BARIKI NA FITO 1 & 2
Hafsat ri’ke fuskan tayi tare da fad’in ni kika mara??
Gimbiya zinatu tace eh ko zaki rama ne??
Hafsat murmushi tayi tare da fad’in bazan rama ba, saboda kinci darajan Yarima inda badan shiba Wlh da Kafin ki sauke hannunki saina nuna miki kuskuranki….. Dasai kinyi dana sanin Marin Hafsat a cikin masarautar su…..
Gimbiya zinatu tabe baki tayi tare da komawa cikin d’akinta, domin tana ganin kaman Hafsat din zata iya ramawa Dan yanda taga lokaci d’aya har tana iya ganin bacin ranta K’ara ra…..
Hafsat fita tayi ta koma d’akin mum dinta, bata ganta a falo ba dan haka tayi bedroom dinta, inda ta sameta ta fito daka wanka……
Mum din tace Hafsat Wai ba zaki ki kwanta ba? kike ta zarya??
Tace mum wani bacci zanyi Yarima yana kulle cikin sauro babu fanka babu katifa, haba mum….. Kuka ta kuma saki…..
Mum din tace wlh kina da aiki Hafsat, kallon Hafsat din tayi tare da fad’in maiya sami Fuskanki naga ya tashi??
Cikin kuka tace mum Wlh gimbiya zinatu bata da kirki, bama mum labari tayi, tare da cewa mum Wlh Yarima shine mai gaskiya amma Abba baima saurareshi ba, jiba Nima daka zuwa kalla abunda tamin….
Mum ranta ya baci amma saita boye Dan Kar y’ar tata ta gane, tace Hafsat komai zai faru ni dake bamu da ikon bud’e Yarima sai abbanku, dan haka kije ki kwanta kina zaune zai sa a bud’eshi Kinji…..
Hafsat jiki a sanyaye ta fita ta nufi gefenta…..
Mum kaya tasa ta nufi gefen Mai martaba, inda ta sameshi zaune a cikin bedroom dinshi Yana kallon news, zama tayi dan nesa dashi har aka gama Labaran sannan tayi gyaran murya tare da fad’in ina son magana dakai inka bani dama…..
Mai martaba yace tunda nake dake, baki taba tambayana izinin magana dani ba, dan haka kiyi maganan ki Kai tsaye…..
Tace magana zanyi akan Yarima wacce nake bukatan amsa, Nasan Yarima yayi laifi babba, na sakin matarshi wanda kayi amfani da maganan matarshi kayi mishi hukunci, sannan maganan al’ada shima a……
Mai martaba ya dakatar da ita, tare da fad’in Khadija koke da kika haifa Aliyu bazaki fad’amin halinshi ba, abunda nake son ki sani bawai naki sauraran Yarima bane ko Nayi amfani da maganan matarshi ba ko d’aya, na hukunta shine ta hikima akan Kalman saki daya furta, wannan hukuncin dana mishi zaisa nan gaba komai zai faru tsakaninshi da iyalinshi bazai yi saurin furta Kalman saki ba, duk kuwa yanda ranshi ya baci, Idan har namiji ya fara furta Kalman saki in ba’ayi wasa ba ya fara kenan tun kana d’aya biyu har sai Ayi uku azo ana nadama….. Wannan hukuncin da namai shine zai nuna mishi cewa komai zai faru ya zama mai hakuri ya daina saka Kalman saki….. Namiji da hakuri aka sanshi mace shu’uma ce in ranta ya baci babu abunda bazata fad’a maka ba, in kaga haka sai ka fita ka barta karka biye mata har Kalman saki ya shiga, yana dakyau namiji ya daina saka Kalman saki a duk sanda matarshi ta bata mishi rai domin a lokacin shaidan yana kansu, zaiyi ta ingiza su, in yaji anyi saki sai yasa ma kanshi rawani yayi nasara, sai yasa ba’a so mutum ya yanke hukunci cikin fushi and Idan mace ta maka laifi akwai hanyar da zaka hukunta ta harta gane tayi kuskure …. Sai yasa nake muhimmanta wannan al’adan masarautar na hana saki sai an Kama mutum da laifi biyu…… Na farko zina domin duk matar da take da miji tayi zina hukuncin jifa ne a kanta, sannan a lokacin da mazinata ke zina ana cire musu imani…… Wa’iyazubillah yanzu in mutun ya mutu yana aikatawa Mai zaice ma Allah???????????? Wanda yanzu zina ya zama ruwan dare ga matan aure….. Duk saboda san duniya shaidan yayi tasiri a zukatan wasu al’umma, suna aikata alfasha basu daukeshi bakin komai ba, suna ganin kaman za suyi tsawon rai Kafin su mutu zasu daina, wanda shaidan ne ke sa musu haka, kaita zuba iskanci kana ganin Aini ba yanzu zan mutu ba Kafin in mutu zan shiryu haka Kai baka shiryu ba mutuwa zata zo maka babu notice sai dai ka farka ka ganka cikin kabari???????????????????? ka girbe abunda ka shuka…. Wlh hawaye nake ina rubuta wannan wajan???????????????????????????????????????? kawai Ina tuna irin azaban kabari da ukuban da mutum zai Tarar in bai aikata Abun al’kairi ba…. Bayan azaban kabari tashin alkiyama, hisabi tsallake sirad’i, saka mako wuta ko Aljanna ???????? kai Wlh duniya ba komai bace…. Allah yasa mu dace….. Mai martaba yace sannan wanda ya aikata kisan Kai shima bashi da imani zai iya kashe kowa…. Kinga mutane biyun nan kaji tsoran zama dasu……..
Mum ta sauke ajiyan zuciya sannan tace hakane Allah yasa mu dace….. Amma maganan auran da yake son ya kara fah??
Mai martaba yace wannan maganan ki bari inya fito naga irin yanda yake ma matar tashi sai in yanke…..
Mum tace babu damuwa duk da tasan itama matar tashi tana da nata matsalan, mum tace sarki Mai adalci Ina neman ma Yarima sassauci domin wajan da zai kwana babu katifa filo ga sauro….
Mai martaba yayi murmushi tare da fad’in karki damu kin San bazan barshi haka ba nasa a bashi maganin sauro….. Da abun lulluba amma bai San nina tura mai ba, zaiyi tunanin fadawa ne suka bashi…..
Mum ta d’anji sanyi da taji haka dan haka ta saki ranta Sosai…….
Bariki dake zaune tana kallo gidan iyayenta na bariki, tashi tayi ta d’auki wayanta ta danna, taga miss call din Yarima, ido ta zaro tare da fad’in ya akai banji K’ara ba, da sauri ta Fara kira lokaci d’aya kuma ta kashe saboda ganin dare yayi Sosai tare da fad’in bari ta mishi message In idanshi biyu zai kira,
Message ta Fara rubutu mishi kaman haka……
Barka da dare Yarima na, sorry ka kira wayan yana silent yanzu kuma naga dare yayi, Ayi min afuwa ur wife to be insha Allah.......... Tura mai message din tayi tana murmushi.....
Ganin bai mata reply ba bai kuma kirata ba yasa tayi tunanin yayi bacci ne, dan haka itama ta fita ta nufi toilet ta Kama ruwa, ta dawo ta shiga Uwar d’aka ta kwanta inda ummanta na bariki take akan gado, tunda bariki tazo abbanta na Bariki baya kwana a gidan, dama a falo yake kwana Wanda bariki ta Fara tunanin dama suyi aure amma bazata musu magana ba dan tasan dukansu ba yara bane, and shima mahaifin nata na Bariki ba’ko yaushe yake kwana ba dan yana da iyali yana dan kwana ne wani zubin saboda mutanan gidan Kar su Fara zargi wannan kenan…….
Gimbiya zinatu Bayan ta koma d’aki, kiran gimbiya Amina tayi ta fad’a mata abunda ke faruwa harda sakin da Yarima yayi mata da Marin da tayi ma gimbiya Hafsat……..
Gimbiya Amina salati ta saki tare da fad’in Kai saki fah kika ce??
Gimbiya zinatu tace eh saki Wlh akan zai K’ara aure, dan Nayi magana shine nayi laifi .
Gimbiya Amina tace lallai Yarima hukuncin damai martaba ya yanke yayi dai dai dashi, amma ina son kiban hankalinki kije ki roki, Mai martaba kaman yanda Hafsat tace miki akan a sako Yarima, ina son ki nuna mishi saboda ke yasa aka sako shi, Idan kikai hakan iyayen nashi zasu gane kina sonshi, Kinga zasu K’ara d’aura Mai laifi…… Sannan kije yanzu cikin daren nan kiba Hafsat hakuri ki nuna mata kinyi nadama Inba haka ba zaki jama kanki ba’kin jini keda kike da y’an uwan miji Mata, bata haka ya kamata kiyi ba, yanzu kije kiyi abunda na saki, ke kije har wajan Mai martaba dinma yanzu amma ki Fara zuwa wajan Hafsat din, ita zata raka ki wajan abban nasu ,
Gimbiya zinatu tace my love kefa da kanki kin San bama Hafsat hakuri a wajena ba abu bane mai yihuwa
Tsaki gimbiya Amina tayi tare da fad’in kiyi abunda na saki, zinatu ban son musu Tana fad’in haka ta kashe wayan….. Ganin haka yasa Gimbiya zinatu saka dogon hijab akan kayan baccin da tasa ta fita domin aiwatar da abunda gimbiya Amina tace mata…….