BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

~HAWWA MUHD USMAN REAL SMASHER~
Marubuciyar ALKAWARIN JINI

~LAYUZA KABIR ADAM~

BOOK 2

                 *PAGE 24*

Bariki hawaye ta farayi tare da fad’in Yarima Ina jin tsoran Kar wani abu ya faru, Yarima Abba da mum Ina ji kaman bazasu amince dani ba in suka San gaskiyan abunda na aikata…… Kuka yaci karfinta lokaci d’aya kuma ta rungume Yarima Aliyu tare da fad’in dan Allah Yarima komai zai faru Karka bari a raba mu ko kuma kayi nesa dani…… Nayi kuskure a rayuwa, aure ba’ayinshi da karya ko yaudara…… Duk abunda akace k’arya dole wata rana asiri ya taunu, sai yasa akace ramin k’arya kurarre ne, duk abunda aka had’ashi da karya baya dad’ewa yake rushewa…… Sai yasa akace gaskiya dokin k’arfe….. Ba’a taba cewa gaskiyan mutum ta k’are sai dai ace k’aryan mutum ya k’are…… Kuka ta kuma saki mai sauti tare da k’ara kankame Yarima Aliyu kaman ance mata za’a kwace mata shi????

Yarima Aliyu kam gaba d’aya ta sakar mishi da jiki, a duniya babu abunda ya tsana kaman yaga kukanta, gashi ita kuma kukan baya mata arha, bini bini ta Fara…… Shima k’ara matseta yayi a jikinsa….. Lallai shima yana tsoran Sanar da Mai martaba ko wacece matar tashi, wannan yana d’aya daka dalilin da yasa ya fara tunanin neman mahaifin Zainab din, domin Idan suka had’u da Mai martaba yana ganin komai zaizo da sauk’i….. Duk da yasan Zainab tayi wauta tun Farko inda ta fad’a mishi ko ita wacece da abun yazo da sauk’i, duk da harda gudun mawarshi wajan k’ara tunzurata ta boye mishi ko ita wacece, domin yanda yake nuna kyamarshi akan mace mazinaciya….. Dole taji tsoran fad’a Mai gaskiyan ko ita wacece….. Abunda Yarima yafi jin tsoran iyayenshi su sani shine Zainab tayi amfani da iyayen Bariki wato iyayen bogi k’arya, a matsayin sune iyayenta, ya tabbata ran abbanshi zai baci Sosai domin zaiga kaman ta raina su ta maidasu k’ananan mutane tayi wasa dasu, amma baya shakkan abban nashi yasan Bariki tayi karuwanci ya tabbata Abba mutum ne mai ilimi zaiyi imani da kaddara tunda bata wuce kan kowa ba, matsalan Yarima Aliyu kawai yanda zai fad’ama abbanshi iyayen matarshi daya aura ba su bane ainiyin iyayenta ba…… Hmmmmm

Yarima jin kukan nata ya’ki tsayawa yasa yace Zainab, ki daina wannan kukan ni dake har abada insha Allah, babu Mai rabamu….. Aurena dake had’in Allah ne, komai zai faru naji na gani ina sonki a haka…… Ki daina wannan kukan Kar kisa kanki ya fara ciwo…….

Tana manne jikinshi tace Yarima….. Ina Sonka bazan iya juran wani abu ya shiga tsakanina dakai ba, plz Yarima karka sa dad d’ina yazo, wlh Ina Ji a jikina kaman zuwanshi zai zama silan rabuwa na dakai yar……..

Da sauri ya cireta daka jikinshi tare dasa bakinshi cikin nata, kissing d’inta yayi na wajan 2mnt, Kafin ya saketa gaba d’aya kasa magana tayi???? dama sai yasa ya Mata domin ta daina wannan maganan ta sami nutsuwa……. Kaman yanda yayi zargin kuwa hakan ta faru domin Bariki kasa magana tayi sai hawaye dake zuban Mata a ido, shima hannu yasa ya fara goge mata, lokaci d’aya kuma ya d’agota tare da fad’in yunwa nake ji, muje muga Mai zamu ci…… Wardrobe d’inta ya bud’e ya d’auko mata jallabiya ya taimaka yasa mata tare da Jan hannunta ta fad’o jikinshi ya d’aura hannunshi akan kafad’anta suka nufi falo, inda an jera kayan abinci, kuyangi na wajan a tsaye suna jiran ta fito su saka mata, Bayan sun fito ita da Yarima kuyangi suka zube suna gaidasu……. Bariki tace kuje zan zuba mishi da kaina…… D’aya daka cikin kuyangin tace ran gimbiya ya dad’e muna Mai neman afuwa bamu San Yarima yana nan ba, bari muje mu k’aro wani……

Bariki tace ku barshi haka kuje kawai….. Fita sukayi suka bar daka Yarima sai his princess bariki au Zainab, gaskiya team bariki kuyi hakuri fah naji Kun Fara cewa a daina batama gimbiyarku suna ana ce mata bariki ???????????? sunanta Zainab, ni gashi barikin na saba dashi????????????……

Yarima Aliyu ja mata d’aya daka kujeran dinning din yayi, tare da fad’in zauna my princess……

Zama tayi shima ya zauna…… Kallonshi tayi tare da fad’in toh who will leak d food???

Yarima yace you mana, tunda kin Kori masu zubawa……

Tace oh Waye Yaban kujera in zauna??

Yace ni.

Tace good, toh waya kamata ya zuba abinci din??

Yarima dariya yayi tare da fad’in my princess mana

Tace a’ah, Nina Fara zama, dan haka Kai zaka saka mana….

Yarima Aliyu kai ya girgiza alaman a’a, sannan yace let me call them su zo su saka mana…..

Bariki tace nidai wanda kasa zanci, ganin dagaske take yasa Yarima Fara bud’e coolers din, d’aukan saving spoon yayi tare da fara zubawa, ganin yanda yakeyi yasa ta Fara dariya……. Tare da tashi ta Fara k’okarin amsan spoon din danta saka musu …….. Amma Yarima ya hanata tare da fad’in barshi my princess ai komai zan iyayi miki Indai it’s will make you happy…… Tace oh komai fa kace?? Yace yes komai kike so indai zaki farin ciki…….

Bariki tace ok, toh yanzu kasan Mai nakeso??

Yarima yace a’a tell me??

Tace indomie nake so, kuma Kai zaka dafa…….

Yarima Aliyu bai son lokacin daya Fara dariya ba, shi ko kasheshi za’ayi bai masan yanda za’a kunna gas ba, balle dafa indomie…… Yace my princess Kina da rigima……

Tace but u promise me komai nake so, zaka min, you have to fulfil ur promise…… In kuma baka iya ba tell me ta k’arasa maganan tana dariya…..

Yace oh you are challenging me??

Tace yes am challenging you…..

Yace OK challenge accepted……. Zan dafa miki indoomie, Zan baki mamaki, but you will help me ki kunna min gas sai ki fita daka kitchen din in kin kunna min…….

Tace babu damuwa zan kunna maka….. But make sure indoomie din yayi dad’i…. Rufe cooler din abincin yayi suka nufi kitchen ta kunna mishi gas sannan ta fita tana jira taga indomie……… Yarima Aliyu yana ganin ta fita ya fara danna wayarshi tare da shiga google ya rubuta……. HOW TO COOK INDOMIE nan yaga yanda ake dafa indomie Kala Kala, d’aura tukunya yayi???????????????? yana karantawa yana zuba abunda akace, cikin minti Goma Yarima ya gama dafa indomie ya zuba a plate……. Falo ya fito tare da ajiye mata a dinning yace Oya come and eat……. Da sauri ta taso dan taga wani irin Abu yayi, Aiko da mamakinta sai taga indomie yayi kyau a ido, ga kamshi yana tashi Sosai.

Zama tayi tana kallonshi sakar mishi murmushi tayi, danta k’osa taci, yanda taga indomie din, gira ya d’aga mata tare da fad’in ko saina baki a baki?

Kaita girgiza mai alaman a’ah Zanci da kaina.

D’iba tayi tasa a baki da sauri ta ajiye Tana kallonshi…. Yace Yadai??

Tace baka sa Magi ba a ciki, anya kasa spicy din kuwa? Naji babu Magi.

Yarima Aliyu shuru yayi can ya tuna bai sa magin indomie din ba, yace oh????‍♀ na manta bansa spicy dinba,….

Dariya bariki ta Fara mishi tare da fad’in, bari in d’auko sai in dinga sawa akai ina ci, kitchen din ta nufa Jim kad’an sai gata da spicy din indomie din ta fito dashi, ta Fara zubawa tana ci, shima zama yayi ya fara cin abinci….. Kallonshi tayi tace Yarima dama you knw how to cook ne dama??

Murmushi yayi tare da fad’in ko ban iyaba akanki ai zan koya.

Tace oh I see, yaushe zaka min tuwo??

Ido ya zaro alaman shock yace tuwo?? Sai kuma yayi dariya tare da fad’in oh plz my princess Nasan babu yanda ake had’a tuwo a Google S…

Shuru yayi domin ya fasa Kwan

Dariya ta farayi tare da fad’in haba, haba, no wander indomie tayi dad’i duk da babu spicy, Ashe a Google Yarima na ya koya, dariya ta saki mai sauti

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button