BARIKI NA FITO 1 & 2
Bariki kam tunda fadawa suka rakata har waje, tafiya take tana hawaye duk inda ta gani yarfa k’afa take bata ma San inda take biba, lallai rayuwar Bariki baiyi ba, duk a sanadin Bariki nake fuskantan wannan matsalan, lallai rayuwar mace k’alilan ce, muddin kika aikata rayuwar banza koda kin tuba sai an goranta miki, wasu mutanan basa ansan tuban mutum gaba d’aya, lallai wa inda sukai sanadin lalacewarta sai Allah ya saka mata, kuka ta tsugunna tanayi Sosai, tare da tuna baya, yanda ta tashi taganta da ciki wanda bata san Wanda yayi mata shiba, wani hawaye mai zafi ne ya fito mata daka ido, tunawa tayi da Yarima ko yana cikin wani hali yanzu? ???? takardan daya bata ta Fara yagawa tare da watsar dashi ko dubawa batayi ba, domin wannan ba’kar takardan ba Abun kallo bane, lokaci d’aya ta tashi taci gaba da tafiya, tafiya take tana kuka, jiri taji yana d’ibanta lokaci d’aya ta fad’i k’asa kaman gawa.
Yarima kam likitoci ne a kansa suna k’okarin ceto rayuwarsa, so suke numfashin shi ya dai daita amma abun yaci tura.
Mum tana asibitin Tana ta sintiri tare da hawaye mai zafi, saiga Mai martaba nan cikin tashin hankali, yake tambaya maiya sami Yarima?
Cikin kuka take fad’a mishi abunda ya faru tun daka kan tura mata hotunan bariki da akayi har yanke hukuncin da tayi.
Mai martaba kallo d’aya zaka masa ka gane ranshi a bace yake, amma ya daure a matsayinshi na sarki Mai shugabantan al’umma baice komai ba sai hakuri da yayi taba mum akan tayi mishi addu’a ne zai tashi insha Allah.
Amma ran Mai martaba yayi mugun baci da irin wannan hukuncin da mum ta yanke ba tare da saninshi ba, lallai komai ya sami Yarima itace, domin itace ummul aba’isin wannan abun, yaka mata tunda taga Abun ta fad’a mishi a matsayinshi na mijinta bawai ta yanke hukunci ba, duk da Mai martaba shima ranshi ya baci da Zainab din akan abunda tayi, musamman iyayen Bariki data samu, kenan su waziri basuyi bincike dakyau ba? Ko ince sarkin anguwan, lallai zanyi bincike akan wannan al’amarin.
Zaunar da mum yayi shima ya zauna, duka babu Mai cewa komai, gaba d’aya suna jiran fitowan Dr.
Suna nan zaune baka jin kukan kowa sai na mum tare da tsanar matar Yarima da take ganin irin wannan son da d’anta yake mata kaman asiri tayi mishi, tunda karuwa ce, and kuma karuwa babu abunda ba zatayi ba. Fitowan Dr ne yasa Mai martaba ya tashi tare da nufan Dr yana fad’in ya jikin nashi?
Dr d’an shuru yayi tare da fad’in ranka ya dad’e muje office, mai martaba da mum suka bi Dr, fadawa Suma suka bi bayansu, koda akace office din Dr mum da Mai martaba ne suka shiga, inda fadawa ke jiransu a waje.
Bayan su mum sun shiga Dr yace su zauna, dakyar mum ta zauna. Mai martaba yace ya jikin nashi?
Dr yace gskiya sai a hankali, mudai munyi iya yin mu, amma gaskiya yana cikin danger rayuwa ko mutuwa, ko wanne zai iya faruwa, tun sanda ya sami bugawan zuciya da farko, abun ya taba zuciyarshi, wanda rashin samun abunda yake so, ko kuma ganin abunda baiyi tsammani ba, ko yaji, zai iya saka shi cikin mugun wani hali, lallai bai kamata ku d’aga mishi hankali ba, irin haka wani Idan aka mishi abun damuwa sai zuciyar tashi ta buga nan take yake mutuwa, amma shidai bai mutu ba amma bazanyi alkawarin zai tashi ba ko akasin haka, domin anything can happen.. Kukan mum ne yasa Dr yin shuru mum tace Dr do what whatever you can, but make sure Yarima ya tashi, shi d’aya ne d’ana namiji dan Allah Dr ka ceci rayuwar d’ana dan Allah, tana maganan tana kuka Sosai, tace Dr ko Nawa kake so zan baka but make sure Yarima ya tashi pl….. Kuka yaci karfinta ba tare data k’arasa abunda take son fad’a ba, ganin haka Dr ya fita ya barsu a office din.
Bayan fitan Dr Mai martaba yace Khadija wannan kukan da kikeyi bashi bane mafita, aiko mai ya sami Yarima ke kika ja, dan haka ki bar wannan kukan
Cikin kuka tace haba Mai naja Mai Nayi da za’a d’aura min laifi??
Mai martaba yace akan wani dalili zaki rabashi da matarshi bayan kin San sarai abunda ya faru baya, wlh Khadija komai ya sami Yarima Kece, akan wani dalili zaki yanke wannan babban hukuncin ba tare da kin fad’amin ba, ai gashi yanzu Idan kika rasa d’an naki saiki huta.
Cikin kuka tace haba Mai martaba yanzu abunda nayi shine Nayi laifi?? Karka manta nifa uwa ce, sannan abunda nayi shine duk wata uwa zata aikata, taya zan yarda d’ana dana haifa cikin cikina ya dinga zama da karuwa a matsayin mata, wacce ta gama yawon gantalinta, sannan Bayan haka tayi mana Karya tare da wasa da mu, ta wajan Kawo iyayen bariki, haba Mai martaba miye laifina dan nace Yarima ya saki wannan fasi’kan yarinyar, kaida kanka ka sani wannan abun yana d’aya daka cikin abunda in mutum yayi ake saki cikin masarautar nan s…..
Dakatar da ita yayi tare da fad’in, kin ganta da idonki ne?? Komai ta aikata tama kanta kuma wannan tsakaninta ne da Allah, yanzu tunda ta riga ta auri d’anki, miye amfanin cewa ya saketa, bayan sarai kin San irin sonda yake mata…
Tace babu wani so, aikin Asiri ne, sannan Wlh bazan yarda d’ana ya zauna da karuwa ba, koda kuwa mai zai faru..
Mai martaba yayi murmushi tare da fad’in in baki yarda ba, yanzu da kika saka ya saketa duk inda taje za’a ce tsohuwar matar Yarima Aliyu Yaron Khadija d’an gidan Murtala, Toh mai kikayi? Khadija yau kin bata min rai yanda bakya zato , kin nuna ban isa ba har zaki yanke hukunci ba tare da sanina ba, toh amma Bari kiji idan kina ikirarin bazaki yarda d’anki ya zauna da karuwa ba kinsa ya Mata saki uku, yanzu saiki shirya kukan mutuwar d’anki dan Kinji abunda Dr yace, sannan a matsayina na mahaifin Aliyu Idan wani abu ya sameshi lallai saina hukunta ki, tunda Kece sila, kinsa ya mata saki uku kin datse zamansu har abada, na tabbata hakkinsu bazai barki ba, dan kina matsayin uwarshi, Nima ubansa ne, inada hakki akansa, amma ki ro’ki Allah ya tashi lafiya, yana fad’in haka ya fita
Mum kam kuka take Sosai tare da k’ara tsanan Bariki, wlh koda Yarima ba saki uku yayi mata ba, bazata Bari yaci gaba da zama da karuwa ba, wacce ta gama ballazar da kanta a titi.
Bariki kam inda ta fad’i mutane sukayi kanta aka zagaye ta, wasu kam d’aukanta hoto suke a Fara yad’awa a media, duk yawan mutanan da suka zagaye ta babu wanda yayi kokarin ya d’auketa koya taimaka mata, yayinda wasu harga Allah tsoran taimakonta suke, domin yanzu duniya ta zama Abun tsoro, saika taimaki mutum ya cuceka, wani mutum ne da yazo wucewa yaga dandazon mutane, dan haka ya faka tare da tambayan maike faruwa? Nan wani ya fara bashi amsa da abunda ya faru, nan mutumin ya kutsa cikin mutane ya ganta a kwance, da sauri ya nufeta tare da daukanta ko kallon mutanen baiyi ba Ya sata a mota, nan wasu daka cikin mutanan suka fara fad’in ka Santa ne??
Mutumin yace koda ban santa ba, shi taimako yana dakyau, ta fad’i kuma ba mutuwa tayi ba, yaka mata ace kun taimaka mata, amma dukanku babu wanda yayi wannan tunanin, Idan yau ya faru akan wata anyi mata haka, toh gobe kaima a kanka zai faru, dan haka ya kamata ku gyara, yana fad’in haka yayi motarshi domin ya kaita asibiti, yabar mutanan cikin tunani yayin da wasu kuma suke fad’in kaji dashi kaida kaga zaka iya.