BARIKI NA FITO 1 & 2
Bariki na kwance taji ana mata nocking, tashi tayi ta bud’e kofar da sauri ta saki kara tare da rungume haulat Tana fad’in mutanan abuja sai yau, ko waya babu…..
Dariya haulat tayi tare da fad’in kiyi hakuri bariki Wlh wayata ce ta fad’i bani da number d’inki yanzu, sai yasa ina dira kaduna Wajanki na fara zuwa Kinga ko d’akina banje na ajiye akwati ba nazo Wajanki…..
Bariki tace shigo mana
Haulat shiga tayi tare da zama tana fad’in Kai nasha abuja
Bariki tace gashi kin kara kyau da k’iba kaman bake ba, kai zama waje d’aya yayi
Murmushi Haulat tayi tare da fad’in dan bani wayarki in tura hotuna na tare da number d’inki, banda pic dina dake ko d’aya a phone dina
Bariki mi’ka mata wayar tayi tare da fad’in yunwa nake ji wlh Bari in duba habib
Haulat tace ok, haulat ta d’auki abunda take so cikin wayar bariki, sannan tayi murna da abunda ta samu a game da bariki din……
Bariki bata dad’e Sosai ba ta dawo, cikin d’akin tare da fad’in habib ya cika yawo kaman yaci kafan Kare…. D’aukan iPhone dinta tayi ta Fara kiran habib harya tsinke bai d’auka ba……
Haulat tace ashe kinyi iPhone ga Samsung ga iPhone gskiya bariki kina jin dad’i…. Tashi haulat tayi tare da mi’ka ma bariki wayarta Tana fad’in Bari inje inyi wanka in huta anjima nazo
Bariki tace ok but nima zanyi tafiya sai dai munyi waya
Haulat tace ok tana murmushi ta fita
Bariki ganin data dinta a bud’e yasa ta shiga whatsapp da message keta faman shigowa ganin Alh madu ya mata message yasa ta bud’e nashi ganin hotunan daya d’aukesu tayi, tsaki taja tare da shiga gallery ta goge dan in an turo Mata hoto shida kanshi yake bud’ewa bata rufe ba, harda na Hon salis duk ta goge su Wanda ya tura mata kwanaki, duk wani hoto data d’auka wanda bai dace ba ta goge a cikin wayarta…… Kiran Alh madu ne ya shigo cikin wayarta kaman Karta d’auka saita tuna da hotunan daya turo Mata Wanda hakan ya tabbatar mata yana son Mata wani tuggu sai yasa ta d’auka tare da fad’in lafiya?
Dariya yayi tare da fad’in hotunan sun d’auku da kyau koh?
Tace tir da hali irin naka
Yace na baki awa biyu kizo inda nake ko yanzu ki ganki a internet ansa hotunan da mukayi kuma da fuskan wani ba nawa ba danna biya kud’i anyi min aikin , babu wanda zai gane an canza fuskan domin kwararru sukamin aikin kuma ba y’an kasar nan bane…..
Bariki k’asa tayi tana hawaye wayar ta sulale a hannunta……
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
BOOK 2
*PAGE 10*
Kuka take Sosai tare da nadaman fadawarta bariki, wanda ita da kanta tana mamakin yanda har ta fad’a wannan mummunan harkan, yanzu kenan kowa zai iyayi mata barazana kenan? Duk yanda taso ta kimtsa kanta sai an gwadayi mata barazana?…… Share hawayenta tayi lokaci d’aya ta saki murmushi tare da shiga toilet tayi wanka tasa dogon wando da hijab, sannan ta d’auki akwatinta ta fita, u/kanawa ta Fara zuwa ta ajiye, bata sami abbanta na Bariki ba sai ummanta na bariki dan haka tace mata bari taje ta dawo.
Bariki direct gidan Alh madu ta nufa, bayan ta karasa ta sallami mai keke sannan ta shiga cikin gidan Kai tsaye….
A falo taga Alh madu
Ganin bariki ta shigo yasa ya tashi yana fad’in dama Nasan zaki zo, nasan dole kizo…..
Bariki ta dakatar dashi tare da fad’in Zanzo for sure, gani nazo Mai kake bukata??
Yace ke nake bukata tare da d’aga mata gira.
Bariki tace ni kake bukata??…. Wani irin dariya ta saki lokaci d’aya kuma ta gimtse fuska tare da fad’in amma wasa kakeyi koh?? ….. Ina tunanin ka manta wacece bariki shi yasa kake kokarin Sani abunda Banyi niya ba…. Kasan Mai yasa nazo???…. Kai a tunaninka saboda ina tsoran ka tura hotona a internet yasa nazo? Never…. Karka manta bariki ake kirana miye danka watsa hotona a internet?? Miye a ciki? Kai a tunaninka dan kasa hotona a internet zanji wani abu?? Dariya ta saki tare da fad’in u r wrong duk yarinyar data baro gidan iyayenta ta fito tana zaman kanta kai a tunaninka dan kasa hotanta da namiji tsirara zata damu??? Aini Idan kasa aka watsa a internet plz kasa a had’a da number dina May be in sami Mai babban ayaba ba irin naka ba na Wasan yara, SANATA ALH MADU….. kana son buga wasa dani tunda ka Fara sai mun buga….. Karka manta bariki ba y’ar Siyasa bace, bariki ba Sanata bace bariki bamai mukami bace….. Face karuwa Mai zaman kanta wacce take aikata komai dan ta sami duniya….. Yau Idan ka d’aura hotona a internet koda ace nice banda kaya a jikina suna zaka samamin zaka sa in sami yawan masoya masu son sex dani, Kaga may be Turai ma su kirani susa inyi blue film a Biyani….. But amma abunda nake tsoro shine inkai ka rasa kujeranka na Sanata……..
Da sauri yace enough don’t you dare say something like that in your life again in front of me……
Dariya tayi tace why?? I thought mulkin farar hula muke kowa Nada y’anci koka manta ne??? Ba nazo wani dogon surutu bane ko turanci ba….. Am hare to warning you, ka fita harka na ,nasha ko d’an Siyasa kaman distinguish senator yana da tunani da basira, ashe ba haka bane….. Oh na tuna abun ya had’e da tsufa dariya ta saki mai sauti sannan tace ga kuma son duniya…. Wlh harna tausaya ma al’umar da kake wakilta basu San tsohon banza suka tura…… Tas ya wanke fuskanta da Mari tare da Jefata kan kujeran falon
Bariki tace u slap me?? Kara mata wani Marin yayi…. Yazo zai kara mata wani tayi wuf ta ri’ke hannun amma karfin mace dana miji ba d’aya ba ya kwace hannunshi tare daja mata hannu yayi bedroom dinshi da ita, yana shiga ya Jefata kan gadon d’akin….. Sannan ya kalleta yana wani huci kaman wanda yayi aikin karfi….. Yace zan nuna miki ni tsohon banza ne, zan ajiyeki a nan har karshen rayuwarki inyi ta cinki sai dai ki mutu y’ar iska kawai…..
Dariyan da bariki ta saki ne, shine yasa ya kura mata ido, tace amma kayi hauka koh?? Ina tunanin Bayan tsufa da toshewan basira ka Fara tabuwa, Bari kaji Kafin inzo inda kake saida na shirya ma, ka d’auka haka kawai Zanzo ba tare da wani shiri ba???? Toh inma haka kake tunani Toh ka daina…… Karka manta dazu ka kirani duk abunda ka fad’a nayi recording, sannan ka turamin ainiyin hotan da ka d’aukemu nida kai, Kaga in kasa an canza wancan zan karyata ta hanyar tura Wanda ka turamin wanda fuskanka ne akai tare da tura recording din da nayi kake ta surutai akan kasa a canza fuska…… D’an shuru tayi tare da kallonshi ganin yanda ya d’an tsorata yasa taci gaba da fad’in Kaga in nasa nawa Nima k’imarka da siyasan ka ya zube…… Madu ina son ka sani bana son bata maka suna amma kana ingizani, are you not are shame, nace na daina harka da maza aure zanyi amma kana son dole saina ci gaba dayi, inaso ka sani daka yau shine rana ta karshe da zaka sake yunkurin shiga al’amari na, zan iya fasa auran da zanyi kaifa zaka iya yarda ka rasa kujeranka???….. Ganin Alh madu ya kasa cewa komai yasa ta Fara kokarin fita har takai bakin kofa ta tsaya tare da waigowa tace ina maka fatan shiriya domin mutuwa ci take kaman rana, a shekarunka yanzu babu abunda ya dace dakai sai istigfari domin neman gafaran Allah dan an bata y’ay’an mutane da dama, kaima ka jira Kaga abunda za’ayi ma naka da yardan Allah…… Fuuuuu ta fita tabar gidan, tafiya take tana kuka a kafa tare da takaicin tsintar kanta da tayi cikin wannan kazamar harkan, amma ta d’anji dad’i tunda yanzu ta tabbata Alh madu bazai K’ara Mata barazana ba akan rayuwarta dama shine matsalanta….. Yanzu Abu d’aya zan fuskanta shine Idan Yarima yasan gaskiya shima zanyi komai yanda ya dace ta hanyar fad’amai da fahimtar dashi komai…