BARIKI NA FITO 1 & 2

Bariki tace andai yi Asara
Habib yace ke kikaga Asara bani ba
Umman bariki tace kudai dingayi a hankali Kun San Gidan mutane, yanzu sai su kaimu gaba….
Habib yace gaskiyanki domin naga matar can d’akin ta kusa daku Tana min wani kallo wanda ban gane ba, inta karamin sai na mata rashin mutunci in cire kaya mu daku Dan ban son iskanci….
Suna cikin haka Yarima ya kirata tare da fad’in baby come out Ina waje…..
Tashi tayi tana fad’in bari inje inga Yarima na.
Habib yace oh kunga salo a gayas….
Fita tayi tana fad’in kaji dashi…..
Motarshi ta nufa tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso ta bud’e motar ta shigo ciki tare dayin sallama….
Amsawa yayi tare da fad’in my princess na gaji, tunanin driving nakeyi in zan koma Gida…..
Kallonshi tayi tare da fad’in ko in tu’ka ka, in kaika gida??
Yace dakin taimaka min kuwa
Dariya tayi tare da fad’in kaman dagaske….
Yace dagaske nake mana Kinga Idan kikaje can saiki zauna kin zama matata babu dawowa….
Hannu tasa tare da rufe fuskanta tana dariya
Yarima kiran sunanta yayi da Zainab…..
Da sauri ta d’ago ta kalleshi domin jin ya kira sunanta daka gani magana zai Mata Mai muhimmanci…. Wanda yake bukatar natsuwanta
Yace d’azu kina son Yimin magana Ina jinki yanzu….
Murmushi tayi tare da fad’in Yarima a kullum Ina tsoran fad’a maka cewa ni dakai bamu dace ba, saboda kai ka fito gidan girma ni kuma ba y’ar kowa bace ina tsoran auranka domin gudun wulakanci irin na mas……
Da sauri yasa hannunshi a bakinta ya rufe Mata, tare da fad’in enough, dama duk wannan nonsense din kike son fad’amin shine kike d’agamin hankali?….. D’an tsaki yayi alaman jin haushi tare da kawar da kanshi gefe…..
Ganin ranshi ya baci yayi banza da ita, yasa ta d’ago tana mishi magana Yarima kayi hakuri, ban San zakai fushi ba…..
Katseta yayi da fad’in Zainab ban taba tunanin zaki dinga irin wannan tunanin ba…. And kina ma sona kuwa????…..
Da sauri ta kalleshi tare da fad’in Yarima baki bazai iya fad’in irin sonda nake maka ba, how I wish in bud’e maka zuciyata Kaga irin sonda take maka….. Yarima Ina Sonka yanda baka zato duk wani jini dake gudana a jikina yana gudana ne da Sonka I….. Da sauri tayi shuru ganin yana kallonta…..
Jin tayi shuru yasa ya ru’ko mata hannu tare da fad’in Zainab are you sure akan abunda kika fad’a??
Kai ta d’aga Mai alaman eh
Wani irin murmushi ya saki cikin jin dad’i, tare da fad’in nace zan baki albishir d’azu right?
Tace eh
Hannunta ya saki tare da fad’in ina goran albishir din???
Dariya tayi tare da fad’in zan baka in naji albishir din
Dariya yayi tare da fad’in promise?
Tace yes I promise….
Yayi murmushi tare da fad’in mai martaba ya amince da maganan aurena dake…. But at first yace in Bari nan gaba tunda ban dad’e dayin aure ba…. Daka baya kuma ban San mai yasa ya canza ra’ayi ba yace za’a turo gidanku ayi magana d’azu waziri yake fad’amin May be cikin week dinnan a turo……
Bariki gaba d’aya komai nata ya tsaya ta rasa mai takeji murna take ko akasin haka??? Gaba d’aya ta kasa ganewa gadai ta nan ne dai….
Ganin tayi shuru yasa Yarima ya kura mata ido tare da fad’in lafiya kuwa my princess? Kodai you are not happy ne dan za’a turo??
Da sauri tace a’a am so much happy tare da sakin murmushi….
Ganin ta saki jiki yasa Yarima jin dad’i sun dad’e suna fira sannan Yarima yace Zai tafi tare da bata wani Leda Wanda bata san ko miye a ciki ba….
Amsa tayi tare da fad’in ngd
Hancinta yaja tare da fad’in sai munyi magana…..
Tace OK tare da fita tayi cikin gida,…. Tana shiga habib ya amsa ledan tare da fad’in Allah yasa Abun ciye ciye ne dan Wlh yunwa nakeji tun safe babu abunda naci….
Su turare ne Arabian perfumes masu shegen kamshi da kud’i a ciki…. Habib d’aukan kud’in yayi dubu d’aya d’aya bandir biyu, dubu d’ari biyu kenan….. Yace Kai Yarima akwai kyautar girma….
Uwar bariki ta Karya tace ai gidan sarauta ya fito dole ya dinga kyautar girma…. Domin da suji kunya gwara dukiyarsu ta k’are….
Bariki kallon uwarta ta bariki tayi tare da fad’in mai kuke cine Wai??
Ummanta tace abinci nake dafawa wani zubin kuma kowa ya siya…
Bariki tace toh yanzu tunda nazo inyi sati d’aya nan sai a fara girki kullum, kallon habib tayi tare da fad’in muje muyi cefane mu dawo……
Tsakanin haulat da farhan soyayya ta shiga Sosai tun Haulat na nuna bata so harta yarda domin tana sonshi kuma uwa uba farhan ya iya nuna ma mace kulawa tare da kalamai masu dad’i da kwantar da zuciya…… Sai dai abu d’aya haulat da yake damunta shine tasan dakyar Hjy habiba ta yarda d’anta ya aureta ….. Sai dai haulat din tana ganin in bata yarda ba kaman ta nuna mata rashin adalci, and inma ta yarda ta auri d’an nata ya zasu dinga yima juna kallo……..
Farhan ne zaune a falo shida mahaifinshi domin yana kasar…..
Farhan ya kalli dad dinshi yace dad I find someone dat I wanted to marry……
Kallonshi mahaifin nashi yayi tare da fad’in farhan aure Bayan baka kammala karatu ba
Yace dad Ina final year ne, Ina son a fara magana b4 in Gama….
Dad din nashi ya kalleshi cikin son gudan d’an nashi yace why are u so rush to marry??
Yace dad just
Dad din yace ok but wacece yarinyar and Waye mahaifinta??
Farhan yace sunanta haulat mum tasan ta domin at tym Tana kwana gidan na……
Muryan hjy habiba sukaji tana fad’in karyanka Wlh koda zaka mutu bazan bari ka aureta ba, gwara ma kabar wannan maganan…..
Mijin hjy habiba ya kura mata ido tare da fad’in akan wani dalili?? Har kike kiran koda zai mutu bazaki Bari ya aureta ba?? Kin kuwa San abunda kike fad’a kuwa? D’an nawa kike ma fatan mutuwa??….. Toh let me tell you Wlh Indai Inada rai kuma yana Sonta dole In tsaya mai…..
Tace ni kuma ban amince ba domin bai dace da ita ba….
Mijin nata yace habiba akan wani dalili? Miye rashin dacewan? Kallon farhan yayi tare da fad’in naji kaman kace yarinyar tana kwana a nan wani zubin….
Farhan yace eh dad
Kallon hjy habiba yayi tare da fad’in na tabbata inda yarinyar tana da aibu bazaki kawota gidan nan ta kwana ba, harki kasa fad’amin, domin naga Idan kikai ba’ki kina fad’amin but baki fad’amin wannan ba, ina son ki sani kaman farhan ya aureta ya Gama Indai Allah yasa matarshi ce babu yanda za kiyi…..
Hjy habiba tace ni kuma Indai har Ina numfashi kuma ni na haifeshi ban yarda ya aureta ba, kuma bazan taba yarda ya aureta ba….
Dad din farhan yace habiba Ina son ki fad’amin dalilin da yasa bakya son ya aureta??
Tace hakanan kawai ban son ya auri yarinyar
Dad din yace you are not serious…. Tare da kallon farhan yace inka kammala karatunka I promise zan tsaya maka har sai ka aureta…. Yana fad’in haka ya haura sama Fuuuuu tare da fad’in rabo dai yana kisa…..
Kallon farhan hjy habiba tayi cikin bacin rai tace wato ni ban isa bako?? Ka kyauta amma ba laifinka bane…. Itama fuuuu tayi sama
Farhan d’aga kafad’a yayi tare da fad’in whatever nidai Ina Sonta kuma tunda dad ya tsayamin banda damuwa….. Fita yayi yabar gidan
Yarima Aliyu ya fara aiki a asibitin shi, sannan an fara gina Mai filin da Mai martaba ya bashi, da yake filin k’ato ne ko wacce za’a Mata gefenta ginin gidan sama, da yake akwai kud’i an d’iba ma’aikata da yawa suna aikin domin Yarima yace nan da wata biyu ko uku yake son a Gama duka ginin…..