BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Hura mata iska yayi a fuska wanda yasa ta bud’e ido da sauri idonsu ya had’e suka fara kallon juna, cikin ido gaba d’ayansu wani irin son junansu suke ji, Sun d’auki lokaci suna kallon juna Kafin bariki tayi k’asa da kanta dan bazata iya juran ci gaba da kallonshi cikin ido haka ba, wannan dinma da tayi tana mamaki, ta rasa mai yasa Yarima ya banbanta da sauran maza, yana Mata wani irin kwarjini da bata ji akan sauran mazan da tayi hulda dasu,…..

Katse mata tunani Yarima yayi tare da fad’in daka ina habib ya kiraki Ina kika je?

Cikin sanyin murya tace ina gidan wata kawar innata ce, naje amso maganin ciwon kai na Hausa, Ina can habib yazo, nama bar wayata a gida tana caji…..

Yarima yace ok but yaushe zaki koma Gida? I dnt knw why bana son wannan anguwar domin mutanan da nake gani a cikinta, plz ban son kina yawan zuwa my princess ya karasa maganan cikin damuwa….

Tace Yarima Karka manta y’an uwana suna nan

Yace eh I know, bawai nace ki daina zuwa bane, kawai Ina so ki rage zuwa ne plz, and my princess plz ki daina irin wannan dressing din, sai a gida na, ki dinga sa hijab dinki inso samu nema harda nikaf plz banso kowa yana ganinki …..

Bariki murmushi tayi tare da fad’in Yarima wannan jallabiya ce babu komai ai dan nasa, shima kaman hijab ne…..

Yarima yace, Nop akwai banbanci nidai bana so ana sawa, Kinga yanda yayi miki kyau kuwa? Only god knows maza nawa kika burge da kika fito…. Sai yasa tunda yau naga Abba Yaban izini very soon za’a turo ayi bikin kowa ya huta in kika zama tawa sai inga Wanda zai kara cewa yana son ganinki…….

jiya saida Nayi typing har 2read more komai nawa ya goge na whatsapp ???????????????? ol my chats yanzu ma saboda nacin my mum my salmaty yasa dole nayi typing dinnan, plz duk Wanda sukai min magana ban basu amsa ba suyi hakuri Wlh komai nawa Ya goge in important magana ne zaku iya Yimin resending message din pls, nayi bayani ne Kar a kaini gaba ace in anyi min magana bana kulawa, maryam ba haka take ba, kowa nata ne thanks

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 8*

Bariki dariya tayi, tana mamakin irin kishin Yarima Aliyu, gashi baya iya boye kishin shi, dole saiya fito dashi……

Katse mata tunani yayi da fad’in dariya koh??

Tace a’a Yarima kawai naga kana tunanin daba haka bane…..

Yace miye ba haka bane? Tell me, tunda kika fito zaki cemin maza basu kalleki ba??

Tace Yarima yanzu fah dare ne Waye zai kalleni? Inba Kai ba.

Murmushi yayi tare da girgiza kai yace my princess you r too much kin iya Kare kanki….. Anyway yaushe kike son Ayi bikin mu?? Domin Idan Mai martaba ya turo lokaci kad’an za’a sa.

Bariki rufe fuskanta tayi cikin jin kunya tace Yarima BANDA ZABI sai abunda su Abba sukace…..

Yarima Aliyu yace hakane but Nasan Kema kina da lokacin da kike so ayi in muka shirya basai mu fad’a ba!?

Tace hakane

Yarima yace ni ko yanzu aka bani zan tafi dake…..

Ido ta zaro lokaci d’aya kuma ta saki dariya Sosai, tace Yarima ni nafi son yakai Nanda shekara d’aya…..

Da sauri Yarima yace what?? Amma dai you are joking koh? Ni bamma tunanin yakai nan da wata d’aya….

Bariki tace Yarima watsa d’aya yayi wuri, ni Ina tunanin nan da wata uku….

Yarima yace hakan yayi miki???

Kai ta d’aga alaman eh, domin Kafin nan ta Gama istabra’i sannan zata samu lokacin gyara kanta Sosai duk da tasan komai tayi bazata dawo budurwa ba, amma zata gwada duk wani kayan gyaran jiki danta d’an gyara kanta…..

Katse mata tunani yayi da fad’in gobe ki koma Gida Zanzo in ganki a can da rana insha Allah,

Tace Yarima gobe kuma?

Yace yes ko you don’t want to see me ne?

Da sauri tace a’a kawai naga kullum sai kazo, baka zama ga amarya a gida, inaga ya kamata ka zauna ka bata hakkinta, da lokacinka

Yarima yace ok hakane, zan zauna bazan zoba har sai kin nemeni, sannan ita amarya Ai tare muke kwana da ita…..

Ganin yanda ta canza fuska yasa yayi murmushi danya Lura taji haushin magananshi ne…..

Kamo hannunta yayi tare da matse su duka biyun, yace my princess I love you so much, plz ki dinga kulan min da kanki Sosai…

Kallonshi tayi ganin shima ita yake kallo yasa tayi k’asa da kanta, cikin sanyin murya tace Yarima……. Shuru kuma tayi tana jin nauyin abunda zata fad’a…..

Yarima Aliyu yace ina jinki my princess…..

Hawaye ne ya zubo mata Mai zafi da sauri tayi k’asa da kanta dan karya gane tunda hannunta na nashi hannun….. Cikin rawan murya tace Yarima Idan ka aureni kaji ba yanda kake expecting ba zaka iya saki na????

Yace ban fahimta ba?? Mai kike nufi?

Tace Yarima Ina nufin Bayan auren mu kaji ba yanda nake ba I mean….. Shuru kuma tayi lokaci d’aya tasa kuka mai sauti……..

Yarima ido ya kura mata cikin rud’ani…… Tare da tunanin mai take son fad’a mishi haka???? Ganin kukan nata na k’aruwa yasa ya fara share mata hawaye cikin tausayinta……. Ya fara magana kamar haka Zainab Ina son ki fad’amin abunda yake damunki ko miye I will accept you a yanda kike, ina miki so dani kaina ban taba tunanin zanyi ma d’iya mace irin wannan son ba, tell me maike damunki????

Kasa magana tayi sai kuka da take ta faman saki cikin tashin hankali da damuwa,….

Yarima kam ido ya kura mata ganin taki magana sai kuka,… Yace Zainab kodai kina pretending ne bakya so na…….

Da sauri tace a’ah Yarima Ina Sonka, kaine rayuwa na, Ina maka son da baki bazai iya fad’anshi ba, sonda nake maka sai yasa nake tsoran fad’a maka abunda nake son fad’ama a halin yanzu saboda ban San yanda zaka d’auki abun ba……

Katseta yayi tare da fad’in Zainab tell me?? Fad’amin Mai yake faruwa?? ……plz Zainab tell me abunda yake damunki kin sani cikin damuwa……

Kuka take Sosai lokaci d’aya ta fad’a jikinshi ba komai take son fad’a mishi ba sai rayuwarta wanda tsoro da fargaban abunda zai biyo baya yasa ta kasa fad’a mishi sai kuka tare da nadama

Yarima tunda ta fad’a jikinshi ya kasa furta koda kalma d’aya ne sai Shafa mata baya da yakeyi tare da tunani Kala Kala akan Mai take son fad’a mishi?? Lallai akwai wani abu mai muhimmanci daya danganci rayuwarta da take fargaban fad’a mishi, to miye abun??? I need to knw, tunanin baya ya farayi tasha son fad’a mishi magana amma saita kasa, lallai akwai wani abu a tare da ita toh miye wannan abun?? I have to find out……..

D’agota yayi tare da fad’in Zainab kukan ya isa haka, what I want you to knw is dat Ina sonki I cnt live without you…… Zainab tun a mafarki Allah ya had’ani dake har na had’u dake a zahiri, ina son ki sani had’uwa na dake had’in Allah ne, na Fara sonki tun Kafin inga Fuskanki, ina son ki sani bawai saboda kyanki ko wani abu nake sonki ba a’a kamalanki da mutunci da yanda kike suturta jikinki yasa na kara sonki koda na had’u dake…… So Zainab dnt be afraid to tell me what in ur mind….. Zainab Abu d’aya zaki aikata in barki duk irin sonda nake miki domin bazan iya juraba dan Indai zan ganki Abun zan dinga tunawa shine ZINA duk da Nasan rasaki a rayuwa ta kaman baraza na ne a tare da rayuwa na, bana tunanin koda a mafarki Zaki iya aikata hakan, ina matukar kishinki Sosai harta habib da kike mu’amala dashi hakuri nakeyi badan ina so ba, tunda kince kaman dan uwanku ne, ban son inga wani abu yazo inda kike Inba niba…….. Ido ya kura mata tare da fad’in tell me wht on ur mind I need to knw……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button