BARIKI NA FITO 1 & 2
RASHIN SANI
KAWATA HAUWA A USMAN JIDDERH
~ina tayaki murnan kammala novel dinki Mai cike da abubuwa da dama, a gaskiya kinyi namijin kokari wajan rubuta novel din rashin sani, Littafin yayi dad’i Sosai tare da Ma’ana, kin zuba basira a cikinsa Allah ya baki ladan fadakarwa yanda kika gama lfya Allah ya baki ikon Fara wani lafiya~
Bariki ganin yayi rejecting kiran yasa tayi murmushi dan tasan dama inta kirashi baya d’auka sai dai ya kirata koya bari ya tsinke ya kira koya kashe ya kira, minti d’aya minti biyu har biyar Yarima shuru bai kirata ba, d’an murmushi tayi tare da fad’in may be yana wani abune Nasan for sure zai kirani, jiran kiran Yarima tai tayi taji shuru, d’aukan wayanta tayi ta duba time din data kirashi taga wajan 44mnt tace lafiya kuwa? Kar dai ace har yanzu yana fushi ne? Kai no Nasan bazaiyi fushi irin haka ba…. Kara dialing number dinshi tayi taji ance mata switch off, tace haba daman Nasan haka kawai Yarima bazaiki kirana ba, may be yasa caji ne koh yana wani Abun…… wata zuciyar tace ko kuma yana wajan amarya ba, yana zuba mata tsantsar soyayya….. Da sauri ta girgiza kai tare da fad’in no….. Jin ana mata nocking yasa ta Fara fad’in Waye ne?
Muryan habib taji yana fad’in bud’e mana, ba kwarto bane da kike zunduma ihun Waye ne……
Bud’e kofar tayi habib ya shigo ,zama yayi yana fad’in Washhhhh Na gaji, d’anzo ki matsamin baya na
Bariki tsaki tayi tare da fad’in Koba baya ba?
Habib yace eh shi nake nufi…… Ke bama wannan ba wai maiya faru tsakaninki da Yarima ne? Naga yanda yake fushi yana ta gudu dama kaman zai tashi sama, sai yasa Nayi mishi karya ya saukeni Kar yaje ya jefamu kan trailer mu mutu, ban ajiye Mai min addu’a ba, ko d’an auren da mata keyi koda shiga ki fito ne ace kadai taba koshi Nayi ai babu laifi……
Bariki tace Hmmm Allah ya kyauta, tare da fad’ama habib abunda ya faru…….
Habib yace amma da iskanci kike akan wani dalili zaki bama wani dama, ai gashi yanzu kinja ma kanki sai ki nemi mafita, ni naga kaman ma nafi son ki auri Yarima domin in Ina wajan da yake Mai kamun kai nake zama, amma ke in banda tsaban iskanci har kice zaki ga wani kuma kin San da wanda kika je wajan…..
Bariki tace ai ka tsaya ka…….
Habib dakatar da ita yayi tare da fad’in Wlh bariki ban son bura uba, akan wani dalili zaki dinga kaini jinsin da ba nawa?… Gskya banso
Bariki tace kwantar da jijiyoyin cillarka…..
Tashi yayi tsaye tare da kama kugu yana fad’in bariki sanin kanki kin San wacece habiba, wlh banki inyi tsirara ba ni dake mu daku……
Bariki tace ah zauna kawata Ina ni Ina fad’a da babbar kawata Allah ya baki hakuri Hjy habiba ikon god….
Zama habib yayi yana fad’in ah toh in banda iskanci taya zaki dinga had’ani da maza har ki dinga cewa in kwantar da jijiyon cilla ta, ni Ina naga jijiya ni da nake da Fata, ai jijiya sai y’an maza ya karasa maganan yana dariya
Itama bariki dariyan ta saki tare da fad’in nidai Wlh na k’osa Yarima ya turo ayi bikin mu Ina gama istabra’i…..
Habib yace yauwa Ina jinki kina ban labari…..
Bariki tace Hmmm nifa Wlh nace ina son ganin mutumin ne saboda muje tare da Yarima amma Yarima yayi min mummunan tunani, yana ganin inda bai dawo ba a tunaninshi zanje wajan mutumin ne…..
Habib yace Kema maiya kaiki?? Ni Wlh ba tun yau na Lura da wannan Yarima dinba akwai shegen kishi Wlh bariki naga kaman kina wasa, samun Yarima Aliyu ba karamin Sa’a bane, inko kika bari ya kubce miki Wlh kinyi Asara, Kut Aina sha fad’a miki inda ni yace yana So Wlh da yaga yanda ake soyayya amma keda yace yana So kina iskanci, namiji har namiji wlh Yarima ya had’u so handsome…….
Bariki tace uhm, waya ce ina wasa da Yarima?? Ni kam duniyar nan banga Wanda nake jin tsoro ba tare dajin tsoran yasan koni wacece ba sai Yarima Aliyu, Kinga kawata inda bana son Yarima yaushe zan damu yasan koni wacece?
Tabe baki habib yayi tare da fad’in ai gashi yanzu kina kokarin ki nuna mishi halin naki ke gindi babu control daka Kinji ance ana son ganinki kin yarda, Allah yasa ba fushi yayi ba sai yasa ya kashe wayoyin nashi ba.
Bariki tace uhm….
Habib yace kyace uhm mana tunda kin shuka tsiya…… Ni tashi muje muyi rawa ko naji sanyi kwana biyu ban girgiza duwaiya ba…..
Bariki tace wa? Rufamin asiri Aini inka ganni a lahira kaini akayi haka kawai tsautsayi ya kaini Yarima yazo a’a Wlh bada niba wai ance da tsohuwa tayi zina……
Shewa habib ya saki tare da fad’in kunji salo nidai Kinga tunda banda tsayayye balle in takura kaina nayi gaba dan yau sai na karkad’a kayan alatu
Bariki tace nan akafi auki……. Lah mota ta na barta a u/kanawa Wlh Yarima ne ya caza min Kai sai yanzu na tuna,
Habib yace tsiyar y’an mazan nan kenan ai sai yasa ni naki yarda Nayi aure, suna auranka suna kaika ciki ka zama nama, sai yasa nake tatsan su a waje… Ke gaki ko ciki baki shiga ba har an fara miki duk da Kece da laifi
Bariki tace uhm bari in kira ubana na Bariki ince a kulan min da motar ni saida ta zanyi ma gobe inna fita
Habib dariya Ya saki tare da fad’in ni sai naga kaman ma kina kama da mutumin Wlh…..
Bariki dariya tayi tare da fad’in amma Allah ya isa……
Habib fita yayi yana fad’in sai da safe zani wajan wasa
Yana fita bariki tasa ma kofarta key ta kwanta tare da kiran babanta na Bariki ta fad’a Mai ya kula da motar, sannan ta kara da fad’a Mai Yarima zai zo jibi dan neman izinin zance….. Tace Bari koma dai miye gobe mayi magana in nazo Abba.
Driver din alh madu koda ya koma abunda bariki ta fad’a haka Ya fad’ama Mai gidan nasa,.
Alh madu dariya yayi tare da fad’in yaro man kaza, yaro yaro ne yaro bai San wuta ba saiya taka, lallai Bariki har yau baki San Waye alh madu ba, amma naga kina son in fito in nuna miki Waye ni dan naga kanki yana rawa very soon zanyi maganin ki, sannan Indai bani zaki aura ba sai dai mu zauna muci gaba da mu’amala yanda mukeyi, dan bazaki aura kowa ba inba niba.
D’aukan wayanshi yayi ya doka ma Hjy babba kira, duk da yasan ba lallai bane ya d’auka domin tun dazu yake ta kira bai d’auka ba, harya kusa tsinkewa aka d’auka……
Hjy babba ya d’auka tare da fad’in Allah ya taimaki Sanata alh madu daka majalisan dattawa sai Villa insha Allah
Alh madu yace kana ina duk inda kake kazo yanzu sannan ina son kazo min da bariki kota wani hali kafarka kafarta yau nake bukatar ganinta cikin daren nan a guest house dina ……
Hjy babba yace an gama ranka ya dad’e yanzu zaka gammu
Bayan alh madu ya kashe wayan, hjy babba yace Toh fah hala bariki ta kara Karta Mai rashin mutunci ne Bari inje d’akinta inji y’ar bura ubar itama har mota ya bata ita da bata iya cin arziki ba inda Tana mishi yanda yake so Aida tafi karfin abunda yafi wannan motar duk da tace baida kayan aiki abu kaman ayabar yara kona jarirai ne tace ma oho ni na manta….. Gaba yayi tare da nufa d’akin bariki data fara bacci nocking yaita mata da karfi…….
Tashi tayi tare da sakin tsaki tana fad’in Waye ne??
Muryan hjy babba taji yana fad’in nice bud’e kofar
Bariki tashi tayi ta nufi kofar tana murza ido, bud’e kofar tayi taga hjy babba dinne tace lafiya cikin wannan daren???
Hjy babba yace lafiya mana, ko 12 bai karasa ba kike cewa cikin wannan daren sai kace nazo miki da karfe biyun dare, Kinga ni bama wannan ya kawo niba, nazo ne muje wajan alh madu dake yanzu ya kirani yace yana son ganinki dan Allah shirya muje……