BARIKI NA FITO 1 & 2
Yace no mum Bari in sauketa
Babu yanda hjy habiba ta iya, dole farhan da haulat suka fita.
Haulat na gaba farhan na mazaunin driver, ta kalli farhan tace plz mu biya ta gidan Hjy Umaima zan amsa sa’ko…….
Farhan yace ok, amma zaki missing train din 8, sai na 10 zaki hau,
Tace babu damuwa
Juya motar yayi sukai gidan Hjy Umaima, haulat ce kad’ai ta shiga….. Ta d’an jima Sosai ban San mai suka tattauna ba sai gata ta fito ta shiga motar ta kalli farhan tana y’ar murmushi wanda shima din ita yake kallo tace muje…..
Mai yakon suje din saiya kama hannun Haulat yana fad’in haulat dagaske aure za kiyi????
Tace aure kuma? A’a
D’an shuru yayi yana nazari, toh tace a’a Bayan mum dinshi tace aure za’a Mata…..
Katse Mai tunani haulat tayi da fad’in, farhan zanyi aure Indai na samu Mai sona kuma wanda nake so, da an taba son had’ani da wani Wanda bana so….. Wanda shine silan fad’awa ta cikin k…… Da sauri tayi shuru domin taso tayi baran barama.
Farhan yace inaji haulat
Tace andai fasa auren nawa
Wani irin ajiyan zuciya farhan ya sauke, tare da kallonta cikin ido yace haulat zaki aureni???
Da sauri ta kura Mai ido, tare dajin bugun zuciya, lallai farhan ya had’u ba tun yau take sonshi ba, tunda ta Fara ganinshi, domin yanda yake nuna mata kulawa, wanda ko wace mace tana son taga ana nuna mata caring….. Sau da yawa rashin nuna halin ko in kula da maza suke nuna ma matansu suke sa su Fara neman mata y’an uwansu, misali namiji ya fita office, ko kasuwa, kodai wajan da yake Sana’a, bazai kiraki ba, may be in kin kirashi bazai d’auka ba, namiji inya auri mace babu kalaman love duk sai ya daina, in baki da lafiya babu sannu koya jiki, inya biya kud’in magani shikenan, maza kuma kuna da laifi Sosai wajan fadawan wasu matan halaka, mace tana son Mai kula da ita Sosai, yau koda auren dole akama mace bata son miji….. Indai yana kyautata mata wlh sai kuga ta Fara sonshi….. Amma kai miji babu kyautatawa daga tayi abu sai hantara…… Idan tana da k’awa taga tana kyautata mata in bata da lafiya, bini bini ta kirata tana ya jiki kaza da kaza, in kawar Tana bin mata haka zatai ta janta a jiki in aka samu Mai raunin imani ganin yanda kawar tata take mata inta fito mata da kudirinta saita yarda ta amince Mata…… Wlh maza kuma kuna da laifi Sosai, damme bazaka dunga nuna ma matarka soyayya da kulawa ba,bayan aure shikenan daka anyi aure sai a fara d’aure fuska haba haba maza ya kuke haka, sannan saika gama d’aure fuska in dare yayi ka lallabo kana Kai hannu ko kunya babu????……..
Farhan ne ya Katse ma haulat tunani da fad’in…. Haulat why r you silent and stare at me lyk this????
Murmushi tayi tare da fad’in nothing, kawai Ina mamakin abunda kace ne……
Farhan yace mamaki kuma? Kodai bazan samu karbuwa bane? Haulat tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki, Wlh haulat so nake na aureki inhar kin amince Kece mace ta farko dana Fara ji ina burin in aura…….
Haulat wani irin murmushi ta saki tare da fad’in farhan zanyi tunani akai, yanzu dai muje train station Kar in makara…..
Tada motar yayi suka wuce kabuwa station, koda suka je saida suka zauna bayan yasai mata ticket, zama sukayi suna jiran lokaci,
Haulat ba komai take tunani ba, sai abunda suke aikatawa da hjy habiba, Uwar farhan gashi d’anta yau yace yana Sonta, in kuma tace bata son farhan tayi karya, tashin hankali uwa da d’a……. Ido ta lumshe tare da fad’in Anya wannan abun zaiyi kuwa? Maganan farhan bai kamata in daukeshi da muhimmanci ba, domin ba Abu bane mai yihuwa naga tsiraicin mum dinshi na cita….. Yanzu kuma sai kawai inzo in auri d’anta Kai no way…….
Farhan ne ya Katseta tare da fad’in when zaki dawo? Koni inzo kaduna?
Dariya tayi tare da fad’in mudai yi waya kawai….. Dai dai lokacin aka fara fad’in su tashi train yazo…..
Tashi haulat tayi tana kallon farhan tare da fad’in sai munyi waya
Kai ya d’aga alaman ok tare da bata Wani karamin Leda daya ciro cikin aljihun shi,
Amsa tayi tana fad’in ngd tare da tafiya….. Koda haulat ta shiga jirgi tunanin farhan tai tayi wanda ta rasa dalili…….. Bud’e ledan daya bata tayi taga wani kwali karami anyi raping dinshi bud’ewa tayi taga wani zoban zinari Mai shegen kyau, bata san lokacin data saki murmushi ba……..
Yarima Aliyu ne zaune gaban iyayenshi yana mi’ka musu gaisuwa, mai martaba yace yaushe zaka Fara aiki a asibitin ka?
Yarima Aliyu yace Abba duk sanda ka bani umarni Niko yau zan iya Fara aiki….
Mai martaba yayi murmushi domin duk cikin yaranshi babu wanda yake so kaman Aliyu bawai dan yana d’a namiji ba kawai, a’ah harda irin biyayyan da yake mishi… Mai martaba yace saika shirya cikin satin nan ka Fara sannan akwai wani fili da nake dashi a u/sarki saika Fara ginawa tunda a can zaka Fara aiki, Nasan wata rana iyalanka zasu bika can din in aiki yayi yawa …….
Mum din Yarima tace Kai Masha Allah, ina taya Yarima godiya
Mai martaba murmushi yayi tare da fad’in kin ara bakinshi kenan kinci Mai Albasa
Yarima yace Abba na gode Sosai Allah ya kara girma, Allah ya biya dan gidan Aljanna
Mai martaba ya amsa da Ameen tare da fad’in waziri zai baka takardun filin sannan zai nuna maka filin,
Mum dinshi tace sai ka Fara ginin mata biyu koh?
Yarima kasa magana yayi, sai mai martaba da yace ginin mata biyu kuma? Aure yace miki zai K’ara?…..
Mum tace eh gashi nan ya fad’a maka da bakinshi….
Mai martaba ya kalli Yarima Aliyu tare da fad’in ina jinka??
Yarima ya fara magana da fad’in Abba dama dama akwai dama….
Murmushi mai martaba yayi tare da fad’in dama me? Gaba d’aya ka kasa magana, mai martaba yaci gaba da fad’in Aliyu inaso ka sani bazan hanaka k’arin aure ba, amma sai dai Ina Mai baka shawara kayi hakuri nan gaba domin baka dad’e dayin aure ba ko sati d’aya bakayi dayin aure ba, inaso kayi hakuri nan gaba kad’an sai a taso da maganan auren da kake son yi, amma fah shawara ce ba umarni ba…..
Yarima Aliyu yace Abba umarni ko shawara duk abunda kace min a matsayin umarni yake a wajena…. Abba kayi hakuri a kullum nafi son kaban umarni domin Ina Mai biyayya ga duk wani abunda kacemin
Mai martaba yace Allah yayi maka albarka, kaima Allah ya baka masu yi maka biyayya
Yarima ya amsa da Ameen Abba,
Mai martaba yace yarinyar y’ar inace????
Yace Abba a cikin kaduna suke, a u/kanawa ,sannan Abba mahaifinta bamai karfi bane….
Mai martaba yace babu damuwa, ya tarbiyan gidan yake??
Yace Abba Alhmdlh gidan akwai tarbiya domin yarinyar yau kwana hud’u data sauke AL’QUR’ANI Mai girma kuma hadda….
Mai martaba yace Alhmdlh, lallai gidan akwai tarbiya, Allah yasa na tsoran Allah ne sannan duk Wanda yake da ilimin addini yaji dad’in duniya da lahira zai iya zama da kowa, dukiya ko mukami bashi bane Abun dubawa tarbiya itace Abun dubawa, kaje zansa Ayi bincike akan gidansu……
Yarima tashi yayi yana mai yima mahaifin nashi godiya sannan ya fita cikin murna yana K’ara godema Allah da har mahaifinshi ya yarda yanzu tunda Mai martaba ya amince toh ya Gama samun Zainab insha Allah, lallai Allah Abun godiya bai taba tunanin zai samu amincewan mahaifin nashi cikin sauri haka ba…… Gefenshi ya nufa na da, koda ya shiga rufewa yayi tare da nufa bedroom dinshi ya fara kallon hotunan Zainab din, Wanda ya zana, tunani ya farayi Mai Zainab take son fad’a mishi wanda take tsoron fad’a??? Kodai in tambayi habib?? Nop bai kamata ba ita ya kamata ta fad’amin koma miye, and d way yanda take kuka yana nunamin abunda take son fad’a Kaman ya shafi rayuwanta? Toh mai take son fad’amin ido ya lumshe yana tunani….. Na farko dai bata da wani aibu balle yace ga abunda take kokarin fad’amai, to Mai Zainab take boyemai??……. Kai ban tunanin abun serious ne inda serious ne data fad’amin…. Wata zuciyar tace mishi kaika sani ko nauyin Abunne yasa ta kasa fad’ama? And kuma Inba serious bane mai yasa take kuka haka in tayi kokarin fad’a Mai? Ganin duk iya tunanin da yayi ya kasa gano komai yasa ya cire abun a ranshi tare da fad’in koma miye Indai Mai muhimmanci ne zai sani, yanzu dai ya kamata in mata surprise inje in ganta….