BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Yarima ya dawo gida yau ko wajan Zainab bai samu ya biya ba, kaman yanda Ya sabayi kullum, domin ya gaji, yana shiga cikin falo gimbiya zinatu ta taso Tana kuka tare da fad’in Yarima jita jitan da naji gaskiya ne???

Kallonta yayi sannan ya kauda kai gefe tare da fad’in fad’amin abunda kika ji coz am tired, I need to rest….

Cikin kuka mai sauti tace Yarima naji ance ginin mata biyu kakeyi zaka K’ara aure……

Yarima Aliyu murmushi yayi tare da fad’in gaskiya aka fad’a miki…..

Wani irin ihu ta saki mai kara tare da fad’in Wlh bazan yarda ba, ai wannan cin fuska ne yaushe ka auroni saboda rashin adalci ka Fara maganan k’arin aure, ko wata d’aya Banyi ba amma kake fad’amin zaka K’ara aure Wlh baka isa ba…..

Yarima Aliyu kallonta yake cikin bacin rai, domin ya tabbata ihun da takeyi kuyanginta suna ji…. Dan haka ya wuce ba tare daya kulata ba…..

Ganin haka tabi bayanshi Tana fad’in ai dole ka wuce wlh Yarima bazan yarda da rashin adalci ba har d’akinshi ta bishi tana surutai….

Yarima kam ko kallo bata isheshi ba, toilet ya fad’a Ya barta nan tana ta surutai kaman zararra

Bayan yayi wanka ya fito daka shi sai towel yana goge kanshi, tashi tayi ta nufeshi tare da rungume shi tana kuka tana fad’in Yarima dan Allah ka tausaya min bana son kishiya Yarima Ina kishin ka, maina rasa da kake kokarin K’ara aure, ko wata d’aya Banyi a gidan nan ba amma har kana maganan aure…… K’asa tayi tana kuka mai ban tausayi…..

Jikin Yarima Aliyu yayi sanyi tare da tausayinta…. Gimbiya dake k’asa tana kuka ganin kaman jikinshi yayi sanyi taji dad’i dan dama tasan za’ayi hakan…..

D’agota yayi tare da fad’in zinatu kiyi hakuri, ki d’auka komai kaddara ne, komai ya faru da bawa ki d’auka wannan auren da zan kara a matsayin kaddara……

Tureshi tayi tare dayin baya tace babu wani kaddara…. Karka kara cewa kaddara akwai abunda ba kaddara bane mutum shike sama kanshi….. Duk namiji inya tashi aure saiya dinga amfani da wannan Kalman kaddara kaddara ban yarda da wannan kaddaran ba….

Yarima Aliyu yace baki da ilimi baki san addini ba, so banda time din in tsaya ina bata bakina wajan yi miki bayani…… Kaya ya fara kokarin sawa…..

Ta Fara zunduma ihu tare da fad’in Wlh baka isa ba ,ni nafi karfin wulakanci, sai dai ka zaba cikin biyu koni ko wacce zaka aura….. Ni Wlh bama laifinka bane na iyayenka ne da suka d’aure maka gindi kake son yin wannan rashin adalcin sune munafukai marasa tsoran Allah d….. Tas ya sauke mata Mari da sai da yasa ta dawo cikin hayyacinta……

Ri’ke wajan tayi domin Marin ya shigeta Sosai…

Yarima Aliyu yace you cross your limit kije na sakeki saki d’aya bazan zauna da macen da zata zagi iyayena ba koda da wasa……

Gimbiya zinatu tace saki?? Yarima kasan Mai ka fad’a kuwa? Ka manta cewa babu saki tsakanin mu koda kuwa maina maka saika kamani da laifin Zi……

Yarima yace keep quiet, wannan ne dalilin daya baki daman kiyi min komai saboda bazan sakeki ba?ciki harda raina iyayena? U r wrong, al’ada ba addini bace, you better leave this place tun Kafin in miki abunda za kiyi mamaki na Iletered ……. Tashin hankali???? Yarima Aliyu ya karya dokan masarauta koya zata kaya muje zuwa……..

plz masu min magana ta messenger kuyi hakuri ku daina saboda bani da messenger na goge facebook kawai gareni shima saboda posting ne, duk mai son magana dani yaje page dina yamin magana zan gani Inba mutum amsa, amma in a messenger ne zan gani babu daman bada amsa, dan na goge

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 12*

Idonta na kanshi ganin dagaske yake zai iyayi mata komai yasa tayi gaba tare da tsayawa wajan kofa tace Yarima nika saka? Auren dako wata d’aya baiyi ba amma ace harka sakeni? Lallai kayi babban kuskure a rayuwanka daka furta min wannan Kalman, sannan inaso ka jira Kaga Mai zai biyo baya tunda har ka karya wannan dokar ta masarauta….. Fuuuuuu ta fita

Yarima Aliyu yace mad girl tare da saka, saka jallabiya ya kwanta danya huta domin yayi matukar gajiya gashi wannan matar tashi ta kara jagula Mai lissafi, yana kwanciya yaji Phne dinshi na ruri kallon wayar yayi tare dakai hannunshi kan wayar, Sunan Mai martaba ya gani, d’auka yayi ban San mai mahaifin nashi yace mishi ba naga yace gani nan zuwa…..

Tashi yayi ya canza kaya sannan ya nufi gefen mahaifin nashi inda yaga mum dinshi damai martaba a cikin bedroom dinshi….. Yana kokarin gaida mahaifin nashi Kafin ya karasa sai saukan Mari yaji tas tas har guda biyu abunda ba’a taba mishi ba tunda ya taso gashi yau mahaifin nashi yayi mishi…..

Cikin fushi da bacin rai Mai martaba yace ka zubar min da k’ima, saki cikin wannan masarautar?? Bayan kasan sai an Kama mutum ya aikata laifi biyu ake saki????

Yarima Aliyu yace Abba Ina Mai neman gafaran ka, Abba zagin iyay…….

Mai martaba ya daka Mai tsawa Wanda ba Yarima ba harta mum dinshi saida ta tsorata da irin tsawar damai martaba yayi ma Yarima Aliyu……. Yace na baka umarnin Ka maida matarka, sannan daka yau Indai harka K’ara Karya wannan dokar ban yafe maka ba duniya da lahira….. A haka kake kokarin K’ara aure??? ….. Mata d’aya ma ka kasa da ita ko wata d’aya bakayi da itaba amma har Kalman saki ya shiga?? Am really dissapointed with you…… Ina son daka yau kaje ka zauna kaida matarka karka K’ara taso da maganan auranka dan banga alaman zakai adalci ba ko kad’an…… Sannan wannan al’adan daka karya saina hukunta ka, kaje kaida kanka kasa a rufeka sai kayi sati biyu Kafin ka fito mutumin banza……

Tunda Mai martaba ya fara magana kan Yarima Aliyu na k’asa, har Mai martaba ya kammala, sannan Yarima Aliyu ya fara magana da fad’in Allah ya huci zuciyar Mai…… Dakatar dashi Mai martaba yayi tare da fad’in tashi kaban waje……. Ban son jin komai daka gareka….

Yarima Aliyu jiki a sanyaye ya tashi ya fita direct cikin kurkukun masarauta yaje tare da bada umarnin a rufeshi……. Fadawa babu daman tambaya face aiwatar da abunda Yarima ya basu umarni…….

Bayan fitan Yarima Aliyu mahaifiyar Yarima tace ma Mai martaba hukuncin da aka yanke ma Yarima yayi tsauri da yawa ya…… Mai martaba dakatar da ita yayi tare da fad’in banso ki kuma saka baki cikin wannan maganan, kije ki fad’ama zinatu ta koma d’akinta……

Mum din Yarima amsawa tayi da Toh tare da fita dan tasan mijin nata yayi fushi Sosai…. Kuma tasan Kafin ya sauko sai anji jiki mutun ne mai hakuri amma bai iya fushi ba, ta tabbata tunda har Ya iya rufe ido ya hukunta Yarima tasan dakyar ya saurareta yanzu…… Koda ta koma gefenta taga zinatu nata kuka rarrashinta tayi akan tayi hakuri tare da fad’in ta koma d’akinta komai ya wuce, kiran Hafsat tayi tace ta raka gimbiya gefenta…..

Hafsat ta amsa da toh tare da cema gimbiya zinatu muje….. Direct gefen gimbiya suka shiga suna shiga gimbiya ta wuce sama tabar Hafsat nan….. Hafsat tace kina da aiki……

Hafsat komawa tayi wajan mum din tasu Tana tambayarta maiya faru,?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button