BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Cikin Wanda sukazo daka gefen Yarima harda Mai Anguwa, ma’ana sarkin u/kanawa, wanda Kafin su zo shine aka bama damar yin bincike akan gidansu yarinyar da irin tarbiyanta, kuma yace babu wani matsala gidan tarbiya yarinyar take Yadai yi magana Mai Kyau akan gidansu bariki ???? ko Mai yasa yayi haka?? Bayan yasan yanda sarauta take?? Sannan hausawa na cewa shidai ramin karya kurarre ne, koma dai miye dalili za muji zamu gani….

Koda su waziri suka koma, sunyi ma Mai martaba bayanin irin gidansu bariki, Sun fad’a mishi gidan mutunci Yarima yake neman aure, sannan suka kara da fad’amai sai dai talakawa ne Sosai ba masu karfi bane, domin yana yin gidansu ya nuna hakan, kuma kaman gidan Haya suke, waziri ya kara da fad’in sai dai abunda ya kara burgeni duk da irin talaucin su , suna da wadatar zuci, basu da kwadayin abun duniya

Mai martaba yaji dad’i Sosai, tare da fad’in ina son Kafin Ayi bikin a nema musu Gida su koma, wannan kyauta ce daka gareni

Waziri yace an gama godiya suke .

Bariki bayan magabatan Yarima sun tafi, ta fito ta sami babanta na Bariki da sauran mutanan, nan suka bata kud’in, sannan ta sallami mutum biyu din akan saita kara nemansu. Tafiya sukayi suna godiya.

Kallon abbanta na Bariki tayi tace gskya aiki yayi kyau

Yace Sosai kuwa, sai naji dama auran nan da iyayenki na gskya kika had’asu, ina tsoran ranan da asiri zai tonu

Bariki tace karka damu, komai a tsari nake tafiyar dashi.

Yace dakyau tare da fad’in ni kam inda mmnki zata yarda Aida munyi aure

Bariki tace dagaske kakeyi?

Yace dagaske nake Wlh

Bariki tace Aikam zan mata magana sannan ni zan biya sadaki, da kayan lefe akwati guda biyu ai zan had’a maka Indai dagaske ne wlh, nima na samu lada

Yace ina godiya Kinga gwara Ayi auran, tunda nida ita Kar tasan Kar ne

Dariya bariki tayi tare da fad’in wannan haka yake.

Yarima Aliyu yana barin asibiti ,direct wajan bariki ya nufa, inda bata ma San da zuwanshi ba, saida ya kirata yace ta fito yana waje, Dan haka ta tashi ta fita ta sameshi a mota

Yarima kallonta yayi cikin jin dad’i tare da fad’in amaryata

Murmushi tayi cikin jin kunya tare da gaidashi

Amsawa yayi tare daja mata hanci, yace am so happy today

Kallonshi tayi tare da fad’in happy for wht?

Yace soon zaki zama tawa ….. Oh na manta kin ma riga kin zama, Ashe an bani ke har an biya sadaki…

Murmushi kawai tayi

Yarima yace yaushe za muje kiga gininki?

Tace a’a basai Naje ba,

Yace toh ni ina son kije ki gani , ya za’ayi kenan??

Tace zan tambayi Umma inta amince sai muje

Murmushi yayi kawai tare da kawar da maganan yace, Mai kike bukata Ayi da bikin mu??

Tace kaman me??

Yace event din da za’ayi

Shuru tayi tana nazari inta yarda Ayi event Kar a wajan event taga Wanda ta sani, Kar su fad’ama Yarima gskya Kafin ita ta fad’amai, kai gskya a’a.. Kallon Yarima tayi wanda shima ita yake kallo tace Yarima inaga Kar Ayi wani bidi’a…..

Kamo hannunta yayi tare da fad’in, a’a ya kamata muyi koda Abu d’aya ne, muyi dinner, inaga zaifi

Tace toh amma fah badan taso ba, ta dai amince ne dan Kar yaga kaman ta’ki yarda da maganansa…..

Kallonta yayi yace tunda an gama maganan event saura na akwati zan baki kud’i Kisai irin kayan da kike so, duk da za’a kawo miki daka gidanmu, wannan wanda zan baki akwai wanda nake bukata ki siya wanda only me zan dinga ganinki dashi, saiki K’ara da irin naki choice din .

Bariki ido ta rufe ciki jin kunyan maganan Yarima, ta rasa mai yasa Idan yayi mata wata maganan take jin kunya Bayan tasan ita bata jin kunyan magana gaban kowa, kodan Yarima badan iska bane sai yasa nake jin kunyan shi? Tabbas hakane domin duk Wanda kuka ga yana maganan banza gaban wani in kuka duba za kuga shiya bada dama Ayi mishi.

Sunyi fira akan in zai dawo zai Kawo Mata kud’i cash ta siya abunda take so sannan ya Mata sallama ya tafi ….. Toh andai ce duk abunda akace an yishi had’e da karya komai daren dad’ewa gskya zata bayyana, zamu gani asiri zai tonu Kafin biki ko sai Bayan biki muje zuwa……..

~MARYAM OBAM~

BARIKI NA FITO

            *BY*

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

WWW.Maryamobamnovels.com

Wattpad @maryam-obam

Instagram@maryam_obam

MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO

DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO

BOOK 2

                 *PAGE 16*

Bariki gida tayi, tana shiga ta doka ma habib kira akan yazo, kallon uwarta ta bariki tayi tace Umma…..

Amsawa tayi da fad’in ya akayi? Yau dai Kedai shar

Bariki tayi dariya, tare da fad’in ina son miki magana Allah yasa zaki amince….

Umma din tace name fah.?

Bariki tace akan abbana, Mai zai hana kuyi aure, inaga zaifi muku.

Umma tace aure? Dawa Rufamin asiri, barni inyi abunda ya kawo ni.

Bariki tace kin fiso ki zauna babu aure??

Tace a’a ina so inyi mana inna samu dai dai ni

Bariki tace gashi kin samu

Dariya tayi tare da fad’in shiya ce miki zai aureni? Ko Kece kike son had’awa??

Bariki tace shiya Aiko ni inyi miki magana, kuma naga Wlh auran shiya dace daku.

Tace hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, saiki fad’a mishi na amince

Bariki tace Alhmdlh, amma dan Allah Ayi bikin Kafin aurena….. Nan dai sukai ta tattaunawa suna cikin fira habib ya fad’o kaman an jefoshi

Bariki tace miye haka ko sallama babu

Tsaki yayi tare da fita ya tsaya a kofar d’aki yana gafaranku dai masu d’aki, tare da kuso Kai…..

Bariki tace wannan ne sallama??? Ai b….

Yace dakata Mlm, nifa ban gane miki ba, tunda Yarima ya fara soyayya dake kika koma wata iri iri, in ke kin zama ustaziya ni barni yanda nake…..

Bariki tace Allah ya shirya, ni bama wannan ba zauna kaji…..

Kallon tara saura kwata ya watsa ma bariki, sannan yace wlh Ina gab da in Tsiga miki rashin mutunci, Idan kina kaini jinsin da ba nawa ba…..

Tace Allah ya baki hakuri, zauna dan Allah

Zama yayi yana bud’e hanci wai shi a dole ranshi a bace yake

Bariki tace iyayen Yarima sun Aiko har Sun tafi

Yace haba dan Allah?? Gud’a ya saki tare da fad’in inama inada duwawu babba dana tashi nayi rawa da duwaiya guda d’aya….

Bariki dariya tayi tare da fad’a ma habib yanda aka yanke bikin nan da wata biyu

Habib yace Wlh bariki ban San mai yasa ba, ina sonki da Yarima,…

Bariki tayi dariya tace ngd kawata, nan suka shiga tsara yanda za’a gudanar da bikin da yanda za’a samo kawayen Haya duk habib yace abar komai a wajanshi……

Sannan maganan gyaran jiki irinsu dilka, maganin Mata bariki tace y’ar Maiduguri take So,da yar Sokoto

Suma habib yace duk zai Kawo, cikin satin nan dan a Fara , sunyi magana Sosai inda tabi habib suka je maraban jos domin ta Fara had’a kayanta wanda take bukata wanda bata so kuma ta bayar…..

Koda suka je sunga haulat ita da Hjy babba suna magana, ganin bariki yasa haulat ta nufi bariki Tana fad’in Indai za’aga wannan kina wajan…..

Habib yace Wlh Haulat zan miki bura uba, ban so

Tabe baki Haulat tayi tana bashi hakuri,

bariki kam wajan hjy babba ta nufa tana fad’in haka hjyta har yanzu fushin ake dani?.

Hjy babba yace kyaji dashi, ni Kinga karki batamin rai yanzu da yamman nan

Bariki tace haba hjyta kiyi hakuri mana

Hjy babba yace Wlh bariki kina bani mamaki, da kyanki da kuruciyarki da lafiyanki, amma kice zaki aure, keda ake rububinki haba bariki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button