BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Rannan saboda tsoro a toilet na kwana, koda asuba yayi da lambo na bud’e kofar toilet din naga bata nan, naje nasa ma kofata key,… Tun daka ranan ban cika fitowa ba, wata rana naje kitchen Zan d’iba abinci sai gata ta shigo nan gabana ya fara fad’i amma sai naji Abu daban, inda ta Fara bani hakuri Wai Wlh shaidan ne ba halinta bane, ita bata haka kaza da kaza tsautsayi ne wlh kunyan had’a ido takeyi dani, dan Allah in rufa Mata asiri Kar in fad’ama kowa……. Ganin harda kuka sai taban tausayi tare da fad’in Ummi ki nemi gafaran Allah akan ya k’ara kareki daka fad’awa halaka, sannan babu wanda zan fad’ama wa, tunda har kin gane kinyi kuskure….. Nan tai tamin godiya…….

Tun daka ranan na daina shige mata, dama ba wani shige mata din nakeyi ba, sai dai ita ce ke k’okarin jana a jiki……

Wata rana naje kitchen d’iban abinci, harna d’iba na fito naga Ummi a falo ita da wata kawarta na gaida kawar wacce ta kuramin ido kaman tsohuwar mayya,, ummi tace zainab Nayi coconut juice yana fridge Nasan kina so…..

Nace eh ummi tare da komawa kitchen na d’auko a cikin fridge, d’akina na shiga na fara cin abinci na, cikin kwanciyan hankali, nasha juice dina tunda ga lokacin ban San inda kaina yake ba, tun wajan karfe biyu na rana, nidai na farka wajan karfe goma na Safiya gabana Nata zugi kaman ansa min Reza an jimin ciwo, kafana duk ciwo suke min kaman anyi dambe dani, jiki na duk tsami, dakyar na tashi nayi toilet dan in samu inyi tsarki da ruwan zafi ko zanji sauki daka zugin da nakeji, bayan na shiga toilet Wanda ban Lura ba kawai naga jini na bimin kafana…… Abun yaban tsoro ya kuma bani mamaki nasan dai bana al’ada sau biyu a wata kuma baifi kwana Goma dana Gama ba, abun ya dauremin Kai, amma tunda nayi wanka tare da gasa wajan, nasa pad, na fito ina tafiya dakyar…..

Abunda Yaban mamaki shine yanda naga pad din bai baci ba, tunawa da nayi ance al’ada yakan Zoma mace tako wani siga, wannan abun ne yasa na basar duk da ban taba yin irinsa ba, ganin jinin baizo ba yasa nayi wanka na fara sallah

Lokacin da dad dina ya dawo daka saudiya baiko nemeni ba, gaba d’aya tunda ya dawo ya canza daka irin kulawan da yake min, da Farko Ina mamaki amma daka baya saina Fara tunanin aiki sunyi mishi yawa, gashi ina son mishi maganan karatu na, domin ni saudiya nake son zuwa karatu ban son inyi a k’asar nan…… Wata rana naje d’akinshi na sameshi akan maganan karatu na, ya nuna bai yarda inje wata k’asa karatu ba, nai k’okarin in nuna mishi irin burina na son zuwa can fad’a ya bini dashi abunda bai taba min ba a rayuwa, kuka nasa ganin haka Ya fara rarrshi na akan inyi hakuri baya son yayi nisa dani ne, haka yaita rarrashi na, duk da ina Lura da irin canza min din da yayi Sosai…….

Wani Tashin hankali da damuwa daya rufeni shine rashin ganin al’ada dina harna wata biyu, ga nonona suyi ta faman min zugi da rad’adi, gashi sun k’ara girma na k’ara wani haske ……. Gashi gaba d’aya turare na da nake masifar so naji suna min wani irin wari, gaba d’aya na zubar nace hala sunyi expire ne, nasa driver yaje ya siyomin wasu irinsu ,shima dai naji warin yakeyi, abun bada ka nan ya tsaya ba nida bani da wani cin abinci Sosai amma minti Goma na fara jin yunwa gashi ci kaman jaka…… Duk wannan abunda ake ciki Dad dina baya k’asar yana Ghana.

Wata rana na fito ina zazzabi shima dakyar na fito na nufi kitchen dan naji yunwa na neman kasheni, ina zuwa falo Nayi d’akina da gudu Ina amai domin warin turaren wutan da aka sa a falon ji nayi kaman warin jaba…… Ina cikin amai saiga ummi da kawarta sun shigo suna fad’in sannu maike damunki bari in kira Dr, ban damu ba dama ina da bukatar ince a kira family Dr dinmu ta dubani domin dad baya Bari maza na dubamu…… Dr tazo tana tamin tambayoyi ina bata amsa Kai tsaye tace bari ta d’iba jini na, na mi’ka mata hannu na ta d’iba, tace zata koma tayi gwaji inta gwada ta gani zata Aiko da magani…..

Bayan Dr ta fita na koma na kwanta ina jiran a kawo min magani, ina cikin bacci naji an bugo min kofa da karfi, tashi nayi inga ko Waye dad na gani da Falmata, Dad dina kallon tsana yake min ina mamakin ya akayi ya dawo yau,

Katse min tunani yayi da fad’in uban wa ya miki ciki ??

Cikin razana da fargaba nace Dad mai…..

Tas tas ya saukemin Mari har biyu tare da fad’in kin cuceni Zainab, nida nake ma jama’a wa’azi , yau gidana shine y’ata ta ciki na tayi cikin shege…. Allah ya isa tsakani na dake Zainab kin cuceni, duk irin tarbiyan dana baki, jiya sanda ummi d’inki ta kirani tace in dawo gida babu lafiya, Banyi zaton wannan mummunan labarin zan Tarar ba…..

Cikin kuka na fara fad’in Wlh dad ba ciki gareni ba, kuma Wlh muje asibiti a duba, Niko saurayi ma ban dashi W…….

Tas Falmata itama ta sakar min wani gigitaccen Mari tare da fad’in shairi likita zata miki, mutuniyar banza, wlh kin cucemu kaf zuri’ar mu babu wacce ta taba Abun kunya sai ke

Cikin kuka nace ummi Kema shaida ce banda K……

Tayi sauri ta katseni tare da fad’in Yimin shuru munafuka

Dad dina shidai shuru yayi inda Falmata take ta kalaman batanci akai na tare da fad’in na d’auko musu Abun kunya yanzu taya zasu kalla mutane da wannan abun nawa….. Falmata ta kalli dad dina babu ko tsoro tace naji kayi shuru kaman kana jin tsoran yi mata magana gwara ka yanke hukunci tun Kafin mu kasa fita

Dad dina yace in fad’i uban da yayi min ciki.

Ina tamai rantsuwa akan ba ciki gareni ba, dan dai nidai nasan ban taba kwanciya da kowa ba nida ko maza ban kulawa taya zan samu ciki, sai dai in a ruwa nasha…. Da sauri nace Dad Wlh hala a ruwa nasha d…… Falmata ta saki shewa tare da fad’in a ubanki gashi nan da yake gabanki kika sha…… Ko tsoran dad batai ba ta dinga zaginshi Wai shine ya dauremin gindi ai yana nunamin so ya d’auki dukiya masu yawa Yaban ba dole Inbi maza ba….. Kuka nake Sosai tare da takaici na tabbata Falmata Nada wani mummunan Abu a kaina tun sanda Dad dina yace tun jiya ta kirashi akan ya dawo, toh ni kuma yau Dr tazo ta dubani kenan tasan wani abu ko ince ita ta kullamin shairi….. Tsawan da Dad dina yamin yasa na dawo cikin hankalina da hayyacina yace na baki nan da zuwa gobe ki fad’amin wanda yayi miki Inba haka ba za kiga fishina y’ar iska fuuuuuu ya fita…… Wannan itace mummunan Kalman dana taba ji Dad ya fad’a tunda nazo duniya kuma ba’a kan kowa ya fad’a ba sai a kaina, Kalman tayi min ciwo, nidai nasan namiji ko hannuna bai taba ri’kewa ba balle ince toh taya na samu ciki kwata kwata na kasa ganewa….. Ina dai nan zaune inda nake ina kuka saiga Falmata ta shigo tazo gab dani Tana fad’in Zainab kiban had’in Kai Indai kina son Dad d’inki ya yafe miki…..

Wani irin kallo na Mata tare da fad’in da in aikata abunda kike bukata gara dad ya yankani d’anya ya soya Naman jiki na, akan in aikata wannan mummunan aikin wanda Manzon Allah ya tsine ma masuyi…..

Tace haba zainab sau d’aya kawai za muyi in mukayi sai mu tuba….

Zainab tace tir lallai tabewa da Asara sun tabbata a kanki, lallai irinku ne wanda ake cewa kuna fita daka addini baku Sani ba……

D’aura hannunta tayi akan nonona da sauri na wanka mata Mari Wanda dai dai lokacin dad dina ya dawo d’akin ganin na mareta yasa ya fara salati tare da fad’in munanan kalamai a kaina wanda zan iya rantsuwa sune suka bini harya kaini inda nake yanzu domin bakin iyaye dafi ne, sai yasa koda wasa karka taba aibanta d’anka domin addu’an iyaye kaman takobi take da kaifi….. Dad yaci gaba da fad’in daka yau bani bake bazan zauna da wannan abun kunyar ba, wlh saboda ke bazan fasa fita cikin al’umma ba , sannan harda marin ummi d’inki lallai wata rana Nima zaki mareni,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button