BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Koda Yarima Aliyu ya d’auki wayarsa yaga message din da aka masa, karantawa yayi tare da dan sakin tsaki a hankali ya furta Kalman I hate u, saboda ke yasa banga fuskan da nake burin gani ba, karan wayan ne ya kara shigowa dubawa yayi yaga lil sis, d’auka yayi fuskanshi dauke da murmushi yace Hafsat how far? Tace not too far gani na dawo gida, yace haba zo in ganki lil sis, dariya tayi tace bros ban dawo ba har yanzu Ina kaduna sis Fatima ta hanani dawowa, plz kazo gobe ka tawo dani bros, yace OK zan gani in zan iya zuwa, tace plz bros kaine kawai zaka zo ta yarda in dawo, murmushi yayi tare da fad’in ina nan tafe toh insha Allah, cikin jin dad’i tace that may bros I love you so much. Kashe wayan tayi tare da fad’in lil rigima, Aliyu yafi sabawa da Hafsat kaf cikin y’an uwanshi kodan ita kanwarshi ce oho, wanka yayi yasa kananan kaya yayi kyau Sosai fita yayi fadawa suka bishi sashin mum dinshi ya nufa inda ya sameta ita da jakadiya suna magana kuma duk akan maganan bikin nashi ne, zama yayi akan kujeran falo din, yace Barka da wannan lokacin mum, tace yauwa my son, muna nan muna ta tsara yanda bikinka zai kasance, murmushin Ya’ke yayi, jakadiya tace gaisuwa Magajin sarki, kai ya d’aga mata alaman ya amsa, kallon mum yayi tare da fad’in mum ya kamata in fara aiki a hospital dina, mum tace toh kaine ai Aliyu babu abunda ba’a saba amma kaki bud’e asibitin, yace cikin week dinnan nake gani ya kamata in bud’e, mum tace ko kaifa, yace gobe zani kaduna zanje d’auko lil sis, daka nan zan biya in ‘kara ganin hspt din, mum tace hakan yayi zadai kaima Fatima tsiya, zaka d’auke mata Hafsat, yace mum haba yau wajan satinta biyu a can fah aita Mata kokari, mum tace Kunfi kusa Allah yasa ta yarda ku tawo taren dariya yayi wanda ya kara fito mishi da kyanshi yace zan tawo da ita, mum tace toh yanzu Mai kake gani ya dace Ayi a bikin ka? Jin mum ta kawo maganan aurenshi yasa ya tashi tare da fad’in mum Inna dawo daka kaduna sai muyi maganan, mum tace toh shikenan fita yayi dan baya son wani maganan bikin shi.

Washe gari wajan karfe 1 bariki ta fito da d’an karamin akwatin ta, yau dressing din da bariki tayi yaba ma kowa mamaki domin wando tasa saita saka hijab, abunda basu taba ganinta dashi ba kenan hijab, habib ne yazo ya tare ta, yace Mai zan gani haka? Oh ikon Allah bariki wani ustazun kika samu haka? Hararanshi tayi tare da fad’in maika gani? Yace naga kinsa hijab kin rufe komai, tace naga tunda na fito ake ta kallo na ashe dan nasa hijab ne, kaida gulma take cinka a tsuliyarka shine saida ka fad’a abunda ke cikinka, yace Wlh bariki zan miki bura uba, damme zaki dinga kaini jinsin da ba nawa ba, Kina wani cemin kai y’ar ke dince ba zaki iya fad’a ba, tace ni ba wannan bane a gabana muje karaka ni bakin titi inhau mota, yace muje mi’ka Mai akwatin tayi tace dan taimaka min mana, tsayawa tayi tare da fad’in taya ina mace zaki ban Abu Mai nauyi sallan in d’auka ya bud’ani in rasa d’an budurci na a’a bada niba, bariki dariya take Sosai tare da fad’in wani budurcin bayan an gama bulaki, habib yace wa Rufamin asiri in mutu maza su kaini, yace ni baki fad’amin inda zaki ba, tace Wlh zanje wajan wani saurayi nane gobe zamu bar kasar, habib yace shine babu sallama? Tace tafiyan na sirri ne shiya sa, tabe baki yayi sukaci gaba da tafiya har bakin titi kiranta akayi a waya Wanda yasa ta d’auki wayan tana magana, dai dai lokacin motar su Yarima Aliyu tazo wucewa, baka jin karan komai saina jiniya ga fadawa sun ri’ke bulala, jin karan jiniya din yasa hankalin bariki yayi kan titi din, Yarima Aliyu yana mota yana karanta news paper kaman ance ya d’ago idonshi ya sauka akan bariki wacce take waya tana murmushi……

~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
RIGAR K’AYA FANS GROUP
wannan page din naku ne ina jin dad’in comment dinku gaisuwa gareki sis hauwa

                 *PAGE 6*

Gabanshi yaji ya fad’i domin sak yarinyar da yake gani a mafarki, dan irin jikinta da yake gani, gashi yau dinma cikin hijab take bai san lokacin da yace ma driver dinshi su tsaya ba, driver din tsayawa yayi ganin motar da Yarima yake ciki ta tsaya yasa sauran motocin da suke binshi suma suka tsaya, bai jira Sun bud’e Mai motar ba dakanshi ya bud’e kofar, koda ya fita baiga bariki ba bai ga Mai kama da ita ba, d’an shuru yayi yana d’an tunani kodai imagination ne nakeyi, kai ya girgiza kai no ita na gani lumshe ido yayi yana ganin fuskanta tana murmushi, yayi wajan minti biyar a tsaye a wajan sannan ya shiga mota suka fara tafiya, gaba d’aya yarima Aliyu ya rasa mai yake mishi dad’i toh mai yake damunshi? Kai Anya kuwa? Ban yarda ita bace gizau ne kawai inda itace sanda na fita Aida na ganta, wannan tunanin da yayi yasa yaji cewan ba ita bace kawai imagination ne

GARIN ABUJA

Magajiya jummai ce zaune a wani dangareren falo, da alama tana jiran fitowan Mai gidan ne, tayi a kalla 30mnt tana jira saiga wata mata ta fito kallo d’aya zaka ma matan kasan babbace a kalla zata Kai 40yrs, matar cikin wata jallabiya mai shegen tsada ga hannunta sun sha zobunan zinari, ganin matan tana nufo ta yasa magajiya jummai ta mi’ke tsaye tana fad’in Barka da fitowa Hjy, matar murmushi tayi tare da fad’in zauna mana magajiya, bayan magajiya ta zauna matar tace kwana da yawa? Magajiya tace Hjy Habiba Wlh kuwa tun sanda mukai waya kika ce zaki nemeni, Hjy Habiba tayi murmushi tace Wlh kuwa magajiya kin san kiran da nayi miki akan matsalata ne, magajiya tace har yanzu Hjy habiba wannan matsalan bata kawar ba? Hjy habiba tace Hmmm kedai Bari Wlh abubuwa sun jagule, ina tsoran hulda da naza Wlh kwanaki saura kad’an Asirina ya taunu, magajiya tace garin ya hakan ta faru? Hjy habiba tace Wlh muna cikin d’aki nida yaron da kika had’ani dashi muna tsaka da soyayya saiga Mai gidan ya dawo, kuma bai fad’amin zai dawo ba ranan, jin kaman karan an rufe kofa yasa na tashi da sauri na bud’e kofa na hangoshi yana haurowa, da sauri na boye yaran cikin wardrobe, koda ya shigo ina mishi oyoyo kallona yayi yace lafiya kike zufa haka? Nace mishi banda lafiya ne bai san zufan cin ayaba bane, magajiya tace Kai kin tsallake Rijiya da baya, Hjy Habiba tace Kedai bari, yanzu kiran da nayi miki na yanke hukunci zan daina mu’amala da maza dan wata kawata taban shawara akan in fara hulda da Mata, Kinga duk namijin da yaga mace bazai maka zargin komai ba, magajiya tace hakane Hjy amma zaki ji dad’in macen kuwa? Naga da maza kika Fara, Hjy habiba tace toh ya zanyi miji ne Allah ya baka ga tarin dukiya ga komai amma babu kayan aiki, ni kuma gani mabu’kaciya ce, magajiya tace gaskiya Indai miji baya gamsar dakai ai gara ka nema ma kanka mafita yanzu dai tunda kin bar harkan Maza zan had’aki da yarinya d’aya, inna koma yau gobe zata tawo, Hjy habiba tace a’a yanzu driver zai tafi dake sai ya tawo min da ita, sannan dan Allah ban son kazama Mai tsafta nake so, magajiya tace karki samu damuwa zan baki Mai tsafta, bayan ta sallami magajiya da kudi mai yawa tare da atamfofi da less sannan tasa driver ya kaita, koda magajiya ta koma garin kaduna Haulat ta had’a driver dashi suka koma garin Abuja.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button