakon yabi Allah yaita istigfari amma shi ina kullum hanyar bata ita yake bi
Bariki tace Allah dai ya shirya, nidai ka fad’a mishi sa’ko na, Tana fad’in haka tayi gaba
Driver din alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad’i Sosai, yanzu kam zani in fad’ama wannan tsohon banzan sa’kon yarinyar nan
Yarima Aliyu saboda gudun da yayi kaman zai tashi sama 20mnt ne ya kaishi Zaria, Allah ya taimakeshi ya sauka lafiya, domin gudun fitan rai yayi yana tuki yana tuna abunda wanna yaron yazo yana cewa he said that you can come he is waiting for you Yarima Aliyu Wanda yaga Abun a matsayin kaman Zainab ta raina shine dan taga yana Sonta da yawa tsaki yaja tareda shiga gefenshi inda yaga gimbiya zinatu a falo tana zaune tana danna waya tasha wata doguwar riga y’ar kanti yayi mata kyau Sosai, kauda idonshi yayi daka kanta kaman bai ganta ba…
Tashi tayi da sauri ta nufeshi tare da rungume shi tana fad’in Yarima inata kiranka baka d’auka ba, tun dazu nake cikin damuwa tare da fargaban Allah yasa lfya
D’an janyeta yayi daka jikinshi tare da fad’in plz allow me to go and rest ,gaba yayi abunshi
Gimbiya zinatu binshi tayi da ido alaman Mai yake nufi, kodai ya gano gaskiyan al’amarin ne? Kai a’a bazai taba ganewa ba domin jinin daya gani zai sa ya tabbatar da ita budurwace, kafada ta d’aga alaman shiya sani Nasan wani wajan ne aka bata mishi rai, chatting dinta taci gaba dayi ita da gimbiya Amina.
Yarima kam yana shiga bedroom dinshi wanka yayi tare dasa jallabiya, ya fito yaga gimbiya nata danne danne dan tsaki yaja mara sauti yakan yi mamaki Idan yaga mutum yana bama waya muhimmanci fiye da komai, danya Lura da gimbiya zinatu Tana son bama waya lokacinta Sosai, dinning ya nufa dan yayi dinner….
Gimbiya ganin ya zauna akan dinning yasa ta tashi ta danna wani abu saiga kuyangi nan sun shigo, sun San abunda za suyi dan haka shi suka farayi zuba ma Yarima abinci, Bayan sun gama suka bar wajan, Yarima Fara ci yayi amma baya jin dad’in abincin dan ranshi a bace yake, yau princess dinshi ta bata mishi rai Sosai, gimbiya zinatu zama tayi itama akan dinning din tare da kura mishi ido tana kallon yanda yake cin abinci kaman baya son ci…… D’ago kai yayi yaga tana kallonshi a hankali yace stop starring at me like that,
Gimbiya zinatu tace in ban kalleka ba wa zan kalla?
Yarima shuru yayi ba tare daya kuma cewa komai ba, ya rasa mai yasa yake tantama akanta Sosai, abunda yasa har yanzu yake ganin kaman akwai wani abu tare da gimbiya zinatu shine lokacin da yayi sex da ita bai San sanda ya fara ba,hakan yana nuna mishi baya cikin hayyacinshi, yaga Abun kaman mafarki har yake ce mata ita ba virgin bace, abun daya d’aure mishi kai kuma shine yanda ya farka yaga jini a jikinta alaman she is virgin, wannan Abun yana d’aure ma Yarima kai, ido ya d’an lumshe lallai gimbiya she is a virgin Inba virgin bace taya zanga blood? Bai kamata Ina tantama akanta ba, I have to believe in what I see, tunda if she is not a virgin bazanga blood ba, duk da Nasan bako wace mace bace take zubar da jinin budurci kuma budurwa ce, but da yake Allah yana son nuna min sai gashi ita gimbiya Tana d’aya daka cikin masu zubar da jini a daren farkon su, sabanin wasu matan dasu baya zuban musu kuma suma virgin ne, ba lallai bane Idan jini bai zuba ba ace mace ba budurwa bace, wata baya zuba wata yana zuba, shi budurci ba daka jini yake ba, yanda kaji cikin mace Idan ka shiga zaka jishi a matse tun daka farko har ciki, wannan shine budurwa, wacce kuma ba budurwa ba koda tayi matsi ana ganewa, domin wajan ne zai matse cikin kuma yana shiga yaji kaman ya fad’a rami, dan haka y’an mata ku daina rud’an kanku kuce AI akwai magani dana miji bazai gane cewa ni budurwa bace wannan maganan karya ne wlh, domin budurci budurcine in kika rasa shi har abada kin rasa shi bazai taba dawowa ba komai zaki ma wajan, domin abun daka Allah ne, kuma budurci shine kimarki wajan mijinki daka yaji ya sameki kofa a bud’e kin bani domin wlh har abada bazai dinga ganin kimarki ba sai dai in a bisa tsautsayi kika rasa budurcinki tayu yaji tausayinki ya d’aga miki kafa, shima ba lallai ba domin in bakiyi wasa ba wata rana saiya goranta miki Indai namiji ne, sai yasa yana da kyau duk wani waje da zaki Indai kin San wajan ba tsaro ki guji wajan Kar ki jaza ma kanki bala’i…….
Yarima tashi yayi dan baya jin dad’in abincin d’akinshi ya nufa ya kwanta, jin karan wayanshi yasa ya d’auka yaga zainab ce kashe wayan yayi gaba d’aya dan baya bukatar magana da ita a halin yanzu………
~haba masoya novel’s din bariki na fito, yanzu dan Allah har sai kun Bari anzo ana tambaya na akan in tura ma mutum novel daka page kaza zuwa kaza???? taya akayi kuka bar haka ya faru plz in an tambaya ku dinga badawa tura ma mutum novel yana mun wuya Wlh, sai inji gwara ma inyi typing da in tsaya turama mutum novel~
NGD SOSAI DA ADDU’A
~ina matukar yinku Sosai Alhmdlh my hrt taji sauki, a rayuwa babu abunda yake min dad’i irin addu’ar da kuke min koda Banyi niyan yin typing ba sai inji Ina son yi muku badan komai ba sai dan addu’ar da kukeyi min daka bakunan ku masu albarka, Ina matukar yinku masoya na one luv~
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
BOOK 2
*PAGE 6*
Y’AR UWA KI GUJI FAD’AMA KAWAYE SIRRIN MIJINKI, BAMA KAWAYE BA HARTA IYAYENKI DA SUKA HAIFEKI KODA KUN SAMI SABANI DA MIJI, KARKI KALAMAN BATANCI AKAN MIJINKI, KICE YA MIKI KAZA YA MIKI KAZA, SAI KIN GAMA BATASHI DAKA KARSHE ACE KIYI HAKURI KI KOMA, BAYAN KIN KOMA KE KINA CAN KUN SHIRYA KUNA ZUBA LOVE DA MIJI, AMMA IYAYENKI NA NAN NA KALLONSHI DA ABUNDA KIKA FAD’A MUSU, Y’AR UWA KI GUJI BATA MIJINKI WAJAN IYAYENKI DOMIN IYAYE BA KOMAI SUKE D’AUKA BA, YA KAMATA KI ZAMA MAI HAKURI DA RUFE SIRRIN MIJINKI INDAI BA ABUNDA YA SABAMA SHARI’A YAYI BA, SANNAN FAD’AMA KAWAYE SIRRIN MIJINKI ZAISA SU RAINA KI SU DINGA MIKI KALLON SAUNA MARA WAYAU, GABA D’AYA ZAMAN AURE HAKURI NE ZOMU ZAUNA ZO MU SABA, SANNAN CIKI BADAN TUWO KAWAI AKAYI SHIBA…….