BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Kai tsaye gefen gimbiya Hafsat ta nufa….. Nocking tai tayi….. Gimbiya Hafsat dake zaune ta kasa bacci taji ana mata nocking tashi tayi ta bud’e kofar ganin gimbiya zinatu yasa ta tamke fuska….

Gimbiya zinatu tace Hafsat nazo in baki hakuri akan abunda ya faru d’azu … Rai nane a bace akan abunda ya faru tsakanina da Yarima, d’aura hannunta tayi akan kafadar Hafsat tace Hafsat Nasan Idan Kece a matsayina May be kiyi abunda yafi haka in zaki min adalci ya kamata kisan duk wata mace ranta zai baci in taji mijinta zai K’ara aure ko wata d’aya batayi ba da aka aurota….. Hafsat Ina son Yarima, sonshi yasa nake kishin shi, Hafsat Kema mace ce, nasan zaki fahimceni, d’azu sanda kika zo idona a rufe yake saboda bacin rai, Nayi nadaman zagin da nayi ma Yarima tare da Marin da nayi miki, gashi saboda ni aka rufeshi dan Allah zoki rakani Inba Mai martaba hakuri a sako Yarima ta karasa maganan tana kuka.

Hafsat gaba d’aya tausayin gimbiya zinatu ya kamata, har take ganin k’arin auren da Yarima yake son k’arawa tabbas baima gimbiya adalci ba , inma zai K’ara aure ya Bari nan gaba Kafin gimbiya ta Gama cin amarci, amma daka zuwanta yace zai K’ara aure gskya baiyi adalci ba ko kad’an Hafsat gaba d’aya sai take ganin laifin dan uwan nata ne, kallon gimbiya zinatu tayi tare da fad’in kiyi hakuri gimbiya komai ya wuce, sannan ina son ki sama ranki komai ya faru da bawa kaddara ne.

Gimbiya zinatu cikin ranta tace ke kika ga kaddara amma bani ba, sai mutum ya tsula maka tsiya ace min Wai kaddara ce…… Amma a fili sai tace hakane, tare da fad’in muje mu sami Abba dare Nayi a samu a fito da Yarima…..

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 14*

Gimbiya Hafsat tace ok bari in d’auko hijab, komawa tayi ta shiga bedroom d’inta Jim kad’an sai gata da hijab a jiki tace muje…… Direct gefen Mai martaba suka nufa suka fara nocking…… Mum ce ta bud’e kofar….. Ganin su zinatu yasa ta fad’in lafiya kuwa?? Bakuyi bacci ba har yanzu??

Hafsat tace mum plz Abba muka zo gani Dan Allah.

Mum tace ku shigo, bari in kirashi….. Ciki tayi Jim kad’an sai gasu ita damai martaba

Mai martaba yace zinatu lafiya??

Cikin kuka tace Abba dan Allah kayi hakuri a fito da Yarima…..

Mai martaba shuru yayi yana nazari can yace Babu damuwa ki tashi kije, zai zo yanzu ya sameki….

Cikin kuka take ma Mai martaba godiya akan yarda da yayi zai sako Yarima, tare da tashi ta fita ita da Hafsat.

Bayan sun fita Hafsat ta kalli gimbiya tace, ngd da kikai magana za’a fito da Yarima ba karamin dad’i naji ba…..

Gimbiya zinatu tayi murmushi tare da fad’in karki damu, nima ba karamin dad’i naji ba, domin bazan iya bacci ba Yarima yana kulle a kurkuku.

Hafsat taji dad’in maganan gimbiya Sosai, dan haka tace mata taje gefenta Kar Yarima ya fito yaje yaga bata nan…….

Bayan fitan su gimbiya zinatu daka wajan Mai martaba, yasa aka bud’e Yarima tare da fad’in yazo inda yake…… Bayan an bud’e Yarima direct wajan mahaifin nashi yaje……

Bayan Yarima yazo gaida iyayen nashi yayi da fad’in Barka da dare…. Zama yayi a k’asa tare da fad’in Abba Nasan yau na bata maka rai Nayi abunda baka taba tunanin zanyi ba, Abba Ina neman gafaran ka, domin fushin ka a kaina baraza ne a rayuwa na, dan Allah Abba ka yafe min…….

Mai martaba ya Katseshi da fad’in Aliyu tunda nake dakai baka taba sani cikin fushi irin yau ba, amma babu komai ni musulmi ne Nayi imani da kaddara kuma haka Allah ya tsara, babu wanda ya isa ya canza, umarni kawai mukebi…… Amma ina son in ro’ki alfarma akan Kar wannan Kalman ta K’ara fita daka bakinka ba tare da babban laifi ba, Wanda yake cikin dokan wannan masarautar, wanda bama fatan hakan ya faru……

Yarima kanshi na k’asa yace Abba ka daina bani shawara ko neman alfarma, koda yaushe nafi son kace kaban umarni, Idan kace min alfarma ko shawara Ina jin wani iri, Abba Nasan na aikata kuskure Wanda Nayi nadama, ina ro’kan gafara tare da bada hakuri…..

Mai martaba yace Allah yayi maka albarka, kaima Allah ya baka yara masu maka biyayya, Mai martaba yayi ma Yarima nasiha Sosai tare da K’ara fad’a Mai muhimmancin hakuri…… Daka karshe yace ya Tashi yaje ya kwanta…..

Yarima tashi yayi tare dayi ma iyayenshi saida safe ya nufi gefenshi……

Bayan fitan Yarima Aliyu, mum din Yarima tace Kai Allah ya kyauta.

Mai martaba ya amsa da Ameen, Aliyu yana da hakuri amma bai iya fushi ba…..

Mum tace ai halinku d’aya…..

Mai martaba murmushi yayi tare da fad’in Kai Anya kuwa? Amma yana da zuciya kuma ina tunanin irin naki zuciyar ya d’auko….. Dariya duka suka sa…….

Yarima koda ya shiga bedroom dinshi ya shiga Kai tsaye ya fad’a toilet ya sakeyin wanka, tare dasa jallabiya, lokaci d’aya kuma ya tuna da wayoyinshi fita yayi yaje ya amso tare da dawowa a falo yaga gimbiya zinatu wannan karan, kallo d’aya ya mata ya kauda kai tare daci gaba da tafiya…..

Binshi tayi da sauri tasha gabanshi tana kuka, tare da fad’in dan Allah Yarima kayi hakuri, nasan nayi maka laifi, wlh shairin shaidan ne da kuma na zuciya, Yarima nayi nadaman zaginka dan Allah ka yafemin Wlh shairin zuciya ne kuka take Sosai tana magana….

Yarima ganin yanda take kuka yasa ta tashi tausayi, yace ya isa haka, kibar wannan kukan komai ya wuce tunda har kin gane kuskuranki…..

Tace Wlh Yarima Ina jin kunyan kallonka domin abunda Nayi maka sai inga kaman bazaka yafemin ba

Yarima Aliyu murmushi kawai yayi tare da jan hannunta suka haura sama, d’akinta ya kaita tare da fad’in go and sleep sai da safe……

Hannunshi ta ri’ke tare da fad’in Yarima plz let slp together plz

Yarima zaiyi magana tace plz Indai harka hakura akan abunda nayi maka let slp together am your wife….

Yarima yace ok let go to my room, I can’t sleep here…..

Gaba yayi itama ta bishi, suka nufa d’akinshi Yarima bai samu ya kunna phone dinshi ba saboda bacci ne Sosai a idonshi dama yau ya gaji ga kuma abunda ya faru…..

Gimbiya zinatu duk yanda taso tayi Yarima danya kulata amma ya’ki domin bai dad’e ba bacci ya D’aukeshi…. Duk da shima ya Lura da abunda take bukata amma bawai ya kyaleta bane akan abunda ta mishi yana da burin hukunta ta, domin inya barta haka nan gaba zata K’ara abunda yafi zagan mishi iyaye…. Ganin yayi bacci yasa tayi tsaki tare da fita daka d’akin tayi nata d’akin…….

Message tayi ma gimbiya Amina akan yanda ta aiwatar da abunda ta sata, tare da fad’in an sako Yarima gobe za suyi waya ta karasa Mata sauran bayani…..

Washe gari Yarima Aliyu tun 7 yabar gida ya shigo garin kaduna, direct hspt dinshi ya nufa, Sai a lokacin ya kunna wayoyinshi yaga sa’kon Zainab dinshi, murmushi yayi tare da ajiye wayan ya fara aiwatar da abunda yake gabanshi……

Bariki koda ta tashi ummanta ta bariki tayi musu abinci, ci tayi sannan taje tayi wanka, tare da shiryawa don Tana son zuwa maraban jos wajan haulat domin tun shekaran jiya take ta kiran bariki akan tana son ganinta….. Kallon ummanta ta bariki tayi tace zan fita amma anjima kad’an zan dawo….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button