BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Biki ya kan Kama amma amarya bata cikin nutsuwa kullum tana cikin fargaba, harta rame saboda damuwa, kullum bata da wani aiki sai kuka tare da K’ara tsanar rayuwar bariki…….. Tana cikin wannan kukan Yarima ya kirata, da sauri ta seta kanta dan Kar ya gane sannan ta d’auka…

Gaidashi tayi

Amsawa yayi tare da fad’in ya naji muryanki haka??

Da sauri tace mura nakeyi Yarima

Yace toh fah, Allah ya sawake zan Aiko miki da magani.

Tace nasha tun dazu

Yace OK, toh ya shirye shirye?

Tace Alhamdullilah

Yace za’a Aiko miki da kayan da zaki saka a dinner sannan masu makeup za suzo suyi miki ranan, lil sis taban sa’ko in fad’a miki

Bariki tace ok Allah ya kaimu

Ya amsa da Ameen, sun d’an taba fira Kafin sukai sallama…..

Yana ajiye wayar gimbiya zinatu ta shigo, Tana fad’in yanzu Yarima saboda cin fuska a cikin gidan nawa kake waya da wacce zaka aura??? Kuka ta fashe dashi tare da fad’in haba Yarima Wlh kana cimin fuska da yawa maina maka haka da kake Yimin wannan abun??

Ganin yanda take kuka sai yaji ta bashi tausayi, rarrashinta ya farayi…..

Gimbiya zinatu ji take kaman ta tureshi Dan tsabagen kishi, Allah ya sani da badan gimbiya Amina tana kokarin hanata wani Abun ba da Wlh babu abunda zai hana tayi ma Yarima mugun tujara, amma Gimbiya Amina tace tayi hakuri ta Bari Ayi auran zata nema Mata mafita, yarda da gimbiya Amina da tayi shine yasa har take dan jurewa, amma ji take kaman zata mutu dan kishin Yarima take Sosai, bata son ganin ko wace mace kusa dashi……

Toh biki ya rage saura kwana biyu, inda a yau za’a gudanar da dinner, bariki da habib sunyi hayan kawaye Wanda sune kawayen amarya, cikin kawayen harda haulat da khairat, zuwan haulat gidan iyayen bariki yasa ta gane yanda bariki ta shirya auranta, ta gano tayi amfani da iyayen bariki, haulat ta kalli bariki tace gskya kinyi dabara, nima Ina tunanin haka zamma farhan, in samo iyayen bariki

Bariki ganin Haulat ta gano komai, yasa tace inko za kiji shawarata karki Fara yin aure da iyayen bariki, gwara ki koma Gida wajan danginki

Haulat tace Hmmm kedai kawai Ayi sha’ani,

Anyi ma amarya makeup na Kece raini, tayi mugun bala’in yin kyau, gaba d’aya makeup din da aka mata yasa ta canza, ta kara mugun kyau dama yaya balle an kara da wanka, an shiryata cikin wani tsaddan material Mai Kama da less anyi mishi dinkin doguwar riga, k’asan kuma anyishi da fad’i kaman weeding gown, an saka mata head maroon kayanta kuma golden, ba karamin kyau tayi ba, kawayenta kuma sunsa kaya red head golden, ba karamin kyau bariki tayi ba, da kawayenta, 7 dai dai aka turo motoci dan d’aukan amarya da kawayenta zuwa wajan dinner da za’ayi a cikin garin kaduna, duk y’an uwan ango suna kaduna, an d’auki amarya an nufi hall da ita, inda motarsu na zuwa na ango yazo, dan haka Yarima ya fito ya nufi motar da Zainab ke ciki, Yarima daya ganta ido ya kara bud’ewa ganin irin kyau data K’ara kaman ba ita ba, dama yasan tana da kyau gashi anyi mata makeup, lokaci d’aya kuma sai yaji yana kishin ta shiga Ayi ta kallonta, ya dad’e a motar yana nazari akan baiso ta shiga…..

Itama ta gefen amarya fargaba take, karta shiga taga Wanda ta sani, asiri ya tonu…..

Jin Yarima shuru yasa usman yazo yana buga glass din motar

Bud’ewa Yarima yayi tare da fad’in Usman gskya aje abama mutane hakuri, an fasa wannan dinner din, suci abinci kawai su wuce

Usman yace Yarima. Kasan Mai kake fad’a kuwa?? Plz Yarima ku fito mu shiga

Yarima yace kasan inna fad’a magana bana canzawa koh??

Usman shuru yayi yana nazari can yace dan Allah Yarima kayi hakuri ka duba girman Allah karka bamu kunya……

Yarima ya dakatar dashi da fad’in am telling you kayi abunda nace, wannan umarni ne…. Karan wayanshi yasa ya d’auka ganin lil sis

Yana d’auka tace Bros ku shigo mana kowa na jira, dan Allah kuyi sauri

Yace sis am sorry bazan zo ba, kuba mutane hakuri …..

Tace what? Tare da tashi ta fito waje dan taji dakyau, hango usman tayi da Yarima a tsaye da sauri ta nufesu, tana fad’in bros miye haka plz kuzo ku shiga….

Zaiyi magana tace plz koso kake ace akwai matsala ne??

Yace let people say what ever, nidai bazan shiga wannan wajan ba.

Hafsat tace bros akan wani dalili?

Yace ban son ayita Kalle min Mata, inada kishin iyali na

Hafsat hannu ta d’aura a Kai, alaman takaici, danta d’auka wani abune akayi mishi da yasa yace bazai shiga ba, motar da bariki take Hafsat ta nufa, sai gata ta fito

Ganin amarya a waje yasa Yarima ya fara yima Hafsat fad’an Mai yasa zata fito mishi da mata….

Hafsat tace bros nifa bani na fito da itaba

Kallon bariki yayi yace Oya muje in kaiki gida

Tace Yarima plz muje mu shiga, zaiyi magana tace dan Allah, karka sa mutane suyi zargin wani abu tana maganan tare da kokarin San zubar da kwalla…..

Ganin haka yasa yayi dan tsaki tare da fad’in karki Fara cewa zakiyi min kuka a nan, dan naga kina da Arhan hawaye, babu yanda Yarima ya iya dole ya shiga shida abokanan shi da amarya da kawayenta, cikin hall din yayi mugun tsaruwa, wajan zaman amarya da ango daban su biyu, y’an jarida da masu hoto sai d’auka suke, kowa yana fad’in amarya da ango sun dace dinner din ya had’a manyan mutane ciki harda Mai martaba, Yarima bai San zaizo ba saida Ya ganshi shida abokanan shi, harda Mai girma governor da wasu masu mukami a gwamnati sun halarta, anyi watsi da naira kaman baza’a mutu ba, an yanka cake daka nan akace amarya da ango suzo suyi rawa, nan suka fara rawa duk da bariki ba a sake take ba, dan tana jin tsoran ko akwai wanda ya Santa a wajan, nan aka fito ana watsa musu naira mum din Yarima tayi musu liki Sosai, a cikin masu likin idon bariki ya sauka akan Alh madu, dam gabanta ya fad’i, musamman irin murmushin da taga yana sakar mata, gaba d’aya jikinta taji ya saki babu kwari, Yarima kaman ya Lura da ita gashi kuma mutane sunyi yawa ko ince maza dan haka Yarima yaja hannun Zainab suka koma suka zauna, Anci ansha kowa ya watse, Yarima yakai bariki gida da jikinta yake a muce ganin Alh madu a wajan dinner, yanda ta gode Allah ta canza layi ma balle ya mata barazana, toh inya fad’a ma Yarima fah?? Nan taji gabanta ya fara fad’i

Bariki harta Washe gari tana cikin zullumi Kar asirinta ya tonu, haulat Dai da khairat sunyi Mata kara domin a gidan suka kwana, dasu kuma ake komai, bariki na kwance haulat tace wai lafiya kuwa naga kinyi shuru??

Bariki tace kalau nake

Haulat tace dan bani wayarki in bud’e hotspots banda data gashi Ina son tura Abu.

Password din wayar bariki ta cire sannan ta mi’ka ma haulat wayan…..

Toh rana dai bata Karya inji masu iya magana yau juma’a aka d’aura auren Zainab musa da angonta Yarima Aliyu, akan sadaki naira dubu hamsin inda dubban jama’a suka shaida……

Bariki tunda taji an d’aura take ta godema Allah, domin anyi auranta cikin nasara ba tare da Yarima yasan gaskiya ba, a hankali tace yau zan fad’a maka koni wacece Yarima Indai aka kawo ni gidanka,….. Karfe hud’u dai dai aka zo aka d’auki amarya inda aka tafi da ita Zaria a can zata zauna Kafin a dawo da ita kaduna, gefen Yarima Nada aka kaita inda aka gyarashi harta wanda suka kawo amarya bariki hayansu tayi, an karrama amarya da danginta wajan su abinci da duk abunda suke bukata, nan sukace zasu wuce tunda sun kawota, anyi musu shatara na arziki Kafin nan suka wuce……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button