BARIKI NA FITO 1 & 2
Kuka nake Sosai domin jin maganan dad nake Wlh kaman bashi yake fad’ansu ba, mutum Mai tawakkali, da ilimi yau shine yake nuna da yaji kunyar duniya gwara ya rabu dani har abada, duk irin sonda yake min ban taba tunanin zai min haka ba, yau koda cikin gareni dagaske ina tunanin dad dina zai d’auka a matsayin kaddara amma gashi anyi min shairi ya yarda
Gashi matarshi sai zugashi takeyi shi kuma yana k’ara hawa yana aibanta ni……
Ranan cikin dare mahaifina yace in bar mishi gidanshi tunda naki fad’an uban da yayi min ciki, ina kuka inata rantsuwa akan banda ciki, inma ciki ne Toh a ruwa nasha, har al’qur’ani na d’auko na dafa akan ban taba saduwa dako wani namiji ba amma dad dina baiko saurareni ba, cikin kuka nace Dad na tabbata abunda kake min yanzu kana yinshi ne cikin rashin bincike, dad kafi kowa sanin wacece ni, kafi kowa sanin abunda zan aikata yau Dad koda ciki gareni ina tunanin zaka d’auka a matsayin kaddara….
Cikin murya irin ta fushi yace fita kibar min gida y’ar iska karuwa……
Lallai wannan Kalman ta dad’e tana Yimin ciwo Sosai har yau inna tuna ina kuka
Mahaifina ya’ki amsan kaddarata saboda Kar yaji kunyar duniya ace y’ar babban malami tayi cikin shege, duk da a lokacin ban San inada ciki ba dagaske…..
Tafiya nake cikin dare komai ban samu na d’auka ba, daka ni sai kayan jiki na, wata babban mota na gani ta lodo wasu kwalaye na samu na shige duk da ban San inda za suba kawai Ina burin inbar garin abuja dan nasan motar wani gari zata, ban dad’e da shiga ba motar ta tashi kaman ni suke jira…… Aiko mukai ta tafiya…… Munyi tafiya Sosai Kafin motar ta tsaya inda na samu na fito na ganni a wani waje kaman kasuwa duk da darene ga mata birjit, cikina naji ya fara ciwo Sosai tare dajin wani abu kaman hanjin cikina zai fita, da sauri nayi wani wajan benci na zauna inata juyi ji nayi wani abu kaman ruwa na fita daka jiki na, ina dubawa naga jini Sosai ga wani irin ciwon ciki inaji Sosai, muryan wani naji a kaina yana fad’in na shiga uku an fasa aurena Mai zan gani haka y’ar uwa??
Ganin na kasa magana alaman ina jin jiki yasa ya kamani yana fad’in oh ni hjy babba sai ku tashi ku kwaso ciki kuzo kusha maganin zubar da ciki kuyi ta juyi, sai a nan na tabbatar da ciki gareni kuma Bari Nayi domin anyi mana bayanin jinin al’ada a islamiyya kuma yanda wannan jinin yake zuba nasan bana al’ada bane, na shiga rud’ani Sosai tare da tunanin a Ina na sami ciki, naci kuka tare da takaicin wannan abun….. Wanna d’an daudun Mai suna hjy babba shine ya taimaka min harna warke na dawo normal Ina kwana a d’akinsa saiya koma d’akin abokanan sa y’an daudu…… Wannan shine silan komawa na gidan karuwai har na fad’a wannan mummunan harkan tunda banda wani abu da zanyi sai shi, sannan nakan je kofar gidan mahaifina ko in tura a ajiye Mai hotuna na da shigan banza dan in kuntata mishi sai dai ban sani ba koya gani ko bai gani ba oho, ina karuwanci ne saboda rasa mafita ko madafa iyayena sun koreni banda wani gata…. Komai ya fado min shi zanyi tunda banda mafita duk da ina aikata Abunne kaman dole sai dai banda wata hujja akai, amma na d’aura hujjata akan ina son in kuntata ma Dad dina, duk da wani zuwa da nayi na ajiye hoto naga gidan babu kowa , na tambaya akace sun tashi tun daka wannan ranan da naje naga gidanmu ban k’ara tunanin in koma Gida ba ko in nemi iyayena ba…… Dan Tsagaitawa tayi tana kuka tana rungume jikin Yarima taci gaba da fad’in Wlh Yarima Ina aikata zina amma Wlh harga Allah cikin raina Ina mamakin haka….. Had’uwa na dakai shine yasa na daina, gaba d’aya, Yarima Nasan had’uwa na dakai had’in Allah ne, na tabbata duk wannan Abun daya faru dani kaddarace Wanda har yanzu ban son wanda yamin ciki ba, Yarima dan Allah kaima karka juyamin baya kaman yanda dad dina yamin dan Allah Yarima…….
Yarima Aliyu dan janyeta yayi a jikinshi ya kura ma fuskanta ido na wani lokaci sannan ya fara murmushi tare da fad’in wow wow nice story I wish dat am a director in had’a film da wannan labarin naki Nasan zan samu kud’i, zainab I will never ever trust you again, komai zai fito daka bakinki karya ne, do you think dat I will believe you with dis ur fake story……. Har kina danganta kanki da babban malami kina fad’in shine dad d’inki?? Wani irin murmushi yayi tare da fad’in you always lies to me…… Bazan k’ara yarda dake ba in my lyf……
Tace Yarima am telling you the truth……..
Yace truth?? Zainab komai naki karya ne, kina tunanin wannan labarin naki zai sa in yarda dake?? You are wrong, this is not the same Yarima dat trust you before, today wen I see d truth about you I have change…..
Cikin kuka tace Yarima Wlh gaskiya na fad’a maka harga Allah, Wannan shine gaskiyan labarin rayuwa ta……
Yace koda gaskiya ne……. I won’t accept you as my wife…… Zaki zauna a nan a matsayin baiwa Mai min bauta…… I won’t accept you macen da kowa ya Santa, but before in baki aikin ki dole in miki HIV test in gani May be kina dashi tunda anbi wancan anbi wancan so Kinga in kina dashi sai in San Kalan aikin daya dace in baki…… Zainab I will make sure to hurt you, saina hukunta ki yanda nan gaba bazaki k’ara yaudaran wani ba, you r lucky I make promise to my dad da yau sai kin bar gidan nan but you will live here as my servant, I hate to see your face, make sure to hide your face from me har sai na nemeki cheater, Yana fad’in haka ya ri’ke kirji dake faman mishi zafi ya fita tare da bar mata d’akin…… K’asa tayi tana kuka shikenan Yarima ya tsaneta duk da ta fad’a mishi gaskiyan ko ita wacece kuka ta saki mai ban tausayi……
Daka yanzu duk wacce take neman BARIKI NA FITO, daka farko taje ta duba Wattpad ko facebook page d’ina MARYAM OBAM NOVELS… Dan gskya daka yanzu babu wacce zan kara turamawa na gaji ga typing ga aikin ture ture haba Abun yamin yawa……
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
BOOK 2
*PAGE 21*
Lallai dama duk Wanda yabar Allah yana tare da tabewa da Asara, duk Wanda ya zabi sabama Allah, amma babu komai zan jure insha Allah, zan d’auki duk wani hukunci ukuba da Yarima zaiyi min…… Da sauri ta tuna da abunda habib ya Mata, lallai habib yaci amanarta rayuwa wanda ka yarda dashi shine mai cutanka…… D’auko wayanta tayi duk da dama Yarima ya canza mata layi gab da bikinsu Tana da number habib dana su haulat …… Kiran habib tayi duk da lokacin wajan karfe biyar saura an kusa kiran sallah asuba….. Cikin muryan bacci ya d’auka daka gani baima ko duba sunan ba…..
Jin muryan bariki yasa habib fad’in harya koroki ne???
Tace habib kaci amanata Tana magana tana kuka, mai yasa kamin haka, duk irin yardan da nayi maka??? Abun ……
Yace dakata ki daina kaini jinsin da ba nawa ba Mlm,
Tace an kaika d’an daudun banza da hofi….. Maci Amana
Habib yace dakata bariki, miye zancan cin Amana?? Au dama bariki akwai Amana ne?? Toh gaskiya Indai haka kika d’auka bai kamata a dinga ce miki bariki ba, karki manta kud’i na fito bid’a, kuma da Farko Aina rufe miki sirrinki, da aka Biyani naira na dukan Naira har million biyar na fad’i gaskiya, sannan wacce taban tace in kira Yarima in fad’a mishi gaskiya, Kafin ki fad’a mishi, sannan ta tura mai hotunan ki da kikai da maza, da sim d’inta na kira kuma ta wayarta ta tura hotunan, dan haka aikin kud’i nayi, ke kina tunanin saboda in rufa miki asiri zanki amsar million biyar, haba bariki ai kin yaudari kanki, Bariki babu Amana ko yarda….. Da Farko na ri’ke miki amana daka baya kud’i yasa na canza, dan haka Kar kiga laifina………