BARIKI NA FITO 1 & 2
Bariki tace abunda Kamin insha Allah sai kaima anyi maka, kaida wacce kuka shirya hakan……
Habib yace Ina ja miki kunne ki daina kaini jinsin daba nawa ba, sannan Bari kiji ita wacce ta Biyani so tayi Yarima ya koroki ita ta aureki domin y’ar lesbians ce, bari in fad’a miki sunanta, sunanta hjy Umaima abunda yasa na fad’a miki koda Kema zaki Biyani ki nemeni dan ki rama, ko yaushe ina free Danni da kika ganni y’ar kasuwa ce ya k’arasa maganan tare dayin shewa ahayye……. Ita haulat da bata da k’ashin arziki Aida ita akaso ayi aikin ta Fara yima matar kwana kwana…..
Bariki kashe wayarta tayi domin bazata iya jin wannan tsinannan ba……
Kuka take Sosai wato hjy Umaima itace tayi komai tare da amfani da habib, toh taya tasan habib din?? Taya suka had’u?? Lallai haulat ya kamata taban amsa, kiran Layin haulat tayi bata d’aga ba, k’ara kira tayi harya kusa tsinkewa sannan haulat ta d’auka cikin muryan bacci…..
Da sauri Bariki tace haulat maina miki keda habib da hjy Umaima…..
Haulat da bacci ke idonta jin haka yasa ta tashi tare da cewa bariki, Kece?? Mai kike fad’a haka……
Nan Bariki ta bata Labarin abunda habib yayi mata
Haulat tace Bariki wlh Wlh ban San hjy Umaima zatai miki haka ba, da Farko dai taso taje wajan boka danta miki asiri ki yarda da ita, har nayi niyan taimaka mata a lokacin, sanda na dawo kaduna in zaki tuna wata rana Aina amshi wayarki?? Toh Ina cikin duba hotunan da nake turawa sai gashi an turo wani keda Alh madu tsirara, nan nima na tura, in baki mantaba data dinki a kunne take ranan, ganin na tura na Alh madu saina had’a dana wani da kika kwana a kirjinshi, ina gamawa na baki wayarki, dama Nayi magana da hjy babba akan Alh madu ya bashi aikin ya gano wa zaki aura, yace yana son in tayashi…… Jin haka saina kira hjy Umaima akan Kar taje wajan boka na bata labarin halinda kike ciki, akan auran da za kiyi akwai wanda yake son rusa auran, harda hotunan dana tura cikin wayarki ta bu’kaci in tura mata tunda na bata labari, nan na tura mata harda number din habib dan na fad’a mata shine yasan komai da kike shiryawa…… Bariki tun ranan da kikai min wa’azi tare da nasiha Wlh daka ranan naji jikina yayi sanyi tare dayin nadama, kuma harga Allah na cire hannuna daka son cutar dake, wlh bariki ban taba tunanin hjy Umaima zata nemi habib ba, dan tunda tamin magana nace tayi hakuri kawai ta bari kiyi aure in yaso daka baya sai ta nemeki, na fad’a mata hakan kawai danta kyaleki Ashe bata hakura ba, kai amma wannan matar ko y’ar iska amma karki damu bariki zan dau miki mataki Wlh, Shima kanshi Alh madu da kanshi ya kira hjy babba yace a daina maganan ya barki kawai………
Bariki kashe wayan tayi bata taba tunanin hjy Umaima ko habib za suyi mata haka ba, lallai makashinka na tare dakai, ta yarda da habib amma yaci amanarta, lallai gaskiya habib ya fad’a bariki babu Amana, sannan komai kayi sai Anci amanarka Indai a bariki ne, jin kiran sallah asuba yasa ta tashi dakyar kanta kaman zai fashe da ciwo, toilet ta nufa dakyar tayi alwala, tazo tayi sallah……
Bayan ta idar gaba d’aya ta kasa bacci , ba komai take tunani ba sai irin matakin da Yarima zai d’auka wanda ta tabbata za taji jiki, dan murmushi tayi tare da fad’in indai wannan hukuncin da Yarima zaimin zaisa ya yafemin Zan jura, koda zaiyi ta azabtar da rayuwa na Indai Ina matsayin matarshi zan jure…. Kuka ta kuma saki tare da fad’in Yarima Ina maka son so, Sonka a jini na yake, zan amshi duk wani horarwa daka gareka…… Tashi tayi ta fita falo da niyan ta Fara aikin bauta daka yau,tana shiga taga Yarima kwance akan kujeran falon yana rawan sanyi, da sauri ta nufeshi cikin Tashin hankali idonshi a rufe kaman yana bacci amma ba bacci yakeyi ba…….. Hannunta tasa akan goshin shi taji zafi Sosai.. Ido ya bud’e a hankali idonshi ya sauka akan Nata gaba d’aya kallon juna suke cikin ido…… Sunyi wajan minti uku suna kallon juna Kafin ta tashi da sauri taje ta samo ruwa da towel tasa towel din tare da matsewa, ta Fara k’okarin sama Yarima akai cikin murya irinta mara lfya yace don’t you dare try to touch me.
Cikin kuka tace Yarima plz allow me to do it, you have a fever…..
Yana k’okarin yin magana tayi sauri tasa Mai towel din akai tana d’an matsa Mai, jin haka yasa ya kasa maganan da yake son yi…..
Amma cikin ranshi babu komai sai k’una tare da tuna hotunan da aka turomai bariki akan namiji tana kwance ga wani kuma yana tsirara ya ri’keta, da sauri yasa hannu ya ture ta…….
K’asa tayi ruwan dake kusa da ita ya zube, yace karki k’ara zuwa inda nake, I have told you, I hate to see your face….
Kuka take Sosai tare dayin nadama akan irin rayuwar data jefa kanta, dan kawai ta kuntata ma Dad d’inta, wanda inta mutu bata da wata hujja, lallai dama irin bala’in dake cikin zina harda rashin ganin k’imar mutum, sannan ba’a ganin darajan mazinaci Wanda gashi shine take gani yanzu, ta tabbata bata ga komai ba yanzu, sai nan gaba…..
Yarima ne ya daka mata tsawa cikin tsana tare da fad’in I said leave from here.
Jiki a sanyaye ta tashi tana kuka harta kusa shiga d’aki yace stop…… Cak ta tsaya
Yace zoki goge wannan ruwan, wa kika bari ya goge?? And make sure ki cire carpet dinnan dan ruwa ya tabashi shima, kije ki shanya a waje……
Kitchen ta nufa ta d’auko mopper ta Fara goge ruwan, carpet din yana da girma kasa d’auka tayi, duk abunda Zainab keyi Yarima na kwance yana kallonta, ganin bazata iya d’auka ba yasa tace Yarima cikin dashewan murya bazan iya d’aukan carpet dinba yayi min nauyi…..
Murmushi yayi tare da fad’in inda sex ne ai kina iya yi, harda kwanciya akan ko wani namiji kin iya, kindai iya karuwanci……
Ido ta lumshe domin maganan Yarima Aliyu ya dakar Mata zuciya, harga Allah Kalman daya fad’a ta iya karuwanci taji Kalman har cikin zuciyarta, tunda take ba’a taba ce mata karuwa ba tunda ta fito karuwanci Abun ya dameta, ita da takeso a dinga ma kiranta da bariki, amma yau shine rana na farko da aka ce ta kware da karuwanci Abun yayi mata ciwo…. Wani zazzafan hawaye ne ya zubo mata ganin in bata fitar da carpet dinba zaiyi ta fad’a mata magana sai yasa ta Fara k’okarin ta d’auki carpet din domin ta kaishi waje din, kaman yanda yace…. Fara ja tayi tana son tayi k’okarin ta d’auka tasa akai, santsin tiles din wajan dabai bushe ba ya di’beta zata Zame, gaba d’aya ta sadakar ta fad’i ji tayi an ri’keta, idonta dake rufe saboda tsoro ta Fara bud’ewa a hankali idonta ya sauka akan na Yarima da shima din ita yake kallo, sunyi wajan minti biyar a haka suna kallon juna , sannan ya d’agota gaba d’aya tare da fad’in stop making and excuse da zaki dinga sawa ina taba wannan kazamin jikin naki…..
Bata ce komai ba shima yana tsaye yana kallonta, kokarin d’aukan carpet din ta karayi……
Hannu yasa shima tare da kama mata duk da baya jin dad’in jikinshi , har kofar waje suka Kai ganin fadawa a wajan, gashi ko hijab balle Gyale bata saba sai dan kwalin dake kanta na jallabiya, yasa yace sake carpet din kibar nan….
Bata musa ba, dan in tayi magana zai iya yi mata ihu, ga fadawa kuma tana hangowa ita yanzu tsoran halin Yarima take, d’auke roban ruwan tayi takai kitchen ta fito kenan shima yana shigowa falon, kallonta yayi tare da kawar da idonshi daka kanta, daka ya kalleta sai ya tuna irin karyan da tamai, Ashe duk ba sonshi take ba, dan kud’i ta aureshi dan k’aramin tsaki yaja tare da wucewa d’akin da yake matsayin nashi danya kwanta yabar ganinta domin wani irin tukukin ba’kin ciki yake cika shi tare da mamaki Wai itace take da wannan munanan halin…..